Na dade da yin bankwana da siyasa – Babangida
Tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi babangida ya yi watsi da gayyatart da jam’iyyar da PDP ta yi masa don kasancewa daya daga cikin manyan bakin da za su halarci taron yi wa jama’iyyar garambawul, saboda kamar yadda ya ce, tuni ya yi bankwana da harkar siyasa.A wata sanarwa da ya bayar a Minna, tsohon […]
Tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi babangida ya yi watsi da gayyatart da jam’iyyar da PDP ta yi masa don kasancewa daya daga cikin manyan bakin da za su halarci taron yi wa jama’iyyar garambawul, saboda kamar yadda ya ce, tuni ya yi bankwana da harkar siyasa.
A wata sanarwa da ya bayar a Minna, tsohon shugaban kasar a mulkin soja, ya ce, “shekara hudu da ta wuce a wani taron da na gudanar a otal din Transcorp Hilton da ke Abuja, na sanar da murabus dina daga siyasar jam’iyya, bayan yunkurin da na yi wajen tsayawa takarar shugaban kasa ya ci tura, kuma yanzu ina da nisan shekarun da suka kai 70, a cikin al’ummar da akasari nisan kwanan mutum bai cika wuce shekara 47 da bakwai ba.
Domin nuna godiya ga irin baiwar da Allah ya yi mini, inda na sha kan dimbin kalubalen rayuwa, a lokacin da na yi fama da jarrabawa, sannan ya kare ni daga rudanin hadurran siyasa, don haka a lokacin na yi rokon cewa kada ’yan jarida su tursasa ni in koma ruwa,” in ji shi.
Ya ce tun daga shekarar 2011, yana bayar da gudunmuwa ne kawai a matsayin uban al’umma da kuma “babban mai bayar da shawara” ga masu neman mukamin siyasa da ire-irensu, wadanda ke bukatar shawara wajen cimma burinsu, shi ya sa yake son ci gaba a irin wannan matsayin.
“A shekaruna 74, ina ganin burina ya cika, a matsayina na uba, wanda ba ya siyasar jam’iyya, kuma a shirye nike in bayar da gudunmuwa ga kowane rukuni na mutane, ba tare da danganta kaina da wata jam’iyyar siyasa ba.
“Ina da dimbin abokai da abokan hulda a cikin manyan jam’iyyun nan biyu na APC da PDP, da sauran wadanda ke cikin kananan jam’iyyu. A wannan mataki na tafiyar siyasata, na fi son yin hulda da su ba tare da an zarge ni da yi wa jam’iyya “zagon kasa ba,” in ji shi.
Wadannan al’amura a cewarsa, suna da matukar muhimmanci in an yi la’akari da tsarin siyasar kasar nan da ke fama da dimbin kalubale.
“Na sha jin rade-radi a fagagen siyasa mabambanta, cewa masu yunkurin gyaran jam’iyyar PDP na share mini fagen tsayawa takarar a zaben shekarar 2019 ne. Shin wannan ba abin dariya ba ne? Domin in sha Allahu nan da shekarar 2019 zan cika shekara 78.
“Idan har na daina siyasa tun a shekarar 2011, me ya sa jam’iyyar PDP ke shirin gabatar da dan shekara 78 a matsayin dan takarar shugaban kasa, a kasar da take da managartan mutane maza da mata, wadanda shekarunsu ke kasa da haka ba?
“Ba ni da niyyar tsayawa takarar kowane irin mukami a Najeriya. Zan ci gaba da addu’ar rokon Allah ya ba ni koshin lafiya da tunani mai kyau, ta yadda zan yi nazarin kasata abin kaunata na ci gaba da bunkasa a halin rayuwata zuwa gushewarta,” inji shi.