Na fi sha’awar waka a kan harkar fim -Gambo Abdul’aziz

Aminiya ta samu tattaunawa da wani fitaccen mawaki mai suna Gambo Abdul’aziz wanda ake yi masa lakabi  da kyauren-Kudun-Sarkin-Waka a unguwar Janaral Tent da ke yankin Aja a Jihar Legas. Gambo ya ce yi wakoki da yawa kamar na soyayya da siyasa da kuma daidaikun jama’a. Ga yadda hirar ta kasance: Ko za ka gabatar […]

Na fi sha’awar waka a kan harkar fim -Gambo Abdul’aziz
Na fi sha’awar waka a kan harkar fim -Gambo Abdul’aziz

Aminiya ta samu tattaunawa da wani fitaccen mawaki mai suna Gambo Abdul’aziz wanda ake yi masa lakabi  da kyauren-Kudun-Sarkin-Waka a unguwar Janaral Tent da ke yankin Aja a Jihar Legas. Gambo ya ce yi wakoki da yawa kamar na soyayya da siyasa da kuma daidaikun jama’a. Ga yadda hirar ta kasance:

Ko za ka gabatar da kanka?

Sunana Gambo Abdul’aziz amma ana yi mani lakabi da kyauren-Kudu-Sarkin-Waka. An haife ni a garin Hadeja da ke Jihar Jigawa a Arewacin Najeriya. Na fara waka tun ina garinmu na Hadeja kuma na shafe fiye shekaru 15 ina waka. Na yi wakoki da yawa daga bisani sai na tattara inawa-inawa na dawo Legas saboda hana waka da aka yi a Arewa lokacin da aka kafa Shari’a.
Me ya sa ka zabi ka dawo Legas a maimakon wata jiha a Arewa?
Gaskiya dalilin da ya sa na zabi Legas shi ne Legas wuri ne da kowa yake gudanar da harkokinsa ba tare da wani ya sanya maka ido ba. Duk abin da ka zo da shi in dai sana’a ce da za ka rufa wa kanka asiri kuma gwamnati ta karu da kai, to babu wanda zai takura maka. Abin da ba a so a Legas shi ne mutum ya yi sata ya zama ci-ma-zaune. Na biyu Legas matattara ce ta jama’a daban-daban kuma wuri ne da mutanenmu ’yan Arewa suke da yawa suna gudanar da harkokinsu na yau da kullum, sannan kuma suna bukatar wanda zai rika nishadantar da su bayan sun tashi daga sana’o’insu. Saboda haka sai na ga bari na zo na rika nishadantar da su don na samu abin sa wa a baka.
Ka ce ka yi wakoki da yawa, wadanne za ka iya tunawa a yanzu?
Gaskiya na yi wakoki da dama amma wadanda zan iya tunawa za su kai kamar 50. Wakokin sun kunshi na sarakuna da ’yan siyasa da ’yan kasuwa da sauransu. Wadanda zan iya tunawa su ne kamar wakar da na yi wa Sarkin Hausawan Legas, Alhaji Sani Kabiru da wakar da na yi wa Sarkin Kasuwar Alaba Rago, Alhaji Ummaru Nagoggo Sakkwato da wakar da na yi wa Sarkin Hausawan Ajah, Alhaji Ibrahim Sarki Goma da wani dan takarar jam’iyyar PDP da sauransu.
A cikin wadannan wakoki da ka yi, wacce ka fi so kuma me ye dalili?
Gaskiya na fi son wakar da na yi wa Sarkin Hausawan Ajah, Alhaji Ibrahin Sarki Goma, wacce na sanya mata suna ‘kasurgumi.’ Dalilin da suka sa na fi son wakar su ne, na yi wakar ne da kayan kida na gargajiya kamar kotso irin wacce dankwairo ke kida da ita kuma wakar ta karbu ga daukacin al’ummar Hausawa da ke nan Jihar Legas da Kudanci kai har da Arewacin Najeriya. Allah Ya kimsa mani fasaha da hazaka a cikin wakar, ni kaina idan na saurare ta sai na rika mamakin irin kalmomin da na yi amfani da su a cikin wakar da kuma irin yadda na rika jera baitukan daki-daki ba tare da wata matsala ba. Saboda haka ne ya sa nake yawan jinta ba na kosawa. Gaskiya na dauki ita wannan waka tamkar Bakandamiyata.
Me ya sa ka fi son waka a maimakon fim da wasan dabe?
Hakika na fi son waka a kan wasan nishadi na dirama ko dabe ko kuma fim. Saboda ita waka takan ba mutum daukaka ba a wuri daya ba, har zuwa wurare masu nisa da ba ka taba zaton za ka je ba. Shi kuwa harkar dirama ko wasan dabe a wuri daya kusan ake gabatar da shi, sai idan da wata bukata ake zuwa wani wuri a gudanar da shi. Gara ma harkar fim da ake dauka a bidiyo a yi kaset a sayar, ita wannan takan daukaka mutum ita ma. Amma gaskiya ni a ganina waka ta fi su daukaka mutum cikin sauri.
Kwanakin baya gwamnatin Jonathan da shude ta ba ’yan fim na Nollywood da Kannywood makuden kudi, shin kai ka samu kudin?
Gaskiya ban samu wannan kudin ba amma ni ma da an ba ni da zan tallafa wa kamfanina da nake da shi na waka. Kuma ni ma zan san gwamnati ta san da ni. Amma da yake ka san yadda kasar nan take in ba wani kake da shi a sama ba duk wani abu da za a yi ba za ka san ma an yi ba. Amma yanzu da yake an samu canjin gwamnati, Buhari ya hau muna sa rai zai tallafa mana don mu bunkasa sana’armu.
Ka taba yin harkar fim?
Na taba harkar fim a lokacin ina gida Hadeja amma daga bisani sai na yi watsi da ita saboda shi fim yana bukatar sai ka shirya wato kudi. Ni kuma sai na ga ba ni da kudin da zan rika daukar nauyin shirya fim saboda haka sai na ci gaba da harkar wakata. Ina mai tabbatar maka da cewa ina da duk wata fikira da fasaha ta shirya fim ko kuma yin fitowa a dan wasa amma ni dai na fi son waka.
Wadanne nasarori ka samu a waka?
Na gode wa Allah, na samu alfanu masu yawa. Ka san ita waka bai wuce a ce an ba ka kudi da wasu kyaututtuka ba. Ni ma kuma na samu irin wadannan kyaututtuka. Saboda haka babu abin da zan ce sai dai na gode wa Allah madaukakin sarki.
Wadannan wakoki kake so ka fitar kwanan nan?
E, to a yanzu babu wadansu wakoki da na yi kwanan nan, babu kuma wadanda nake son na fitar amma dai akwai wadanda nake yi wadanda ban kai ga kammala su ba amma da yardar Allah zan fito da su duniya ta ji su. A yanzu ba zan fadi sunayensu ba saboda kada na yi riga malam masallaci. Amma na san da yardar Allah wakokin za su karbu ga jama’a.