Naɗe-naɗen Tinubu na ta da ƙura

Tinubu yana tafiyar da gwamnati ce shi kaɗai tare da danginsa na Legas da Osun.

Naɗe-naɗen Tinubu na ta da ƙura

Ana ci gaba da nuna damuwa game da naɗe-naɗen da Shugaban Kasa Bola Tinubu ke yi, inda ake ganin yana fifita abokansa da abokan siyasarsa tare da watsi da ‘cancanta’ lamarin da ya sha alwashin zai magance wajen nada wadanda za su dafa masa.

Wata guda kacal da zabensa a matsayin Shugaban Kasa, Shugaba Tinubu ya faɗi a wata sanarwa cewa ba zai lura da addini ko kabilanci ko sauransu ba a yayin naɗa mukarraban gwamnatinsa ba.

Ya ce, “A matsayina na shugabanku na gaba, na rungumi nauyin da kuka dora min. Ana magana kan gwamnatin hadin kan kasa. Burina ya wuce nan. Ina son kafa gwamnatin da ta dace da kasa.

“A yayin zaben jami’an gwamnatina, ba zan yi watsi da cancanta da kwazo ba. Lokacin karkata ga gidan siyasa ya wuce.

“Zan tattaro kwararru maza da mata da matasa daga sassan Nijeriya don gina kasa mai zaman lafiya da adalci da kyakkyawar makoma.

“Za a naɗa matasa. Za a ba mata muhimmanci. Imaninka zai kai ka bauta a coci ko masallaci, amma ba zai zama silar ba ka matsayi a gwamnatin ba, sai dai kyakkyawan hali da cancanta.

“Ceto kasar nan ta zama mai kyakkyawar makoma ne manyan abubuwan da muka ba fi fiffiko. Ba za mu sallamar da wadannan manufofi don dalili na siyasa ba.

“Hargowar siyasa za ta koma can baya don ba kyakkyawan shugabanci dama,” in ji Shugaban Kasar, yana bayani kafin a rantsar da shi lokacin da yake mayar da martani kan kiraye-kirayen ya kafa gwamnatin hadin kan kasa.

Sai dai sabanin wannan alkawari, wasu ’yan Nijeriya suna nuna damuwa sosai kan yadda Shugaban yake nada abokai da iyalai da abokan siyasa a kan mukaman mulki, a wasu lokuta ma ba tare da lura da cancantarsu ba.

Baya ga masu sukar rashin lura da cancanta wasu shugabannin jam’iyya wadanda suka yi yaki don nasarar Jam’iyyar APC, suna nuna damuwa kan yadda “aka yi watsi” da su a naɗe-naɗen da Shugaba Tinubu ya riƙa yi zuwa yanzu.

Wasu ’yan siyasa da manzarta da talakwan Nijeriya, sun ce fatar da suke da ita cewa Shugaba Tinubu zai dauki darasi daga kura-kuran magabatansa ta rushe, lura da jerin nade-naden da ya yi.

Zarge-zargen karkata ga yanki daya a naɗe-naɗen da aka yi ga Shugaba Muhammadu Buhari sun sake bayyana.

Wasu sunayen da suke zuwa idan ana batun naɗin son kai a kan Shugaban Kasar sun haɗa da naɗa mijin ’yarsa Oyetunde Ojo a matsayin Babban Shugaban Hukumar Gidaje ta Kasa (FHA).

’Yar Tinubu, Folshade Tinubu Ojo ita ce Shugabar Mata ’Yan Kasuwa ta Legas (Iyaloja).

Sai kuma naɗa ’yar Cif Bisi Akande, Temitope Ilori a matsayin Darakta Janar ta Hukumar Yaƙi da Kanjamau ta Kasa (NACA) da kuma naɗa ɗan Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa, Umar Abdullahi Ganduje a matsayin Babban Darakta a Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara (REA).

Sauran naɗe-naɗen da suka tayar da ƙura a baya-bayan nan sun haɗa da na Olufemi Akinyelure a matsayin Shugaban Sashin Ayyuka a Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NEP).

Olufemi ɗan Cif Pius Akinyelure, wanda a baya Tinubu ya naɗa a matsayin Shugaban Hukumar Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL) marar gafaka.

Shugaban Kasar ya kuma naɗa Muhammad Abu Ibrahim, ɗan abokin siyasarsa Sanata Abu Ibrahim a matsayin Babban Sakataren Asusun Bunkasa Noma na Kasa (NADF).

Baya ga wannan masu sa ido sun nuna tuhumi yadda ake wasan kura a wasu naɗe-naɗen, inda daga baya Shugaban Kasar kan janye sunan da ya mitka daga farko.

