Na fi son dan Enugu dan PDP a kan dan Jigawa dan APC – Sule Lamido

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya ce ya fi son mutumin Enugu dan Jam’iyyar PDP a kan dan Jigawa dan Jam’iyyar APC. Alhaji Sule Lamido ya bayyana haka ne lokacin da matar dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar PDP Hajiya Rukayya Aitu Abubakar ta kai masa ziyara a gidansa da ke Bamaina kusa […]

Na fi son dan Enugu dan PDP a kan dan Jigawa dan APC – Sule Lamido
Na fi son dan Enugu dan PDP a kan dan Jigawa dan APC – Sule Lamido

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya ce ya fi son mutumin Enugu dan Jam’iyyar PDP a kan dan Jigawa dan Jam’iyyar APC. Alhaji Sule Lamido ya bayyana haka ne lokacin da matar dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar PDP Hajiya Rukayya Aitu Abubakar ta kai masa ziyara a gidansa da ke Bamaina kusa da Birnin Kudu da ke Jihar Jigawa. Ya ce “Mu a Jihar Jigawa kanmu a hade yake kuma muna kaunar junanmu amma duk da hadin kanmu, na fi son mutumin Enugu dan Jam’iyyar PDP a kan Bahaushe dan Jigawa wanda yake APC.”                                                                                                                                                Ya çi gaba da cewa, “Na fara yin siyasa tun 1976 kuma na tsaya takara a kan mukamai daban-daban amma haka bai sa na taba tunanin sauya sheka ba sai a yanzu saboda lalacewa a ce na fice daga PDP na koma APC? Allah Ya kiyaye. Wa zan bi kuma ina zan je, su wane ne a APC din? Tun farko lokacin da Rukayya Atiku Abubakar ta kai ziyarar barn girma ga Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammadu Sunusi ya danganta tarbiyyar yara a hannun iyaye mata, inda  ya ce iyaye mata suna da matukar daraja a tsakanin al’umma.

Sarkin yA ci gaba da cewa kamata ya yi iyaye su mayar da hankali matuka  wajen kulawa da tarbiyyar ’ya’yansu saboda ana cikin wani zamani da ake fama da gurbacewar tarbiyya.

Ya nuna damuwarsa kan yawaitar shaye-shayen miyagun kwayoyi wadanda su kansu matan aure ba su tsira ba daga wannan hali na shaye-shaye.

Dan haka Sarkin ya bukaci mata a matsayinsu na masu bayar da tarbiyya su tsaya sosai wajen yaki da shaye-shaye, domin ganin an sama wa matasa tarbiyya tagari

Da take nata jawabin, Hajiya Rukayya ta bukaci Sarkin Dutse da ya taya mijinta da addu’a kuma suna bukatar goyon bayan Masarautar Dutse. Ta ce makasudin zuwansu fadar shi ne, domin neman sanya albarkar masarautar kuma su nemi taimakon masarautar a kan zaben da za su shiga na neman Shugabancin Kasa da mijinta yake takara.

Hakazalika ta hori mata da kada su yi kunshi har sai bayan zabe, saboda a cewarta lalle yana sa wa matan da suka yi kunshi su yi hasarar kuri’arsu a lokacin zabe.

Hajiya Mairo Waziri ta ce Jihar Jigawa ita ce cibiyar siyasar Najeriya saboda a nan ne jagoran Jam’iyyar PDP yake, wato Sule Lamido. Ta danganta wadanda suke ficewa daga PDP zuwa APC a matsayin matsorata. Ta kara da cewa duk wadanda suke ficewar suna fita ce saboda tsoron kada a kama su.

Ta ce dole ne idan ana so burin Atiku ya cika na zama Shugaban Kasa sai an hada kai da mutane irin su Sule Lamido, ba don komai ba, dama can Atiku da Lamido hade suke, ba su rabuwa.

 

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta