N500 ta yi sanadiyyar kashe matashi a Kano
Fada tsakanin wasu matasa biyu ya yi sanadiyyar mutuwar dayansu a unguwar Dantsinke ta karamar hukumar Kumbotso a Jihar Kano. Takaddamar ta barke tsakanin wani matashi mai suna Sani Ibrahim da wani mai suna Aminu Malam Hambali, wanda hakan ne ma ya harzuka wani mai suna Haruna Ya’u da ya yi zargin cewa marigayin yana […]
Fada tsakanin wasu matasa biyu ya yi sanadiyyar mutuwar dayansu a unguwar Dantsinke ta karamar hukumar Kumbotso a Jihar Kano.
Takaddamar ta barke tsakanin wani matashi mai suna Sani Ibrahim da wani mai suna Aminu Malam Hambali, wanda hakan ne ma ya harzuka wani mai suna Haruna Ya’u da ya yi zargin cewa marigayin yana kallonsa yayin gardamar.
A kan haka ne ya fusata ya dauki almakashi ya caka wa Sani a kirji inda nan take ya fadi.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce nan take aka garzaya da marigayin zuwa Asibitin Kawararru na Murtala Muhammad, amma kafin a kai ya riga ya rasu.
Ko da yake babu cikakken bayanin a kan musabbabin takaddamar, amma wasu bayanai na cewa a kan wani biyan bashi na N500 ne.
Amma kakakin ‘yan sandan ya ce rahoton da suka samu ya nuna wanda ya yi kisan ba ma da shi ake gardamar ba.
Kiyawa ya ce wan mamacin ne ya kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda da misalin karfe sha daya na daren ranar Talata da abun ya faru.
Ya ce, “Da jin haka jami’anmu suka isa wajen tare da kai mamacin zuwa asibitin Murtala idan aka tabbatar mana ya rasu.
“Hakan ne ya sa Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Habu Sani ya umarci rundunar tsaro da Operation Kan-ka-ce-kwabo ta zakulo wadanda ake zargin cikin sa’o’i 24.
“Cikin ikon Allah jami’anmu suka bazama tare da samun nasarar cafke babban wanda ake zargin, mai kimanin shekaru 24 mazaunin unguwar ta Dantsinke.
“Tuni wanda ake zargin ya amsa laifinsa da cewa yadda marigayin yake kallonsa lokacin takaddamar ne ya sa ya hassala ya yanke shawarar daba masa almakashi a kirji”, inji Kiyawa.
Kakakin ya ce Kwamishinan ‘Yan Sandan ya umarci a mika batun ga Sashen Binciken Manyan laifuka na rundunar don fadada bincike, kuma da zarar an kammala binciken za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya.