Na fi maida hankali kan matsalolin iyali a rubutuna – Hauwa Maiturare

Wacece Hauwa Lawan Maiturare?: Assalamu alaikum. Sunana Hauwa Lawan Maiturare ‘yar asalin Jihar Kano ce inda aka haife ni kuma na tashi a nan. Na Fara Karatun Muhammadiyya kamar yadda yake a al’adar bahaushe, bayan na girma na fara karatun furamare bayan na kamala na fada sakandare ta Mata dake garin Kwa a Jahar Kano. […]

Na fi maida hankali kan matsalolin iyali a rubutuna – Hauwa Maiturare

Wacece Hauwa Lawan Maiturare?:

Assalamu alaikum. Sunana Hauwa Lawan Maiturare ‘yar asalin Jihar Kano ce inda aka haife ni kuma na tashi a nan. Na Fara Karatun Muhammadiyya kamar yadda yake a al’adar bahaushe, bayan na girma na fara karatun furamare bayan na kamala na fada sakandare ta Mata dake garin Kwa a Jahar Kano. Saboda dalilai na rayuwa da ya hada da maraici katsahan, sai ban samu nasarar kammala karatun sakandaren ba, sakamakon rasuwar Mahaifina. Aka aurar da ni, bayan shudewar wasu shekaru sai na samu sahalewar uban ’ya’yana don ci gaba da karatun. Wannan ya sa na yi murna sosai, na fara karatu da kwarin gwiwa da karfin zuciya, na samu nasarar kammala karatun sakandare. Na fada kwalejin horar da malamai ta gwamnatin tarayya dake Kano wato (FCE). Alhamdulillah na shiga karatun da himma sosai Allah kuma Ya dafa min na kammala karatu na fito da kyakkyawan sakamako, wannan sai ya kara min kwarin gwiwar neman ci gaba da karatu a Jami’ar Bayero ta Kano, don samun shaidar Digiri na farko, nan ma Na kammala cikin nasara. A halin yanzu ina koyarwa a makarantar sakandare ta maza dake Goran Dutse. A cikin wannan gwagwarmaya ta karatu na yi yara guda uku.

Abinda ya ja hankalinta ga rubuce-rubuce:

Na Fara rubutu da tazara kafin in fada harkar karatu. Rubutun ne ma ya kara karfafa min gwiwar ci gaba da karo ilimi. Domin kowace tafiya idan akwai ilimi a cikinta an fi samun hanyar billewa. Zamata malamar makaranta ya kara kaifafa min kwanya tare da gane halayyar mutane daban-daban da kuma fahimtar matsaloli. Kasan sai da kalubale ake samun idea ta rubutu sai marubuci ya yi ta kokarin nemo hanyoyin mafita da masalaha. Abinda ya ja hankalina da fara rubutu shi ne sha’awa. Sai kuma kokarin kawo gyara a rubutu. Sha’awa a matakin farko, makaranciya ce ta rubuce- rubuce na magabatanmu, a hankali sai na fara jin sha’awar fara rubutu, musamman idan na ci karo da labarin da kila karshensa bai gamsar da ni ba, ko kuma kwata-kwata ba haka ya kamata ya kasance ba. Daga nan lissafe-lissafen yadda ni nake so ya kasance zai fara zuwar min a kwakwalwata, sai kwatsam wata rana na dauki biro da takarda na fara rubutu. Na fara rubutu ne da wani littafi me suna Da Na Sani. Amma Allah cikin ikonSa littafin ma bai samu sararin fita cikin kasuwar adabi ba, sai dai kullum ina alfahari da shi, kasancewarsa littafina na farko kuma shine ya samu sararin shiga jami’a gurin malamai don masa gyare-gyare kuma su ne suka fara haska min hanyoyin da ya kamata na bi, da shawarwarinsu na ji gara na shigo fagen karatun don a dama da ni.

Yawan litattafan da ta wallafa:

Zuwa yanzu ina da litattafai guda 14 wadanda na rubuta da hanuna. Littattafan sune kamar haka; Biyayya. Khairiyya. Babbar Mace Hakima. Jarabin Rayuwa. Kundin kaddara. Rikita-rikitar Zamani. Ita Ce Sila. Abu A Dunkule. Makauniyar Tafiya. Haske Maganin Duhu. Duniya Ba Ta Auren Rago. Duniya A Tafin Hannu. Cinikin Kifi A Ruwa. Gobarar Gemu. Wadannan sune jerin litattafan da suka shiga kasuwa.

Abinda ya bambanta littafinta na farko da sauran:

Murmushi! Baka ji abinda bahaushe ya ce ba? Da tsohuwar zuma ake magani. Ina alfahari da shi ne saboda kasancearsa rubutun farko gare ni. Zan iya kiransa da dan mabudin alkhairi, domin ai na fada ma ya shiga hannun malamaina, irin gyaran da na samu shi ya kara min karfin gwiwa, kuma ya zama sanadin da na fada neman sani haikan. Wato gaskiya littafin Da Na Sani bai zamo min nadama ba, sai ya zamo min silar alkhairi na ke kuma ji da shi matuka. 

Bambancin adabi a jiya da yau:

Kowane yanayi ko al’umma ta na rubutunta ne a irin halin da ta tsinci kanta, ko kuma yanayin yadda ta ke gudanar da mu’amalarta. A karnikan baya marubutan na rubuce- rubuce kan addini, fatauci, siyasa, zamantakewa da kasuwanci, bukukuwa da nishadi. To a yau an samu sauye-sauye sosai a rayuwar bahaushe ta hanyar shigowar bakin al’adu da cudanya da mutane daban-daban. Wannan tasa shi ma bahaushe dole ya canza daga yadda yake a baya, ya tasirantu da zamani. Gaskiya na fi maida hankali kan rayuwar zamantakewa ta iyali, matsalolin da suke addabarsu musamman mata da yara. Duk da hakan dai mukan taba mas’aloli na rayuwa nan da can. Kamar littafina Abu A Dunkule, jigonsa yana magana ne akan lafiya, yadda aka bayyana tasiri da yaduwar cutukan zamani musamman Sida. Sannan liittafina Ita Ce Sila, jigonsa tasirin shigowar wayoyin hannu cikin al’umma. Haka Duniya Ba Ta Auren Rago, labara ne akan bara. 

Za mu ci gaba a mako mai zuwa.