Na biya ma’aikata albashinsu – Gwamna Yuguda
Takaddama ta kunno kai a tsakanin Gwamnan Jihar Bauchi Malam Isa Yuguda da shugabannin kungiyar kwadago ta jihar bayan da Gwamnan ya ce babu wani ma’aikaci da yake binsa bashin albashi. Gwamna Yuguda ya bayyana haka ne lokacin da kungiyar ’yan acaba da Keke-NAPEP ta bashi lambar yabo a dakin taro na gidan Gwamnatin Jihar, […]
Takaddama ta kunno kai a tsakanin Gwamnan Jihar Bauchi Malam Isa Yuguda da shugabannin kungiyar kwadago ta jihar bayan da Gwamnan ya ce babu wani ma’aikaci da yake binsa bashin albashi.
Gwamna Yuguda ya bayyana haka ne lokacin da kungiyar ’yan acaba da Keke-NAPEP ta bashi lambar yabo a dakin taro na gidan Gwamnatin Jihar, inda Gwamna Yuguda ya ce “Babu ma’aikacin da ke bina albashi na biya su dukkan hakkokinsu.
Sai dai da yake zantawa da Aminiya Shugaban kungiyar kwadago reshen Jihar Bauchi,
Kwamared Hashimu Muhammed Gital ya ce suna bin gwamnatin jihar bashin albashin watan Disamban shekarar 2014.
Gital ya ce tun lokacin da Gwamna Yuguda ya ce babu wanda yake bin sa bashin albashi da yawan ma’aikata abin ya daure musu kai.