Sojoji za su fara kera makaman yaki a Najeriya —Buhari

Buhari yana son kasar ta rage dogaro da kasashen waje kacokam wajen makaman yaki.

Sojoji za su fara kera makaman yaki a Najeriya —Buhari

Motar yaki da Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta kera a 2012.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ya umarci Ma’aikatar tsaro da ta fara kera makaman yakin da sojojin Najeriya ke bukata.

Ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Abuja, yayin bikin bude wani taro na kwanaki biyu kan gwajin kwazon ministocin don duba nasarorin ko koma-bayan da aka samu a muhimman bangarori guda tara da gwamnatin ta fi mayar da hankali a kai.

Buhari ya ce kafa sashen kera makaman na sojoji zai taimaka wajen magance yawan dogaron da kasar ke yi da kasashen waje ta bangaren makamai da sauran kayan aikin sojoji.

Shugaban ya ce za a aiwatar da shirin ne a karkashin Kamfanin Kera Makamai na Sojoji (DICON).

A cewarsa, gwamnati ta gamsu da nasarar da ake samu a yaki da ’yan ta’adda, tun bayan sayo jiragen yaki kirar A-29 Super Tucano.

Ya kuma ce ya amince da ware Naira biliyan 13 da miliyan 300 domin fara aiwatar da ayyukan ’yan sanda na yankuna a duk fadin Najeriya a matsayin matakin bunkasa tsaro.

Buhari ya kuma jaddada cewa aikin ginin gadar Second Niger Bridge, da na titin Legas zuwa Ibadan da ma sauran manyan ayyuka za a kammala su kafin karshen wa’adin mulkinsa.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya