Na fi maida hankali kan matsalolin iyali a rubutuna – Hauwa Maiturare

Tura littafi hannun kwararru don gudanar da gyare-gyare:  Murmushi! Wasu daga cikin litattafaina sun bi hannun manyan marubuta don nazari da kuma zakulo gyare-gyare tare da abokai na kusa wadanda da ma makaranta ne, sukan yi sharhi a litattafan wasu dangane da ginin labari, nakan ba su tun yana takarda da biro su karanta, inda […]

Na fi maida hankali kan matsalolin iyali a rubutuna – Hauwa Maiturare

Tura littafi hannun kwararru don gudanar da gyare-gyare: 

Murmushi! Wasu daga cikin litattafaina sun bi hannun manyan marubuta don nazari da kuma zakulo gyare-gyare tare da abokai na kusa wadanda da ma makaranta ne, sukan yi sharhi a litattafan wasu dangane da ginin labari, nakan ba su tun yana takarda da biro su karanta, inda ake bukatar tsokaci su yi, daga nan sai a kai shi gurin bugu, amma daga baya lokuta sun ja an dada samun kwarewa da azanci, idan mu kai rubutunmu sai kawai mu buga abinmu ba tare da wani ya ji ko gani ba, sai dai kawai makaranta su tsince shi a kasuwa.

Wanene gwaninta a fagen adabi?:

Wannan tambaya tana bisa turba, a farkon rubutuna gaskiya ina kwaikayar salon Hajiya Bilkisu Funtuwa ne, domin tana rubutunta ne kan mas’aloli da suka shafi zamantakewa musamman ga mata, salon sai yake burge ni, dan tana kokarin zaburar da mata kan jajircewa a fannoni da yawa na rayuwa don su zama nagartattu, sannan da damfaruwa wajen bin Allah, wadannan daliliai su suka zama tubalan ginin nawa rubutun.

Nasarorin da ta samu a harkar adabi:

Gaskiya babbar nasarar da na samu ta fannin rubutu shi ne arziki na jama’a, domin ka san babu abinda ya fi mutum dadi kuma da shi ne arziki ke samuwa. Na hadu da mutanen da mafarkina bai taba gaya min ba, sannan na taka inda ada aka ce zan je zan sha mamaki. Sannan alhamdulillahi kuma na yi shuhura gwargwadon hali ta yadda idan ana lissafa marubuta mata ina cikin sahunsu. Haka kuma a cikin wannan nasarar muka kafa kungiyar marubuta mata ta Mace Mutum, kungiyar da indai ana lissafa kungiyoyin rubutu tana cikin jagaba. Sannan kuma babu laifi akwai abububuwa na rayuwa da nasarar rubutu ya kai mu ga mallakarsu.

Yanayi da lokacin da ta fi samun damar rubutu:

Nakan yi rubutu a yanayin da bani da takura ta zuciya, bi ma’ana lokacin da nake walwala da rashin yawaitar uzuri. Wani lokaci kuma na fi yin rubutu lokacin hantsi da kuma bayan sallar La’asar.

Iyalanta:

Murmushi! Alhamdulillahi ina da yara guda biyar, maza hudu sai ‘yar autata Mashakura.

Sakonta ga marubuta na hausa:

Sakona ga marubuta a duk inda suke fatan alhairi, sannan a yi kokarin kyautata rubutu wanda zai dace da bahaushiyar Al’umma tare da zabar jigogi masu kyau wadanda za su kawo ci gaba a duniyar bahaushe ta fannin zamantakewa, ilimi, kimiyya da kowane bangare na ci gaban rayuwa, sannan su rika zurfafa bincike yayin da za su yi rubutu akan kowace mas’ala. Sannan su fahimci irin baiwar da Allah ya ba su ta fasaha su gode ta hanyar mutunta kansu da wannan ni’ima wajen bayar da gudummawar gina al’umma a ban kasa, domin su ma wasu halifofin Allah ne a ban kasa, kada su rika rubutun da zai keta addini da kuma al’adarsu. Na gode.

 

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume