Na bar bara na koma waka ne don gudun mutuwar zuciya-Makaho mawaki

Yahaya Usman  shahararren mawakin Hausa ne da ke zaune a garin Kaduna. Duk da cewa makaho ne, amma makantarsa ba ta hana shi jajircewa wajen yin dadadan wakokin da ke nishadantarwa da ilimantarwa da kuma fadakar da jama’a ba. Aminiya ta tattauna da shi a ranar Lahadin da ta gabata a gidansa da ke garin […]

Na bar bara na koma waka ne don gudun mutuwar zuciya-Makaho mawaki
Na bar bara na koma waka ne don gudun mutuwar zuciya-Makaho mawaki

Yahaya Usman  shahararren mawakin Hausa ne da ke zaune a garin Kaduna. Duk da cewa makaho ne, amma makantarsa ba ta hana shi jajircewa wajen yin dadadan wakokin da ke nishadantarwa da ilimantarwa da kuma fadakar da jama’a ba. Aminiya ta tattauna da shi a ranar Lahadin da ta gabata a gidansa da ke garin Rigasa,  inda ya yi gamsasshen bayani dangane da rayuwarsa da yadda ya rasa idanunsa da daililin da ya sa ya shiga harkar wake-wake da kuma sauran al’amuran da suka shafi rayuwarsa.

Wane ne Yahaya Usman?
Assalamu alaikum, sunana Yahaya Usman amma jama’a sun fi kira na da Malam Yahaya Makaho, saboda lalurar rashin gani da nake fama da ita. An haife ni a shekarar 1983 a Gundumar Idesu wanda take cikin karamar Hukumar Giwa da ke Jihar Kaduna. Wannan lalurar kuma ta same ni ne bayan na cika shekara uku, a sanadiyyar ciwon bakon dauro. Na yi makarantar allo, na kuma kammala karatun firamare a shekarar 1997. Daga nan ne na bude shago wanda na fara sana’ar sayar da kayayyakin masarufi. Ina cikin wannan sana’ar ne, wani malami ya ba ni shawara da in bar ta don in kama sana’ar bara, saboda a cewarsa ta fi kawo kudi.
Na yi na’am da shawararsa, sannan na dawo garin Kaduna a shekarar 2001, inda na kama harkar bara gadan-gadan. Ina cikin hakan ne kuma sai wani ya kara ba ni shawarar cewa mabaratan da ke Jihar Legas sun fi wanda ke Kaduna samun sadaka nunkin-ba-nunkin. Kamar yadda waccar shawarar ta yi tasiri a kaina, haka na karbi wannan ma hannu biyu. Na kama hanyar Legas ni kadai. Bayan na kwashe lokaci ina bara a can, sai na fahimci cewa tabbas ana samun sadaka a Legas, amma tsadar rayuwa ta sa kusan duk abin da mabaraci ya tara na karewa ne a kan abinci da sauran dawainiyar yau da kullum. Sai na ga zai fi kyau na dawo Kaduna, daga nan na yanke shawarar cewa na bar bara har abada. Na yi amfani da kudin da na tara ta hanyar bara wajen koma wa Legas, inda a wannan karon na je don saro kayan wuta kamar su talabijin da rediyo. Na saro wadannan kayayyaki don na sayar da su, amma sai ’yan uwa da abokan arziki suka karbe su duka bashi.  Na  komo ba riba, ba uwar kudi. A lokacin da nake cikin wannan halin ne kuma idan ka ba ni sadaka sai na nemi wani mabaraci na ba shi.
Me ya sa?
Saboda a fahimta ta da a ce na ci gaba da karbar sadaka a lokacin, to da wata kila zuciyata ta sake mutuwa.
Me ya sa kake tafiya ba tare da dan jagora ba?
Ina tafiya ba dan jagora ne saboda a fahimta ta idan na dauki dan jagora zan tauye masa hakki. Misali idan na ba shi abinci ba lallai ba ne na fahimci cewa ya koshi, hakazalika idan ya gaji ba zan iya ganewa ba idan har ba fada ya yi ba. Tsoron shiga hakkin dan jagorana ya sa nake yawo ni kadai.
Mene ne dalilin da ya sa ka fara sana’ar waka?
Na shiga harkar wake-wake ne a shekarar 2003, bayan jarin da na fara kasuwancin kayan wuta ya karye. Akwai wani da ake kira Malam Sanusi Kunni shi ne mutum na farko da ya ga halin da nake ciki, ya ba ni shawarar cewa na gwada sana’ar waka kila ko na dace. Kuma muka je dakin daukar waka da shi, ko da isarmu sai ma’aikatan wurin suka yi kememe suka ce su ba su yarda makaho ya shiga ba, saboda a tunaninsu zan bata musu lokaci ne kawai, amma sai suka ga sabanin abin da suke tunani. A lokacin ne kuma na yi wakata ta farko wadda na yi wa tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar. Daga nan kuma na yi wa tsohon Shugaban kasa Ibrahim Babangida sai kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna, Alhaji Sama’ila Yakawada.
Wakokinka za su kai nawa?
Akalla za su kai 375.
Wacce ce bakandamiyarka?
A gaskiya na fi kaunar wakar nan ta ‘Ban San Ka Ba’, saboda yadda ta kunshi tarihin rayuwata da kuma kalubalen da makafi ke fuskanta.
Wane irin kalubale ka fuskanta a rayuwa?
kalubalen na da yawa, wanda ba zan manta da shi ba shi ne, akwai lokaci da farkon shiga ta sana’ar waka, saboda ba ni da kudin mota, kuma ina bukatar in kai wa wani mutum wata waka da na yi masa har ofis dinsa da ke matatar mai ta Kaduna (NNPC). Haka na  tashi karfe 3:00 dare, saboda a lokacin ne babu motoci da yawa a gari, daga nan na kama hanya har zuwa can, inda na isa karfe 9:00 na safe, ka ga tafiyar Kilo mita 26 ke nan.
Yaya kake rubuta wakokinka?
Ba na rubuta wakokina, ina hada kalmomina da amshin da zan yi amfani da su a waka ne kafin in shiga dakin daukar waka.
Wadanne kyaututtuka ka samu a harkar waka?
Na samu fili da mota da kuma babura bakwai duk sanadiyyar waka.
Wane buri kake da shi a rayuwa?
 Ba ni da wani buri da ya wuce a ce na ilmantar da ’ya’yana. Kuma ina so a ce na  samu wadatar da zan dauki dawainiyar kaina da ta iyalina.
Mene ne gaskiyar abin da ake cewa kana da sha’awar aikin soja?
Gaskiya ne, ni mutum ne mai matukar sha’awar aikin soja, saboda yadda nake son jarumtaka, ka ga kuma aiki ne na jarumai.  Na takaita maka jawabi, duk da wannan lalurar da nake fama da ita, idan da zan samu aikin soja a yau, zan yi.  
Yaya batun  iyali fa?
Ina da mata daya Lubabatu da kuma da daya mai suna Usman, wanda nake kyautata zaton duk da ban yi aikin soja ba, to shi In sha Allah zai yi.