N4,000 ake biyan ’yan fansho a Borno —NLC ga Zulum
Har yanzu akwai tsoffin ma’aikata da ke karɓar Naira 4,000 duk wata a matsayin fansho, a cewar Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) Reshen Jihar Borno
Har yanzu akwai tsoffin ma’aikata da ke karɓar Naira 4,000 duk wata a matsayin fansho, a cewar Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) Reshen Jihar Borno, Kwamared Yusuf Inuwa.
Shugaban na NLC ya ce a irin wannan hali na matsin tattalin arziki, ya sanar da haka ne a lokacin da yake jawabi yayin bikin zagayowar ranar ma’aikata a Maiduguri.
Yusuf ya roki gwamnatin jihar da ta sake duba abin da ake biyan ’yan fansho domin rage musu wahalhalun da suke fama da su.
Ya kuma ja hankali kan yadda aka samu bambancin mai girman gaske tsakanin albashin ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi.
- Rikicin Isra’ila da Iran ne ya haddasa matsalar man fetur a Nijeriya — IPMAN
- An Yi Tiyatar Ƙoda ta Saman Fata Ta Farko A Kano
Ya ce, a yayin da ma’aikatan jihar ke karbar kashi 90 na albashin CONHESS, ma’aikatan kananan hukumomi suna karbar kashi 40 ne kawai.
Don haka ya bukaci gwamnatin jihar da ta kawo ƙarshen wannan bambancin.
Bugu da kari, shugaban na NLC a Borno ya yi kira ga Gwamna Babagan Zulum da ya taimaka ya aiwatar da sabon mafi karancin albashi da kuma karin albashin ma’aikatan kananan hukumomin jihar.
A nasa bangaren, Gwamna Zulum, wanda mataimakinsa, Umar Usman Kadafur, ya wakilta a wurin taron, ya jaddada aniyar gwamnatinsu wajne fifita jin daɗin ma’aikatan jihar.
Ya bayyana kokarin da gwamnatin ta yi a baya-bayan nan wurin bayar da rancen Naira biliyan biyu mara ruwa ga ma’aikata.
Sannan ya ba da tabbacin ci gaba da ƙoƙarin inganta jin ɗaɗin ma’aikatan da ke aiki da ma wadanda suka yi ritaya a jihar.