Na fuskanci kalubale sosai wajen rubuta littafina na farko – Abdullahi Bello
Ko za mu fara da jin tarihinka a takaice? Sunana Abdullahii Usman Bello. Ni dai mutumin Gombe ne kuma an haife ni a 1974. Daga nan na yi makarantar firamare da sakandare a Kano. Bayan na kammala makarantar Science Secondary School a Dawakin Tofa sai na je Jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi na […]
Ko za mu fara da jin tarihinka a takaice?
Sunana Abdullahii Usman Bello. Ni dai mutumin Gombe ne kuma an haife ni a 1974. Daga nan na yi makarantar firamare da sakandare a Kano. Bayan na kammala makarantar Science Secondary School a Dawakin Tofa sai na je Jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi na yi digiri a Kimiyyar Kwamfuta a 1998. Bayan nan na fara aikin hidimar kasa da farko a Jihar Imo kafin na dawo Abuja a Stanbic Merchant Bank. Bayan na gama sai suka dauke ni aiki amma daga baya sai na koma Afri Bank. Na yi kamar shekara 5 ina aiki a banki sai na koma Hukumar Yaki Da Ta’annatin Tattalin Arzikin kasa (EFCC) saboda sha’awar aikin da nake yi, a 2004. Mu ne rukunin ma’aikata na farko da aka bai wa horo a ma’aikatar, wanda ya hada har da na rike mukami, baya ga masaniya a bangaren al’amuran kudi da ka dauke da shi, inda na fara aiki a bangarensu da ke kula da sha’anin damfarar banki, a lokacin ofishin ma’aikatar na cikin fadar Shugaban kasa, kafin ya koma inda yake a yanzu (Wuse2).
Na yi ayyuka a bangarori daban-daban, ciki har da na manyan bincike da kuma kasancewa a cikin kwamitoci daban-daban. Bayan na yi kamar shekara 4 a ma’aikatar sai na yanke shawarar karo ilimi, inda na ajiye aiki a 2008. Sai dai kafin na tafi karatun, na samu aiki a wani kamfani mai suna Sandwich, inda na shugabanci bangarensu na tsaron kudi na shekara kamar daya a wajen sai na samu gurbin karatu a wata jami’a da ke Ingila mai suna Chebal Howell, inda na je domin Digiri na biyu a bangaren bin diddigin zirga-zirgar kudi (In-Forensic Accounting). Bayan na gama cikin shekara daya sai na samu wani gurbin karatu na Digirin-Digirgir a bangaren gano badda sawun kudi, (Money Laundering) wanda ya kunshi gano asalin inda kudi ya fito da kuma yadda aka badda shi, wanda na yi a Jami’ar Newcastle, duk a Ingila inda na samu tallafin rabin kudin daga jami’ar. Na yi kamar shekara biyu da rabi sannan na gama. Sai dai kafin ma na gama, jami’ar ta dauke ni aikin koyarwa kafin na yanke shawarar dawowa gida Najeriya a watan Disamba na 2015. Na sake samun aiki a hukumar EFCC a matsayin jagoran bangaren bin diddigin zirga-zirgar kudi da bincike a kai (Forensic Accounting and Financial Inbestigation). Na yi shekara daya da wata hudu ina aiki a wajen, wanda ya kunshi bincike a kan almudahana masu sarkakiya, bayan nan sai aka tura ni wani bangare mai suna Nigeria Financial Intelligent Unit (N.F.I.U) kafin na yanke shawarar yin ritaya a hukumar a watan Disamba ta 2017, a sakamakon sha’awar da nake da ita na kafa kamfani na kaina, don gudanar da ayyuka a wannan bangaren ga kamfanoni ko ma’akatun gwamnati, inda na kafa kamfani mai suna Abdubel Consultants.
Me ya ba ka sha’awar wallafa littafi a kan wannan bangaren?
Asalin littafin kundina ne na cika sharadin kammala karatun Digirin Digirgir (PhD). Abin da ya faru shi ne, Farfesan da ya yi nazari a kan rubutun da na yi don ganin ko na cancanta a ba ni PhD ko kuma ban cancanta ba, shi ne ya nuna sha’awar da in maida abin da na rubutan zuwa littafi. Wannan shi ne babban abin da ya ba ni kwarin gwiwar juya kundin zuwa littafi. Sai dai kuma dama ina da sha’awar zama marubuci tun a baya. Daga nan ne kuma sai na fara tuntubar manyan kamfanonin wallafa littattafai na duniya, har na hadu da Kamfanin Macmillan, wanda ke da cibiyoyi a manyan birane na duniya kamar 150, inda suka amince su wallafa littafin da kuma watsa shi zuwa cibiyoyinsu da kuma jami’o’i, ana sayar da su bayan yarjejeniya, na za su kasance masu ikon mallakar littafin, dama hurumin juya shi zuwa dukkan wani harshe da suke so, ni kuma na koma ban da ta cewa a kai.
Mece ce ribarka na buga littafin kasancewar duk abin da suka sayar nasu ne?
