Na fasa satar

Wani dan sane ne ya yanke wa wani mutum aljihu a cikin kasuwa, ya kwashe masa kudi. Ashe wani dan sanda ya gan shi. Sai da dan sanen ya zo wucewa, sai dan sandan ya rike shi ya ce masa: “Ina kudin da ka sata, kawo su nan!” Koda dan sane ya mika masa kudin […]

Na fasa satar
Na fasa satar

Wani dan sane ne ya yanke wa wani mutum aljihu a cikin kasuwa, ya kwashe masa kudi. Ashe wani dan sanda ya gan shi. Sai da dan sanen ya zo wucewa, sai dan sandan ya rike shi ya ce masa: “Ina kudin da ka sata, kawo su nan!” Koda dan sane ya mika masa kudin duka, sai ya ce masa: “Wuce ka ba ni wuri, barawon banza, barawon wofi.” Ashe abin nan ya kona wa dan sane rai matuka, sai kawai ya koma wajen mutumin da ya yi wa sata, ya ce masa: “Malam, malam, ni dan sane ne, na yi maka sata amma ga dan sandan can shi ya karbe kudin. Saboda haka ka bi shi ya ba ka abinka, ni na fasa satar kuma.”

Daga Sunusi NNPC, 08034367040