Na fito takara ne don in kawo canji – Eglah D. Kasim

Wata kwararriyar ma’aikaciya da ta shiga siyasa Misis Eglag Sulaiman D. Kasim, ta ce ta shiga siyasa ce domin ta kawo canji a yankin mazabar Sanata ta Gombe ta Kudu. Misis Eglag Kasim wadda ta kai matsayin Babbar Sakatariya, ta ce duk da cewa akwai manyan ’yan siyasa da suke neman wannan kujera, gwiwarta ba […]

Na fito takara ne don in kawo canji – Eglah D. Kasim
Na fito takara ne don in kawo canji – Eglah D. Kasim

Wata kwararriyar ma’aikaciya da ta shiga siyasa Misis Eglag Sulaiman D. Kasim, ta ce ta shiga siyasa ce domin ta kawo canji a yankin mazabar Sanata ta Gombe ta Kudu.

Misis Eglag Kasim wadda ta kai matsayin Babbar Sakatariya, ta ce duk da cewa akwai manyan ’yan siyasa da suke neman wannan kujera, gwiwarta ba ta yi sanyi ba, domin ta ce fitowarta
takara kalubale ne ga maza.
Misis Eglah ta ce kayar da wanda yake kan kujerar a zaben da ke tafe ya fi komai sauki a wurinta, domin yanzu canji jama’a suke so, kuma mata ne za su dana.
Ta ce wannan shi ne karo na farko da ta taba fitowa takara, amma duk da yawan ’yan takara da ake da su a PDP a yankin, ta ce ta fi so a gudanar da zaben fidda-gwani, “idan kuma sasantawa za a yi su maza da suke da yawa a sasanta su in sun rage biyu ko uku sai a kawo su, ni mace in fafata da su,” inji ta.
Misis Kasim, ta ce ganin babu mace ko daya a cikin sanatoci uku da ake da su ko ’yar majalisar jiha daa cikin 24 ya sa ta fito takarar don ganin ta kwato wa mata ’yancinsu a jihar. “Mata da yawa suna so su fito takara amma saboda rashin kudi da goyon baya daga maza ya sa suke baya-baya wajen fitowa a dama da su a zabe,” inji ta.
Ta yi kira ga matan jihar su fito kwai da kwarkwatarsu wajen mara wa mata ’yan uwarsu da suka fito takarar mukamai daban-daban a jam’iyyarsu ta PDP.
Ta ce idan ta zama Sanata za ta hada kai da Gwamnan Jihar Ibrahim Hassan dankwambo wajen gudanar da ayyukan raya kasa a yankinta na Gombe ta Kudu.