Ba ni da kobo a ciki bayan dan abin da suka ba ni na farko da ke matsayin na sallama. Da dai a ce ina koyarwa ne har yanzu, da wallafa littafin da suka yi na iya jawo mani karin girma kuma a rika gayyata ta zuwa wasu jami’o’i na duniya in ba da lacca a kan wasu darusan da ke cikin littafin a dalilin yada sunana da suka yi ta dalilin littafin. Sai dai marubuci ya samu kamfani irin wannan ya buga masa littafinsa kadai ba karamar daukaka ba ce. Tun tuni littafin na kasuwa sai dai na yanke shawarar sake kaddamar da shi ne a nan Najeriya bayan na karbi wani adadi daga ciki a kan wani kayyadajjen farashi da zan dora nawa a kai na samu wani abu. Farashinsa a manyan shagunan littatafai na duniya dala 99 ne ko kuma yuro 74 kamar yadda aka sa a internet. Sai dai ni idan na nema za a zabtare mani wani dan far shi. Kuma yanzu haka ma ina shirin yin sautun wasu kasancewar babban bankin kasar nan wato CBN sun bukaci kwafi 200 a lokacin kaddamarwar don raba su ga wasu wurare.
Mene ne babban abin da littafn ke karantarwa?
Littafin kamar yadda sunansa ya nuna wato Improbing Anti Money Laundry Compliance, yana magana ne a kan yadda za a kyautata tsarin gudanar da binciken almundahna ta dukiya, kama daga yadda za a gano su da sarkakiyar da ke cikinsa da kuma tasirinsa a tattalin arzikin kasa da kuma kalubalen da ma’aikatan ke fuskanta da dai sauransu.
Ka yi aiki har sau biyu a hukumar EFCC, kafin ka ajiye aiki. Yaya za ka banbance aikin wajen da wanda kake yi a yanzu?
Aikin da na yi a hukumar EFCC kayyadajje ne mai kuma dabaibayi idan zan kamanta shi da wanda zan iya yi a kamfani na kashin kaina. Sai dai dimbin sanin makamar aiki da na samu a wajen da na wuraren da na yi karatu da kuma kwasa-kwasai da na samu a kan aikin, zai ci gaba da taimaka mani a wajen yi wa kasa aiki a bangaren kamfanoni masu zaman kansu ko hukumomin gwamnati da ma ita kanta hukumar, ta hanyar yi mata aikin tuntuba da ba da horo ga jami’anta da ta dauka wanda abu ne da ake yi. Haka nan gwamnati a matakin kasa ko ta jiha za ta iya bai wa kamfaninmu aiki na tattara wasu bayanai da ta ke so a kan almundahnar kudi kamar na tona asirin masu almundahana.
Wane irin kalubaale za ka ce ka fuskanta a yayin rubuta littafin?
Kamar yadda na yi maka bayani, littafin ya kunshi darussan da suka shafi karatuna na PhD. ne da na mika, to farkon kalubale da na fuskanta shi ne na yadda zan tsara littafin tun a farkonsa kamar yadda yake ga kowane littafi, wato abin da ake kira da Turanci Methodology, wanda wannan ba bangarena ba ne. To, a nan ne na tuntubi wata Farfesa, wadda ta ba ni shawarar da na tafi Amurka don yin bincike a kai, inda na yi tattaki zuwa Jihar Carlifornia na samu wani Farfesa wanda ya kirkiro yadda ake tsara Methodology na littafi, ya koyar da ni a kan yadda zan yi bincike a bangaren da zai ba ni damar sauya tsarin littafin daga bayani kawai zuwa koyarwa. A lokacin da na fara sai na share kamar karfe daya na dare ina aiki a kai bayan na dawo daga wajen aiki. Haka nan kuma a lokacin ranakun karshen mako. Sannan bayan na yi sai na tura wa Farfesoshi kamar uku don su yi nazari da kuma ba da shawarwari a kai don yin gyara. Wannan ba karamin kalubale ba ne. Sannan da na tashi kaddamar da shi a nan Najeriya, Farfesa Abdullahi Shehu ne ya yi nazari a kai, wanda masani ne sosai a kan abin da ya shafi ilimin almundahnar kudi sannan ya taba rike mukamin darakta a wata kungiya mai kula da al’amuran a kasashen Afirka ta yamma baki daya.
A karshe, wane buri kake da shi a fagen wallafa?
Ai in sha Allahu na fara ke nan. Ina kuma fatan wannan littafin zai zame mani silar wallafa wasu rubuce-rubuce da na yi a baya kamar a bangaren bankin Musulunci da inshora (Islamic Banking and Insurance) da dai sauransu, da ma wadanda zan rubuta a nan gaba in Allah Ya yarda, kasancewar a dalilin littafin na koyi yadda ake fara rubuta littafi.
Ga masu sha’awar littafin kamar a ina ne za a iya samunsa?
Za a iya odarsa ta intanet ko kuma a bi ta wajena, inda hakan zai ba ni damar fa’idantuwa na samun wani abu daga sayar da shi, sannan ya saukake masu kudin safararsa daga waje ba tare da sun fuskanci karin kudi a kan abin da ake sayar da shi a kasar wajen ba.