Na fuskanci kalubale da nasarori a rayuwata – ’yar fim Shan George
daya daga cikin ’yan fim din Najeriya mata da suka dade suna fuskantar suka da kwarmato, Shan George ta bayyana irin kalubale da nasarorin da ta samu a rayuwarta ta sana’ar fim.’Yar fim din, wacce a baya ake mata korafin cewa ta cika kashe aure kamar kuma yadda aka yi zargin cewa ta cika fitowa […]

daya daga cikin ’yan fim din Najeriya mata da suka dade suna fuskantar suka da kwarmato, Shan George ta bayyana irin kalubale da nasarorin da ta samu a rayuwarta ta sana’ar fim.
’Yar fim din, wacce a baya ake mata korafin cewa ta cika kashe aure kamar kuma yadda aka yi zargin cewa ta cika fitowa cikin tsiraici, ta bayyana cewa mafi yawan mutane suna sukarta ne ba bisa ka’ida ba. Asali ma, ta danganta irin wadannan korafe-korafe da cewa su ne kadan daga cikin kalubalen da take fuskanta, a matsayinta na ’yar fim.
“Wani babban kalubale da nake fuskanta shi ne, yadda masu kallo kan alakanta ni da fina-finan da na fito a cikinsu. Haka za ka ji ana zagi na, ana cewa ni mai hali kaza ce mara kyau, kawai saboda na fito a haka a fim. Ba zan taba mancewa da wani abu da ya faru da ni a Kasuwar Alade da ke Legas ba, inda na je in sawo wasu kaya. Wasu mutane na gani na, sai kawai suka fara jefa mani rubabben tumatiri.” Inji Shan.
Da aka tambaye ta, ko yaya take ganin ma’aikatar fina-finai ta Najeriya? Sai ta bayyana cewa a kullum tana gaya wa mutane cewa, su daina kwatanta harkar fim din Najeriya da ta Amurka, domin kamar mutum ya kwatanta yaro ne da aka haifa yau da tsoho dan shekara sittin. “Harkar fim a Najeriya tana ci gaba, amma akwai matsaloli nan da can, kamar wajen kasuwancin fim din da sauransu, kuma akwai alamun da ke nuna cewa nan gaba za a bunkasa, a fi haka.”
A yayin da take shawartar masu sha’awar shiga sana’ar fim, ’yar wasan ta ce, duk mai son shiga fim da farko, tana ba da shawarar ya fara dagewa ya samu ilimi. Kamar yadda ta ce: “Ilimi, shi ne ginshikin rayuwar da kaker son ginawa a rayuwarka. Na biyu, mutum ya kasance mai kokari da jajircewa, da maida hankali kan duk aikin da aka ba mutum. Da zarar ka kasance haka, to kafin ka ce wani abu, za ka gan ka cikin nasara.”