Na ci amanar gwamnoni biyar – Gwamna Lamido

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya furta cewa ya ci amana tare da butulce wa abokansa gwamnonin Jam’iyyar PDP biyar da suka koma Jam’iyyar APC a watan Nuwamban 2013. Gwamna Lamido ya bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata, bayan ya yi ganawar sirri da Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Alhaji Ahmadu […]

Na ci amanar gwamnoni biyar – Gwamna Lamido
Na ci amanar gwamnoni biyar – Gwamna Lamido

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya furta cewa ya ci amana tare da butulce wa abokansa gwamnonin Jam’iyyar PDP biyar da suka koma Jam’iyyar APC a watan Nuwamban 2013.

Gwamna Lamido ya bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata, bayan ya yi ganawar sirri da Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu, a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.
Gwamnonin G-7, tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar da suka hada da tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon Sakataren Jam’iyyar ta kasa, Sam Jaja da tsohon Gwamnan Jihar Kwara, Sanata Bukola Saraki na daga cikin wadanda suka fice daga wurin Babban Taro na Musamman na Jam’iyyar PDP a Abuja, inda suka kafa sabuwar PDP.
Gwamnoni biyar da ake kira G-5 daga kungiyar gwamnoni bakwai da ake kira G-7 da suka hada da Gwamna Rotimi Amaechi na Jihar Ribas da Abdulfatah Ahmed na Jihar Kwara da Aliyu Wamakko na Jihar Sakkwato da Rabi’u Kwankwaso na Jihar Kano da tsigaggen Gwamnan Jihar Adamawa Murtala Nyako sun koma Jam’iyyar APC bayan turka-turka da aka samu na kafa sabuwar PDP.
Sauran gwamnoni biyu da suka hada da Gwamna Sule Lamido na Jigawa da takwaransa na Jihar Neja Aliyu Babangida sun noke suka ki bin takwarorin nasu zuwa APC.
Wannan ya rika jawo takaddama a tsakaninsu, lamarin da ya sa Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya zargi Lamido da Babangida da cin amanar gwamnonin biyar.
Ya ce dukkan gwamnonin bakwai sun yi yarjejeniyar barin PDP, sakamakon sabanin da suka samu da shugabannin jam’iyyar. “Kowa ya san Gwamna Lamido yana cikinmu, shi ne jagoran kungiyar. Ya jagorance mu zuwa wani matsayi, amma ya sauya ra’ayi, kuma dukkanmu mun ji mamakin matakin da ya dauka a karshe,” inji Kwankwaso.
Gwamna Lamido ya tabbatar da abin da Kwankwaso ya fada inda ya ce: “Eh na butulce musu. Ni butulu ne. Tabbas.” Kuma ya ki ya kara bayani a kan haka.
Da aka tambaye shi me ya sa ya butulce wa kungiyar, sai ya mayar da jawabi da cewa, “Na yarda da abin da (Kwankwaso) ya ce. Ku je ku nemi karin bayani daga wurinsa.”
Gwamna Lamido ya ce ba zai koma APC ba, “Yaya za a yi in koma APC? In da ta ni ne, da ba a samu APC ba,” inji shi.
Game da ficewar Obasanjo daga Jam’iyyar PDP, Gwamna Lamido ya ce wannan matsala ce ta cikin gidansu, ya ce Obasanjo ubansu ne kuma bai kamata wasu su rika shiga tsakanin uba da ’ya’yansa ba.
“Bai kamata ka fito kana cin zarafin babanka ba. Matsalarmu ce ku bar mu. Ku ba ’ya’yansa ba ne don Allah ku rabu da mu,” inji Lamido.