Na fara koyon waka ne a makarantar Islamiyya- Umar dan Hausa
Umar Musa Ibrahim wanda aka fi sani da ‘Umar dan Hausa’ mawaki ne, kuma Sakatare-Janar na kungiyar Marubuta Wakokin Hausa (National Lyrics and Singers Union) reshen Jihar Kaduna. A zantawarsa da Aminiya kwanakin baya, ya yi bayanin dalilin da ya sa ya shiga harkar da irin kalubalen da harkar ke fuskanta da kuma irin nasarorin […]

Umar Musa Ibrahim wanda aka fi sani da ‘Umar dan Hausa’ mawaki ne, kuma Sakatare-Janar na kungiyar Marubuta Wakokin Hausa (National Lyrics and Singers Union) reshen Jihar Kaduna. A zantawarsa da Aminiya kwanakin baya, ya yi bayanin dalilin da ya sa ya shiga harkar da irin kalubalen da harkar ke fuskanta da kuma irin nasarorin da ya samu.
Tarihina a takaice
Assalamu alaikum, sunana Umar Musa Ibrahim, an haife ni a Unguwar Sanusi da ke yankin karamar Hukumar Kaduna ta Kudu cikin Jihar Kaduna, a shekarar 1982. Daga bisani muka koma garin Rigasa, inda a can ne na yi makarantar firamare da sakandare. Na samu shaidar Difloma a bangaren aikin jarida a Kwalejin Kimiyya da Fasaha da ke Kaduna (Kaduna Polytechnic) a shekarar 2005.
Dalilin da ya sa na zabi sana’ar waka
Hakan ya samo asali ne tun lokacin da nake karami, saboda yadda muke sauraron wakoki ba kama hannun yaro. A lokacin da muke makarantar Islamiyya na samu haske sosai a kan kabli da ba’adin waka daga wasu darussa na littafin Adaf.
Daga wannan lokacin ne na fara waka, inda a shekarar 1998 na yi wa tsohuwar jam’iyyar UNCP wata waka.
Irin mutanen da nake wa waka
A gaskiya na fi ba da karfi wajen wakokin siyasa da kuma wakokin tallace-tallacen kamfanoni. Misali na yi wa Shugaban kasa Goodluck Jonathan waka a lokacin zaben shekarar 2011. Na yi wa Gwamnan Jihar Kaduna Mukhtar Yero da Gwamnan Jihar Gombe Ibrahim Hassan dankwambo da tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Bola Tinubu da sauransu.
Yawan wakokin da na yi
A gaskiya kayyade yawan wakokina zai yi wahala, saboda a lokuta da dama nakan shiga dakin daukar waka, na yi waka, na wuce. Amma a takaice za su kai guda 5000. Kuma bakandamiyata ita ce wata waka da na yi wa Manzon Allah (SAW) mai suna ‘Manzo dan Amina’.
kalubale
kalubalen farko da mawaka ke fuskanta shi ne, yadda jama’a ke yi musu mummunar fahimta, musamman a lokacin da suke neman aure ko neman wata bukatarsu ta yau da kullum.
Abu na biyu shi ne, yadda wasu daga cikinmu suke bata lokaci su yi wa wasu ’yan siyasa waka, ba tare da umarninsu ba. Sai bayan ’yan siyasar sun gamsu da wakar da aka yi musu, sai ka ga sun saka musu da abin bai taka kara ya karya ba, ko kuma a yi ta yawo da hankalin mawakin.
Yana da kyau jama’a su fahimci cewa mawaki mutum ne mai dimbin daraja. Ya dace su ma mawaka su rika mutunta kansu, saboda ta haka ne kawai za su kare martabar sana’arsu.
Nasarori
Alhamdulillahi, na samu nasarori daban-daban. Na san manyan mutane ta sanadiyyar waka. Hakazalika, albarkacinta na samu gida da kujerun Makka da kuma motoci da kalla za su kai guda takwas da sauransu.
Burina
Ba ni da wani buri da ya wuce in gama da mutane lafiya, saboda idan mutum ya samu shaidar jama’a, to insha Allahu ya samu dacewa duniya da lahira.