Na ci moriyar faduwar Jonathan – Patience Jonathan

Uwargidan Shugaban kasa mai barin gado Dame Patience Jonathan ta ce ta ci gajiyar faduwar mijinta Shugaban kasa Goodluck Jonathan inda ta bayyana yadda faduwarsa a zabe a ranar 28 ga Maris ya samar mata da lafiya daga wata cuta da ba a san kanta ba kuma take bukatar a yi mata babban aiki a […]

Na ci moriyar faduwar Jonathan – Patience Jonathan

Uwargidan Shugaban kasa mai barin gado Dame Patience Jonathan ta ce ta ci gajiyar faduwar mijinta Shugaban kasa Goodluck Jonathan inda ta bayyana yadda faduwarsa a zabe a ranar 28 ga Maris ya samar mata da lafiya daga wata cuta da ba a san kanta ba kuma take bukatar a yi mata babban aiki a kasar waje.

Patience Jonathan wadda ake yi mata lakabi da Maman Peace, ta bayyana cewa an shirya za a yi mata wani babban aikin fida a asibiti, amma bayan gudanar da zaben wanda mijinta Jonathan ya sha kasa a hannun Janar Buhari wanda ya samu nasara, sai likitoci suka shaida mata cewa lafiyarta kalau kuma ba ta bukatar wani aikin tiyata a asibiti.
Uwargidan Shugaban kasar ta bayyana haka ne a cocin Fadar Shugaban kasa, a lokacin gudanar da addu’o’in godiya ga Ubangiji Wanda Ya hukunta musu sauka daga mulki ita da mijinta da rai da lafiyarsu.
Ta bayyana yadda aka yi mata aikin fida a kasar waje lokacin da tsakiyar kamfe a watan Janairun bana.
Uwargidan Shugaban kasar ta ce: “Na yi matukar godiya ga Ubangiji kan barina a raye. Ubangiji ne mai mu’ujizoji. Ubangiji Ya bayar da mamaki a rayuwata, domin mutane sun yi hasashen dayanmu ba zai koma gida ba. Amma Ubangiji Ya sa hakan zai yiwu; dukkanmu mu biyun za mu koma gida lafiya.”
Ta kara da cewa: “A wani lokaci a bana, lokacin da mijina yake kamfe, wannan lokacin kamfe lokacin jarrabawa ne a gare ni. Shaidan ya sake zuwa, kuma wadancan da suka san tsohon Shugaban kasa da matarsa, an fita da gawar matarsa daga wannan wuri. Mun gode Ubangiji cewa ni da mijina muna raye. Mung ode Ubangiji yau muna taro a raye babu mutuwa. kofofinmu suna bude. Wannan lokacin kamfe Shaidan ya kawo hari ya kuma dawowa. Cikin radadi aka garzawa da ni asibiti a watan Janairu kuma likitoci sun shaida min cewa: Mama za a yi miki babban aikin fida yanzu-yanzu.”
Ta ce “Ana cikin kamfe ne na rika mamaki kan yadda za mu yi wa jama’ar Najeriya bayani a kai. Ka san ku zuwa duba lafiyarka ka yi, za su rika bugawa ‘a jaridu, suna fadin maganganun da suka ga dama. An yi min aikin tiyata na farko a karshen watan Janairu. Kuma cikin rahamar Ubangiji an yi min tiyata na warke, kuma daga wancan tiyata ce na wuce dandalin kamfe. Kuma sun gaya min cewa, “Mama za a sake yi miki wata babbar tiyata da ta fi ta baya.”
Mahalarta addu’ar godiyar sun yi tsit suna sauraren matar Jonathan wadda ta kara da cewa: “Wannan ba zai yiwu a wannan asibiti ba. Asibitin ya yi kadan ya yi irin wannan tiyata. Sai dai ki je babban asibiti, sai na ce, “a’a,” zan tafi, ina da yakini ga Ubangijina. Kuma Ubangijina zai fitar da ni. Ya kuma halicce ni ne saboda wata manufa. Sai na kira fastona kan ya ci gaba da yi min addu’a. Suna son in zamo tamkar dabbar layya, amma ba zan zamo ba.”
Ta kara da cewa: “Kun sani na tafi babban asibiti, na ajiye ranar da za a yi mini aikin tiyata, sannan aka ce in tafi kamfe. Suka ba ni sabuwar rana, na biya komai, ina jira kawai a kira ni a dakin tiyata, sai wani abu ya faru, asibitin suka ce bari su sake duba ni. Zuwa wannan lokaci mijina ya riga ya fadi a zabe. Na fice daga fadar Shugaban kasa, muna shirin tafiya. Cikin ikon Allah na tafi asibitoci hudu amma cutar ta bace. Likitocina suka ji mamaki, ba su taba tunanin haka zai faru ba. Likitoci suka ce mu tafi.”
Misis Patience Jonathan ta kuma yi wawaye kan abin da ya faru shekara biyu da suka gabata, inda ta ce, an yi mata aikin fida sau goma sha biyu a kasar waje, ta ce ikon Allah ne da ta ci gaba da rayuwa.
“Na goda Ubangiji kan barina da raina a yau. Allah gagara misali ne, shekara biyu da suka gabata an yi ta yi min tiyata kan tiyata. A cikin wata daya sai da aka yi min tiyata sau 12, abin mamaki ne. Wasu mutane ma cewa suka yi ta mutu, amma sai Ubangiji Ya tayar da ni. Ubangiji ya ce min, “diyata ki koma zan ba ki dama ta biyu, ki koma ki kammala aikinki.”
Ta ci gaba da cewa, “A yau, idan mijina ya fadi a zabe, ina da yakinin Ubangiji Ya sa na kammala aikin.”
Misis Jonathan ta ce tana cike da godiya ga Ubangiji saboda ba ta yi zato ko a mafarki ba cewa za ta kasance matar Shugaban kasa ko matar Mataimakin Gwamna ba. “A rayuwata ban taba zaton zan kasance matar Shugaban kasa ba. Ban taba mafarkin zama koda matar Mataimakin Gwamna ba, saboda mijina ba dan siyasa ba ne. Amma Ubangiji Ya kaddara haka, kuma Ubangiji Ya daukaka mu daga Mataimakin Gwamna zuwa inda muke,” inji ta.
Ta ci gaba da cewa: “Wajibi ne mu gode wa Ubangiji kan abin da Ya yi mana. Ni da iyalina muna godiya ga Ubangiji. Ga mabiyanmu yau tana iya zama ba mai dadi ba, amma ina son su yi godiya ga Ubangiji, saboda kun bi mu na tsawon lokaci daga Mataimakin Gwamna zuwa Gwamna zuwa Mataimakin Shugaban kasa zuwa Shugaban kasa. Kun san wannan mukami ba na rai da mutuwa ba ne. Babu abin da yake tabbata; don haka ina so ku karbi haka da sakakkiyar zuciya, wannan shi ne nufin Ubangiji, don haka ku gode wa Ubangiji. Ubangiji hakika Mai ban mamaki ne. Wannan shi ne bangaren abin da ya shafi siyasarmu.”