Irin waɗannan sun haɗa da janye sunan Imam Kashim Ibrahim Imam, mai shekara 24, da aka naɗa a matsayin Shugaban Hukumar Daraktocin Hukumar Kula da Hanyoyi ta Tarayya (FERMA) bayan ’yan Nijeriya sun nuna damuwa kan ƙarancin shekarunsa.

Sai kuma janye sunan Dokta Maryam Shettima (Maryam Shetty), mai shekara 44, da aka so naɗa ta a minista, inda Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa, Ganduje ya ce, an yi ‘kuskure sa’ shugaban ya naɗa ta.

’Ya’yan APC sun damu, ba a cika alkawuran da aka yi musu ba Manyan ’ya’yan APC da wadanda suka yi mata yaƙin zabe suna nuna damuwa sosai kan naɗe-naɗen na Shugaban Kasa.

An ce masu ruwa-da-tsaki a jam’iyyar ba su jin daɗin salon naɗe-naɗen na Tinubu ba tunda ya zama Shugaban Kasa.

Da dama suna nuna damuwa kan yadda kalilan ne suka rabauta da mukaman da aka naɗa, yayin da saura suka damu kan yadda har yanzu bai naɗa mukamai a hukumomi da cibiyoyi da sassan gwamnati ba.

Majiyoyi masu tushe da suke da alaƙa da batun, sun nuna damuwa kan jan kafa wajen cika alkawarin saka wa ’yan jam’iyya a matakin kasa.

A cewar wani babban ɗan jam’iyyar da ba ya so a ambaci sunansa, burin Shugaban na 2027 na iya rugujewa, saboda yadda ake ganin yana “kidinsa yana rawarsa shi kadai” a Abuja, kuma bai damu da ’ya’yan jam’iyya a jihohin da suka zaɓe shi ba.

“Galibin waɗanda suka nuna masa cikakkiyar biyayya bisa fatar za a saka wa goyon bayansu da naɗe-naɗen muƙamai a tarayya duk an yi watsi da su,” in ji majiyar.

Wata majiyar da ke da masaniya kan abubuwan da suke gudana a Fadar Shugaban Kasar ta ce, “Shugaban Kasar ya buƙaci gwamnoni su miƙa sunayen shugabannin hukumomi, kuma sun yi haka, amma sai ya ki aiki a kan waɗannan sunaye har zuwa yau.

Maimakon haka sai ya naɗa mutanensa a waɗannan hukumomi ciki har da waɗanda gwamnonin suka zaɓi ’ya’yan jam’iyya don cike su tare da mika takardun bayanansu.

“Dubi Hukumar Bayar da Tallafin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Kasa (REA) da sauran hukumomin da ya sanar a bayan nan.

“An zaɓi wasu sunaye daga farko amma lokacin da aka sanar sai wasu sunaye na daban suka bayyana.”

Wata majiyar da ta nemi a sakaye sunanta ta shaida wa wannan jarida cewa, manufar miƙa sunayen daga gwamnonin ita ce a gyara kura-kuran da aka yi a naɗin ministoci da sauran naɗe-naɗen da mutanen da Shugaban ya ba amana suka yi.

“Yanzu ta bayyana ga waɗannan gwamnoni da sauran masu ruwa-da-tsaki cewa Shugaban ya yi watsi da sunayen da suka miƙa masa, kuma hakan ya nuna yana tafiyar da gwamnati ce shi kaɗai tare da danginsa na Legas da Osun,” in ji shi.

A cewar majiyar, yana da muhimmanci a yanzu Shugaba Tinubu ya dauki darasi daga kurakuran tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan a shekarar 2025.

“Shekarar 2027 tana zuwa kuma mun zuba ido mu ga wajen su wa Shugaban zai je. ’Yan Nijeriya ba su cika mantuwa ba. Abin da ya samu Jonathan yana iya samun Tinubu a 2027, idan bai gaggauta gyara karkata ga dangi da abokai a nade-naden ba.

“Gwamnoni sun fusata kuma an kunyata su. Don haka akwai bukatar Shugaban Kasa ya yi abin da ya dace,” in ji shi.

Wani jigo a APC ya ce, aksarinsu suna korafi ba don nade-naden sun ba da fiffiko ga abokai da abokan siyasar Shugaban kawai ba ne, hatta ma wadanda ba ’ya’yan jam’iyyar ba ne sun amfana a gwamnatin fiye da su.

Masu ruwa-da-tsakin sun koka kan Ministan Birnin Tarayya (FCT)), Nyesom Wike wanda ya samar da muƙamai takwas a tarayya ga ’ya’yan PDP na jiharsa ta Ribas, yayin da aka yi watsi da ’ya’yan APC.

Bayanai sun ce a jerin sunayen da Shugaban ya bayar da umarni a shirya kuma ya amince, akwai Hukumar Kula da Al’ummun Iyakoki (BCDA) da aka ba Jihar Kebbi, amma daga baya aka ba Ribas ta hannun Wike.

