Na fi mayar da hankali ga wakar al’ada – Sani Tasko Agades
Sani Tasko, mawakin Hausa ne wanda yake tashe a yanzu, kusan ba a kasar Nijar ba har da wasu kasashen na Afirika masu jin Hausa. Asalinsa mutumin Dankama ne ta karamar Hukumar Kaita, a Jihar Katsina. An haife shi a garin Maradi na Jamhuriyar Nijar, sanadiyar kaura da mahaifansa suka yi zuwa can da zama. […]
Sani Tasko, mawakin Hausa ne wanda yake tashe a yanzu, kusan ba a kasar Nijar ba har da wasu kasashen na Afirika masu jin Hausa. Asalinsa mutumin Dankama ne ta karamar Hukumar Kaita, a Jihar Katsina. An haife shi a garin Maradi na Jamhuriyar Nijar, sanadiyar kaura da mahaifansa suka yi zuwa can da zama. Ya koma garin Agadez da zama kimanin shekara hamsin da ta wuce. Aminiya ta sadu da shi a taron Makon Hausa da Kwalejin Ilmi ta Tarayya da ke Katsina ta shirya a kwanakin baya, bisa amsa goron gayyatar da aka yi masa don halartar wannan biki na shekara-shekara da ake yi a cikin makarantar. Ga tattaunawarsa da Aminiya:
Ahmad Kabir, a Katsina
Bari mu fara da jin takaitaccen tarihinka.
Sunana Sani, wanda ake yi wa lakabi da Tasko. Asalin mahaifana ’yan Dankama ne ta nan Katsina, wadanda suka yi kaura zuwa Maradi, inda ni a can aka haife ni a wata unguwa da ake kira dangulbi. Daga bisani na koma Agades da zama.
To, ina maganar karatu fa?
Na Muhammadiyya kullum muna yi, domin shi na sani ba na zamani ba.
To, me ya kai ka Agades?
Karatun Muhammadiyya. Amma kafin in koma can sai da na yi yawon karatu domin har nan Katsina na zauna wajen almajirci.
To, me ya hada ka da yin wakoki?
Na shiga yin waka ne domin inganta al’adunmu na gargajiya. Ni ma in ba da gudunmuwata ga al’adu.
To, akwai wani wanda ya ja hankalinka koda ta wakar ce wadda ta sa ka shiga harkar wakar?
Basira ce kawai Allah Ya ba ni, domin ni ba makadi ba ne, ko na yi barance da wani makadi ko mawaki. Allah ne kawai Ya ba ni basirar yin waka. Ai na ce maka ni almajiri ne ta fuskar neman ilmi. A kan harkar neman ilmin nan na je har Aljeriya da Libiya kafin in dawo Agades. To amma wani abin ikon Allah, duk wadannan yawace-yawacen da na yi, kawai sai dai in ji ni ina sha’awar yin waka, don janyo hankalin al’umma. Hakan kuma ta kasance. Kuma farko ni ban dauki waka a matsayin sana’a ba, ina yinta ne don sha’awa. Daga baya kuma sai ta zamo amfani gare ni. Kuma na fara waka ne a garin Agades amma yanzu wakokina sun shiga har su Burkina Faso da Mali, balle uwa uba Najeriya.
Ko za ka iya tuna wakarka ta farko?
E! Na fara waka ta bege ne. Na fara wakar yabon Annabi ne. Daga nan sai na shiga yin wakokin aure, na jan hankali ko wayar da kai a kan wasu al’amurra; kai har dai ta siyasa duk muna yi.
Ka ce da wakar begen fiyayyen halitta ka fara, ko yaya take?
Ya Rabbi Sarki, Ya Allah mai shirya kowa.
Ya Rabbi sarki, Ya Allah mai shirya kowa.
Ku duba mutane duniyar duk tashi ce.
Ku duba mutane lahirar duk tashi ce.
Mu bi ta a sannu, duniya ba ta san gwani ba.
Mu taka a sannu, duniya mai kada wawa.
To kai kadai kake yin ta ko akwai masu amshi?
