Na dauki harkar farauta a matsayin sana’a ce -Hajiya Sadiyya Mai Bindiga
Aminiya ta samu zantawa da wata fitacciyar ’yar farauta mai suna Hajiya Sadiyya Mai Bindiga, wadda ta kware wajen sarrafa bindiga irin ta gargajiya da kuma fita farauta, dare da rana, tun shekaru masu yawa da suka wuce: Ga kuma yadda hirar ta kasance: Aminiya: Na ganki cikin shiri irin na mafarauta, ta yaya kika […]
Aminiya ta samu zantawa da wata fitacciyar ’yar farauta mai suna Hajiya Sadiyya Mai Bindiga, wadda ta kware wajen sarrafa bindiga irin ta gargajiya da kuma fita farauta, dare da rana, tun shekaru masu yawa da suka wuce: Ga kuma yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Na ganki cikin shiri irin na mafarauta, ta yaya kika shiga wannan harka ta farauta ga shi kuma kina mace?
Sadiyya Mai bindiga: To da farko dai ina godiya ga Allah da Ya ba ni damar yin hira da wannan jarida mai farin jini, wadda kuma ta yi fice wajen ba da sahihan labarai masu ban mamaki. Ni na gaji farauta ne daga mahaifina Muhammadu Ba-ka-barin-ta-kwana, wanda shi mutumin Kano ne, amma mahaifiyata mutumiyar Funtuwa ce ta Jihar Katsina.
Aminiya: An fi ganin maza a harkar farauta da shiga daji, ba ki shan wahala idan an fita farauta da ke?
Sadiyya Mai bindiga: Ko kadan ba na shan wahala, saboda na riga na saba da shiga dazuka, dare da rana, kuma dazuka masu miyagun namun daji masu ban tsoro,amma babu wahalar da nake sha ko razana.
Aminiya: A lokutan bukukuwan salla ko wata sabga, ana ganin ki cikin ayarin Sarkin Kano, yaya kika dauki wannan aiki?
Sadiyya Mai bindiga: Ina cikin tawagar Mai martaba sarkin Kano bisa jagorancin shugaban ’yan bindigar sarki watau Mai-Tafari, kuma na dauki wannan aiki a matsayin amana da kaunar da nake yi wa sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero da kuma masarautar Kano.
Aminiya: Kina fita farauta zuwa wasu kasashe na waje?
Sadiyya Mai bindiga: kwarai kuwa, ina fita kasashe kamar Chadi da Kamaru da Ghana da wasu dazuka da ke iyakokin Nijeriya da kasashen Yammacin Afirka, kuma Alhamdulillahi, ina matukar jin dadin wannan shiga daji da nake yi.
Aminiya: Kin taba zuwa farauta da kika ji tsoron faruwar wani abu gare ki?
Sadiyya Mai bindiga: kwarai kuwa! Na je wata farauta da na dimauta saboda haduwa da muka yi da wata bauna wadda ta haukace ta nemi hallaka mu a tsakiyar dajin Abaji da ke wajen Abuja, amma sai Allah Ya kare mu.
Aminiya: Kin taba shiga daji aka yi wani fadan farauta wanda ya ba ki tsoro?
Sadiyya Mai bindiga: Wannan ai ba sabon abu ba ne. Ba zan iya lissafa dazukan da na je aka yi fadan farauta ba. Ka san ita farauta ta gaji a yi fada, musamman idan an hadu da abokan gaba. Gaskiya na shiga dazukan da aka yi fadace-fadace masu matukar ban tsoro, sai dai Allah ke kare ni, ina fita babu ko kwarzanen rauni.
Aminiya: An ce mafarauta suna tsafe-tsafe da sauran wasu abubuwa na kare kai, mece ce gaskiyar hakan?
Sadiyya Mai bindiga: Ka san kowa da irin shirin gidansu, amma dai ni a gidanmu babu dukkan wadannan abubuwa, illa dai shiri na neman kariya da muka gada kuma Allah Yana ba mu kariya cikin ikonSa.
Aminiya: Yaya kika dauki farauta ke nan?
Sadiyya Mai bindiga: Na dauki harkar farauta a matsayin sana’a, domin gaskiya ina samun kudade, sannan na san mutane masu yawan gaske, ga shi kuma Allah Ya yi mun arziki ta dalilin farauta. Sannan na san kasashe masu yawa da dazuka masu hadarin gaske.
Aminiya: Kina wani abu banda farauta, idan kin sami zuwa gida daga yawo?
Sadiyya Mai bindiga: Ina ba da maganin grgajiya kan cututtuka masu yawa kuma ana samun waraka. Allah Ya ba ni ikon sanin magunguna masu inganci ta dalilin shiga dazukan da nake yi da cudanya da sarakan daji. Babu shakka ina da sahihan magunguna kuma masu amfani ga lafiyar al’umma.
Aminiya: Ta yaya kike sarrafa wannan bindiga doguwa kuma ta gargajiya?
Sadiyya Mai bindiga: Ai sarrafa bindiga irin tamu babu wahala, kuma gadon harbi na yi daga mahaifina. Na yi fice sosai a wannan harka kuma ina kara godiya ga Allah da Yake kare ni a duk sa’adda na fita wasu kasashe farauta.
Aminiya: Ina kike da zama yanzu ke nan?
Sadiyya Mai bindiga: Yanzu ina zaune ne a Jarkasa yankin karamar Hukumar Dawakin Tofa ta Jihar Kano.
Aminiya: Kina da yara a gabanki?
Sadiyya Mai bindiga: Ina da ’ya’ya 8, maza da mata, sai dai babu wanda na ga alamar zai iya gadon harkata, duk da cewa akwai yaro daya da na ga yana kwatantawa.
Aminiya: To muna godiya, Allah kuma Ya kara nasara.
Sadiyya Mai bindiga: Ni ma na gode kuma za mu kara ci gaba da karanta wannan jarida ta Aminiya mai nishadantarwa.