Dokta Dakorinama Alabo George, wanda aka sanar a matsayin sabon Darakta Janar na hukumar a ranar 14 ga Maris, shi ya kula da dimbin ayyukan gine-gine da Wike ya gudanar a shekara takwas yana Gwamnan Jihar Kuros Riba.

Baya ga wannan wasu shugabannin APC a Babban Birnin Tarayya a kwanakin baya sun nuna adawa da naɗe-naɗen da Wike ya yi, inda suka ce ya fifita ’yan PDP daga Ribas a kansu.

Kimanin wata takwas da suka gabata sai da masu ruwa-da-tsaki a APC a shiyyar Kudu maso Yamma suka nemi Tinubu ya yi taka-tsantsan kan yunƙurin mamaye dukkan nadenaden da za a ba yanki da ’yan siyasar Legas ke shirin yi.

Masu ruwa-da-tsakin a karkashin Kungiyar Magoya Bayan APC a Kudu maso Yamma (SASG), sun yi zargin cewa jihohin da suke yankin an mayar da su gefe a nade-naden da muukarraban Shugaban Kasar suka sanar, inda ‘Yaran Legas’ ne kawai suke darewa kan kujerun.

A wata sanarwa da Babban Ko’odinetanta na Kasa, Otunba Dele Fulani, SASG ta nuna damuwa cewa hakan zai iya zuwa har kan nada ministoci da mukaman ma’aikatu da hukumomi da sassan gwamnati idan ba a hanzarta magancewa ba.

Sanarwar mai taken: “Hadarin Legastan da Kudu maso Yamma,” masu ruwa-da-tsakin sun kawo misali da mukarrabai 20 da Shugaban ya riga ya nada, inda ta ce, 13 daga cikinsu ’yan siyasa mazauna Legas ne.

‘Babu sabon abu a naɗe-naɗen Shugaban Kasar’

Da yake mayar da martani, Mashawarcin Shugaban Kasa kan Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya shaida wa Aminiya cewa babu wani sabon abu a naɗe-naɗen da Shugaban ya yi zuwa yanzu, inda ya ce matukar waɗanda aka naɗa suna da kwarewar da ake buƙata, bai kamata ’yan Nijeriya su rika korafi ba.

Ya ce, a duk duniya an san shugabanni sukan naɗa waɗanda suka sani ne kuma suka yarda da su domin su ƙara tagomashi ga mulkinsu, inda ya kawo misali da shugabannin Amurka John F. Kennedy da Donald Trump.

“Ba sabon abu ba ne. Ana yi haka a ko’ina a duniya. A Amurka, Shugaba Kennedy ya naɗa ƙaninsa a matsayin Babban Lauyan Tarayya; a bayan nan Shugaba Donald Trump ya naɗa surikinsa; kuma ko a wannan mako a Jihar Kano, wato Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa babban dan ubangidansa na siyasa kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, a matsayin kwamishina.”

“Idan sun cancanta ban ga abin magana ba. Kawai a duba in sun cancanta,” in ji shi.

Kan zargin an yi watsi da jiga-jigan APC da dakarunta wajen naɗe-naɗen mukaman da kuma sauya sunayen waɗanda Shugaban ya amince, Onanuga ya ce, “Ba ya da labari a kan haka.”

Ya kara da cewa, akwai sauran muƙamai na zuwa, inda ya ce, akwai sama da mukaman tarayya 7,000 da za a cike ta hanyar nadi, kuma kasa da 1,000 ne aka sanar.

“Akwai muƙamai da dama da za a naɗa nan ba da jimawa ba,” in ji shi, inda ya kara da cewa babu wani dalili na tayar da ƙura a kan abin da babu shi.

Kamar Buhari kamar Tinubu?

Idan za a iya tunawa an riƙa nuna irin wannan damuwa a lokacin mulkin Buhari, inda ’yan Nijeriya suka rika zargin Shugaban a lokacin kan karkata ga abokai da iyalansu.

Daga cikin irin wadannan naɗe-naɗen da suka shafi abokai, iyalai da abokan siyasa mutane sun kawo misali da naɗa Muhammad dan abokin Buhari, Malam Musa Bello daga Adamawa a matsayin Ministan Abuja; sai naɗa Ahmad Salihijo Ahmad ɗan tsohon aminin tsohon Shugaban lokacin da Buharin ya shugabanci Asusun PTF, a matsayin Manajan Daraktan Hukumar REA da naɗa surikinsa Dokta Mahmood Halilu Ahmed a matsayin Manajan Daraktan Kamfanin Buga Kudi da Muhimman Takardu na Kasa (NSPM) Plc.