Naɗin sarautar Hausawa ta haddasa saɓani da fadar Oba na Benin
Dakatar da bikin naɗin sarautar da Sarkin Hausawan Benin ya yi shirin yi, ya kusan ɓata dangantaka tsakanin Hausawa da fadar Sarkin Benin.
Majalisar Masarautar Benin da ke Jihar Edo ta dakatar da bikin naɗin wata sarauta da Sarkin Hausawan Benin ya yi shirin yi, tare da yin gargaɗi mai ƙarfi ga Sarkin Hausawa na ya guji wuce makaɗi da rawa a jihar.
Lamarin da aka ce ya kusan ɓata dangantaka tsakanin Hausawa da fadar Sarkin Benin.
- Ana kashe mutum 28, a sace 24 kullum a Nijeriya — Rahoto
- An harbe kwamandan sojoji har lahira a Kastina
Kamar yadda rahotanni suka nuna Sarkin Hausawan Alhaji Adamu Isa Adam ya shirya naɗa Alhaji Ɗanjuma Garba Binkola a matsayin Garkuwan Hausawan Benin wanda fadar Mai martaba Sarkin Benin kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar ta ce, hakan ba ya bisa ƙa’ida kuma ba hurumin Sarkin Hausawan ba ne.
Hakan na ƙushe ne a cikin wata sanarwa da Iyase na Benin, Cif Sam Igbe ya sanya wa hannu a madadin Majalisar Masarautar Garagajiya ta Benin (BTC) kuma aka rarraba wa manema labarai a jihar.
Sanarwar ta ce, irin wannan shiri da ake yi ya saɓa wa al’adar mutanen Benin da kuma tanadin dokar al’ada da ta shafi harkokin sarauta.
“Ya zo kunnen Majalisar BTC cewa wani mutum da ke kiran kansa “Mai martaba Alhaji Adamu Isa Adamu wanda ya bayyana kansa a matsayin ‘Sarkin Hausawa’ na shirin gudanar da bikin naɗin sarauta a inda za a naɗa Alhaji Ɗanjuma Garba Binkola a matsayin ‘Garkuwan Hausawan Benin’ a ranar 5 ga Mayu, 2024, a Lamba 7 Butcher Street, ƙarshen Titin Mission, Benin-City.
“BTC tana sanar da Rundunar ’Yan sandan Nijeriya da sauran hukumomin tsaro da sauran jama’a cewa wannan taron da aka shirya ya saɓa wa al’adar Masarautar Benin da kuma dokar al’adu da harkokin masarautu. Don haka, bai kamata a gudanar da shi ba.
“Don kauce wa shakku, majalisar na nanata cewa a matsayin hukumar da aka tanada kan al’amuran sarauta, Omo N’Oba N’ Edo Uku Akpolokpolo, Mai martaba Sarkin Benin, Ewuare II, Oba na Benin, bai ba da izini ko amince da naɗin ba.
Yin naɗi ko ba da sarauta da kowane suna da aka kira ga kowane mutum mai suna ‘Alhaji Ɗanjuma Garba Binkola’ ko kuma a ba da izini ga duk wani mai suna ‘Mai martaba Alhaji Adamu Isa Adamu, zai gudanar da irin wannan biki a Birnin Benin ko kuma wani yanki na Gundumar Edo ta Kudu a Jihar Edo,” in ji sanarwar majalisar.
Don haka BTC ta buƙaci su guji keta alfarmar dokar gargajiya ta Benin ta hanyar soke bikin da aka shirya nan da nan.
Jin wannan umarni ko gargaɗi daga fadar Mai martaba Sarkin kan shirin naɗin sai Alhaji Ɗanjuma Garba Binkola ya garzaya fadar Sarkin yana neman afuwa da yafiya bisa abin da ya kira kuskure da ajizanci, amma ba don a ɓata mata da kuma al’adun mutanen Benin ko ƙasƙantar da darajarsu ba.
A cewar wakilinmu hakan ta tabbata ne a bisa ganinsa da aka yi a cikin wani faifan bidiyo na tsawon minti biyu da ake ta yaɗawa a durƙushe a gaban Sarkin yana magana da Ingilishi yana cewa, “Babana Alhaji Garuba haifaffen Benin ne, ni ma a nan aka haife ni kuma a nan na girma, kuma bisa tsawon rayuwata a nan, na san da al’adun mutanen Edo.
“Ban san illar abin da na aikata ba, domin wanda zai ba ni muƙamin ya shaida min cewa aikina shi ne in taimaka masa wajen kula da harkokin al’ummar Hausawa a Jihar Edo,” in ji shi.
Shugaban Al’ummar Arewa Mazauna Jihar Edo, Alhaji Badamasi Saleh a hirarsa da Aminiya kan lamarin ya ce, ba su goyon bayan duk wani abu da zai kawo rashin jituwa a tsakanin al’ummar arewa mazauna jihar da fadar Oba na Benin.
“Muna ƙoƙarin sasanta rigimar domin kada ta janyo wa ’yan Arewa baƙin jini a jihar.
“Domin bisa tsarinsu naɗa wani a kowane matsayi da ya shafi gargajiya hurumi ne na Majalisar Mai martaba Oba na Benin. Saboda haka muna ƙoƙarin ganin mutanenmu suna bin doka da ƙa’ida,” in ji shi.
A ranar Alhamis ɗin makon jiya ne Oba Ewuare II ya ƙi amincewa da shirin yin naɗin da za a yi na Garkuwan Hausawan Benin, taron bikin da aka shirya gudanarwa a ranar Lahadi 5 ga Mayu, 2024 a garin Benin babban birnin Jihar Edo.