Na fi kowa ne dan takara cancanta- Kwankwaso
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya shawarci daliget da su zabi mutumin da ya fi cancanta a matsayin dan takarar shugaban kasa daga jam’iyyar PDP. Kwankwaso ya bayyana hakan ne a sakatariyar PDP a Jihar Sokoto, inda ya gargadi daliget din da su cire san rai su zabi cancanta. Ku kasance kun zabi dan takarar da […]

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya shawarci daliget da su zabi mutumin da ya fi cancanta a matsayin dan takarar shugaban kasa daga jam’iyyar PDP.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a sakatariyar PDP a Jihar Sokoto, inda ya gargadi daliget din da su cire san rai su zabi cancanta. Ku kasance kun zabi dan takarar da ba kawai yaci zabe ba, sai dai wanda bayan zabe zai iya gudanar da abin ‘yan qasar suke bukata.
A tattaunawar da Sanatan ya yi da manema labarai ya ce, Shi ne dan takarar da ya dace a zaba saboda sanin abubuwan da ya yi wa kasar.
Kwankwaso ya ce, ‘ina da ilimin siyasa da kware wa, na fito takara sau 15 na yi nasara sau 13. Nasarar da na samu ba za a iya hada ta sauran ‘yan takarar ba.