Na ci na sha da kasuwancin mangwaro -‘Yar Anti mai mangwaro

Wata mata mai suna ‘Yar Anti Mai mango, ta ce ta ci ta sha ta biya bukatunta ta hanyar  sayar da mangwaro a Unguwar Barakallahu  da ked aura da Cibiyar horar da malamai ta kasa (NTI) da ke kan  hanyar Kaduna zuwa Zariya. ‘Yar-Anti sa kara da cewa, ta fi shekara 25 tana sayar da mangwaro, […]

Na ci na sha da kasuwancin mangwaro -‘Yar Anti mai mangwaro
Na ci na sha da kasuwancin mangwaro -‘Yar Anti mai mangwaro

Wata mata mai suna ‘Yar Anti Mai mango, ta ce ta ci ta sha ta biya bukatunta ta hanyar  sayar da mangwaro a Unguwar Barakallahu  da ked aura da Cibiyar horar da malamai ta kasa (NTI) da ke kan  hanyar Kaduna zuwa Zariya.
 ‘Yar-Anti sa kara da cewa, ta fi shekara 25 tana sayar da mangwaro, tun marigayi Manjo Bazza, wanda shi ne ya kafa wannan wurin da ya sanya wa suna Barakallahu lokacin yana da rai.
 Ta ce, ta samu karuwa na ci da sha da taimaka wa dangi da wannnan sana’a na sayar da kayan gona. Sannan ta ce tana taimaka wa maigidanta da yaranta, wadanda sun zama samari don su cigaba da karatu.
 Ta ciga da cewa, idan mangwaro ya fara janyewa, sai ta koma sayar da Gwaiba. Idan kuma Gwaiba ta wuce sai ta koma sayar da doya da kayan-miya har sai kakan mangwaro ya dawo, idan kuma ya wuce sai su rungumi duk abin da yake da yawa da aka fi so kuma ya fi dadin sha’ani.
 ‘’Abin mamaki a yanzu shi ne yadda mangwaro ba shi da takamenman lokaci, don yana iya farawa kafin ruwa ya sauka, maimakon a baya da bai farawa sosai har sai ruwa ya kankama. Shi ya sa ba shi da tabbas na lokaci, sai dai duk lokacin da ya kama sai mu shiga hada-hadarsa.’’
 ‘Yar-Anti ta ce, suna samun mangwaro ne idan mai babban gidan-gona ya samu mangwaro sai ya nemi dillalai irin su maigidanta wadanda za su sari mangwaron tun yana sama, su sanya leburori su tsinke, su kawo musu, su kuma su sara su rika sayar wa jama’a.
 Ta ce mangwaro irir-iri ne, masu sunaye daban-daban kamar: Tomi da  Apul da Peta da Juli da Juli-Mai-Aur da Binta-Suga da Paparanda da Alfonso da Bakin Aku da dan-Kamaru da Dapsha da Jaman-Mango, da dai sauransu.
 Ta ce kowa da irin wanda ya fi son zakinsa. Kuma wani ya fi wani dadi zaki. Amma ita ta fi son Apul-mango da Tommy da Dapsha da Juli.
 Sai dai ta ce idan mangwaro ya dade da tsinka yana lalacewa, amma babu asara, don masu neman iri suna diba su amfani da shi.  ‘’Muna sayer da danye muna sayar da nunnanne.’’ Inji ta.
 ‘’Abin mamaki shi ne har daga Abuja ana zuwa nan a sayi mangwaro. Wadansu da jiniya suke tsayawa su saya, wadansu kuma su tsaya su aiko a saya musu. Matan Gwamnoni da jami’an tsaro suna tsayawa su sayi mangwaro su wuce.’’