’Yan mata nike koya ma wa. Kana jin ta ’yan koroso da wasu mawakan a nan Najeriya suna kwaikwayonta. A lokacin da muke yin ta, mutane masu saurare wallahi har kuka suke yi. A wakar, ina tunasar da mutane matsayin Annabi Muhammadu (SWA) ga Allah. Kuma mutane su bi duniya a sannu saboda wanda aka yi duniyar da lahirar domin shi, Allah Ya karbe shi. Saboda haka, kada mutum ya dauka wani matsayi ko arziki zai yi masa wani abu, ita mai kayar da wawa ce.
To, daga nan aka tsaya?
Ai daga nan sai abu ya ci gaba. In kamo nan da can har in hada waka.
Ga fahimta kana horar da masu rera wakar, haka ne?
Haka ne. Ka san mutane sun fi son su ji waka daga bakin mata. To mu koyarwa ce muke yi, sai mu koyar da su yadda za su rera wakar da rawar da komai.
Wace waka ce ka yi suna a kanta?
Wadda na sani dai ita ce wakar Gajere. Ita mutane suka fi sani amma fa a batun waka kana iya farko ko tsakiya ba ka yi suna ba sai a karshe ka yi suna. To, ita wannan waka ta Gajere daga baya-baya ne, bayan ma na yi sama da shekara 20 ina wakar sannan ta fito. To sai ta zamo ita Allah Ya sa mutane suka fi so. “Gajere, gajere, haka nike son mijina gajere.” Wannan wakar mutane suna son ta fiye da wadda mahaukaciya ta ba ni karshen amshinta.
Yaya aka yi mahaukaciya ta ba ka amshin waka?
Lokacin da nike kokarin hada wakar ‘Rayuwar Mutane,’ na yi ta kokarin kawo amshin wakar, ka san amshi ga waka ya fi komai wuya. To ina hada amshin,”Rayuwar mutane tai nisa duniya ake so…” to yadda zan kai karshen ne ya yi mini wuya. Na kusa mako ina tunanin yadda zan kai karshen amma hakan ba ta samu ba. Rannan na taho ina maimaita baitin, sai hanya ta kawo ni kusa da wata mahaukaciya kuma kowa ya san wannan mahaukaciya ba ta magana amma ina yin wannan baiti sai kawai ta ce: “ba a fadi.” Ai daga nan baitin amshi ya tashi: “Rayuwar mutane tai nisa duniya ake so ba a fadi.” Malam ka duba halin masu kudi duniyar suke so, hatta da matan aure duniyar suke so.. A haka waka ta tashi kuma ta yi suna.
Ina ka fi mayar da hankali a wajen wakokinka?
Gaskiya na fi ba da karfi ga wakokin al’ada ko gargajiya. Zan dubi wani abu namu na al’ada ko gargajiya in yi masa waka. Ka ga na yi wa akushi waka, na yi wa rawani da sauransu. Bature ko wata kabila, ba ka da abin da za ka burge shi irin ya ga ka rike al’adun gargajiya. Za ka zuba abinci cikin kwano ya lalace amma cikin akushi fa? Kuma duk inda ka shiga da rawani a kanka sai ka ga ana girmama ka fiye da saura. Ke nan mu tallata kayanmu na al’ada ya fi komai mutunci a wajenmu.
To, kai da wadanne irin kayan kidin kake amfani?
Don tafiya da zamani ina amfani da jita daya amma saura duk kayan kidi ne na gargajiya, wato ganguna da irinsu.
Kana da Bakandamiya?
E! Amma ban fiddo ta fili ba. Dalilin daukar ta tamkar bakandamiya a wajena shi ne, duk irin yadda wani abu na bacin rai ya faru a cikin gidana, da zarar an rera wakar shi ke nan kowa zai zamo cikin farin ciki. To shi ya sa na dauke ta a matsayin bakandamiyata, duk da cewa ba ta fito ba. Amma ban sani ba ko ita waccan wakar ta Gajere mutane za su dauka bakandamiyar.
Wane sako gare ka ga sauran mawaka?
Sakona gare su shi ne, duk irin yadda za a yi waka, to a yi ta bisa ga koyar da wani abin da jama’a za su amfana. A guji yin kwaikwayo, kamar irin wakokin Indiya, Turanci da sauransu. Muna da fasahar da Allah Ya yi mana wadda duk inda muka gwada za a yi sha’awa, to don me za mu rika yin aro?