Na ba Sambo Dasuki Naira biliyan 63 daga kudin Abacha – Ngozi Iweala
A shekaranjiya Laraba ne tsohuwar Ministar Kudi Ngozi Okonjo-Iweala ta ce ta bai wa tsohon Mai Bai wa Shugaban kasa Shawara ta Fuskar Tsaro Kanar Sambo Dasuki Naira biliyan 63 daga cikin kudin da aka karbe daga iyalan marigayi tsohon Shugaban kasa Janar Sani Abacha.Iweala ta bayyana haka ne lokacin da take mayar da martani […]
A shekaranjiya Laraba ne tsohuwar Ministar Kudi Ngozi Okonjo-Iweala ta ce ta bai wa tsohon Mai Bai wa Shugaban kasa Shawara ta Fuskar Tsaro Kanar Sambo Dasuki Naira biliyan 63 daga cikin kudin da aka karbe daga iyalan marigayi tsohon Shugaban kasa Janar Sani Abacha.
Iweala ta bayyana haka ne lokacin da take mayar da martani ga wani rahoto da aka buga a wata sadarwa ta Intanet da ke zarginta da karkatar da wasu kudi ga ofishin tsohon Mai Bai wa Shugaban kasa Shawara ta Fuskar Tsaron. An dawo da kudin kasar nan ne a watan Janairun bana.
Sanarwar da ta fito daga Mai Bai wa tsohuwar Ministar Shawara kan Watsa labarai, Paul C Nwabuikwu, ya ce yunkurin da ake yi na bata sunan uwar dakinsa na cewa ta karkatar da wasu kudi, ba gaskiya ba ne.
Har ila yau, ta ce kamar yadda Sambo Dasuki ya bukata, tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya ba ta umarni biyan wadannan kudin.
Gabanin hakan, Jonathan ya fara kafa wani kwamiti wanda ya kunshi tsohon Ministan Shari’a da Sambo Dasuki da kuma tsohuwar Ministar Kudin domin ba da shawara kan yadda za a kashe kudin da aka dawo da su don ayyukan ci gaban kasa.
Dokta Ngozi ta ce “Lokacin da kwamitin ya zauna ne Sambo Dasuki ya bukaci a ba shi kudin don ayyukan tsaro, inda ya kafa hujja da cewa babu wani ci gaba da za iya samu idan babu zaman lafiya da tsaro.”
A farkon watan nan ne Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta tuhumi Kanar Dasuki da laifuffukan da suka danganci almundahana da halarta kudin haram a gaban wata kotu.