N2,000 nake sayen sassan jikin dan Adam —Matsafi
An kama wani boka dauke sassan jikin dan Adam wanda ya ce yana saya ne a kan N2,000 daga hannun wani dillalin sassan jikin mutane. Matsafin ya ce yana so ya yi amfani da sassan jikin dan Adam ne don yin tsubbbace-tsubbacen, inda ya tuntubi dillalin, don samo masa, shi kuma ya kawo masa ba […]
An kama wani boka dauke sassan jikin dan Adam wanda ya ce yana saya ne a kan N2,000 daga hannun wani dillalin sassan jikin mutane.
Matsafin ya ce yana so ya yi amfani da sassan jikin dan Adam ne don yin tsubbbace-tsubbacen, inda ya tuntubi dillalin, don samo masa, shi kuma ya kawo masa ba tare da bata lokaci ba.
- Dangote ya tafka asarar Naira biliyan 342 a cikin sa’a 24
- Dubun mai yi wa kananan yara fyade a Filato ta cika
ya shaida wa Aminiya hakan ne a hedkwatar ’yan sanda da ke Osogbo a Jihar Osun, inda Jami’an Sashen Binciken Manayn Laifuka na Rundunar ’Yan Sandan Jihar suke tsare da shi.
Jami’an ’yan sanda sun kuma kama cafke dillalin na sassan jikin dan Adam din kuma ya amsa cewa shi ne ya sayar wa bokan da sassan jikin mutum.
Kwamishinan ’Yan Sanda jihar Osun, Wale Olokode, ya shaida wa wakilinmu cewa an kama wani da ake zargi ya sayi kokon kan mutum daga dillalin sassan jikin dan Adam din.
A zantawarsa da Aminiya, wanda aka kama da kokon kan mutum din, ya ce ya saya ne N20,000 a wurin dillalin, kuma ya saya ne wa wani daga cikin abokan huldarsa.
A cewarsa, ya kashe mutane da yawa, ya sayar da sassan jikinsu a kasa da N2,000 kuma ya kashe kudaden da ya samu ne a wurin shaye-shaye.
Kwamishina Olokode ya ce ana gudanar da bincike kan lamarin kuma za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu nan ba da jimawa ba.