Na ga abin mamaki a makabarta – Mai aikin makabarta

Aminiya ta samu tattaunawa da Malam Babangida Haladu, wanda ya shafe shekara da shekaru yana yi wa gawa wanka tare da binne mamata a makabartar Agege da ke jJhar Legas. A matsayinsa na shugaban masu lura da makabartar, ya bayyana yadda ya shiga aikin binne mamata da kuma irin abubuwan mamakin da y a rika […]

Na ga abin mamaki a makabarta – Mai aikin makabarta
Na ga abin mamaki a makabarta – Mai aikin makabarta

Aminiya ta samu tattaunawa da Malam Babangida Haladu, wanda ya shafe shekara da shekaru yana yi wa gawa wanka tare da binne mamata a makabartar Agege da ke jJhar Legas. A matsayinsa na shugaban masu lura da makabartar, ya bayyana yadda ya shiga aikin binne mamata da kuma irin abubuwan mamakin da y a rika gani a shekarun da ya yi yana aikin.

Ko za ka gabatar da kanka?

Sunana Babangida Haladu. Ni asalin iyayena mutanen Lahadin Makole ne a Jihar Kano amma ni a Legas aka haife ni shekaru 72 da suka wuce. Na yi aiki a Kamfanin Sufurin Jiragen Sama na Najeriya a Jihar Legas daga bisani sai na dawo yi wa mamata hidima a makabartar Agege, inda yau na yi kimanin shekaru kusan 40 ina yin wannan aiki saboda Allah.
Wadannen irin ayyuka kake yi a nan makabartar?
Muna yi wa gawa wanka da kuma binne ta. Duk wani abu da ya shafi yi wa gawa hidima ni ne nake yi tare da sauran abokan aikina.
Tun lokacin da ka fara aiki a wannan makabarta za ka iya sanin yawan gawarwakin da ka binne?
Gaskiya ba zan iya sani ba saboda ba kirgawa nake yi ba kuma ba mu da wata rajista da muke kayyade gawarwakin da aka kawo makabartar nan. Amma abin da zan iya cewa shi ne, a shekarun da na yi ina binne gawa na binne mutane da yawa.
Ta yaya aka yi ka shiga wannan sana’a?
Na shiga wannan sana’a ce saboda Allah don neman ni ma Allah Ya yi mani gafara saboda hidimar da nake yi wa gawarwaki. Sannan kuma ita wannan sana’a aba ce ta sa-kai, ba don samun wani abin duniya ba. A shekaruna a yanzu me nake nema a duniya? Ba na neman komai tunda shekaruna sun ja. Muna dai fata Allah Ya ji tausayinmu, ya gafarta mana.
Shin lokacin da ka fara wannan hidima, ya iyalanka suka ji?a
Ai su iyalaina ba su ji komai ba, su dai na kawo musu abinci su ci. Sun rika kara mini kwarin gwiwa tare da yi mani addu’ar Allah Ya sa na gama lafiya. Kuma babu abin da zan ce sai san barka da kuma neman Allah Ya karbi ayyukanmu, ya sa mu cika da imani.
Shin ka taba gamuwa da wani abin tsoro ko kuma wani abu da ya ba ka mamaki a shekarun da ka yi kana wannan aiki?
E! Abu daya ne ya taba ba ni mamaki. Wata rana muna haka kabari ni da abokin aikina, sai muka hako wani kabari da babu komai a ciki. Ga shi kabari ne a hake da komai da komai amma babu alamun an taba sanya mutum a ciki. Sai na ce wa abokina wannan kabari Allah Ya yi ikonsa, ya dauke wanda yake cikin kabarin. Daga nan sai na ce tunda abin ya zama haka, mu binne gawar da aka kawo a ciki, sai muka binne gawar da aka kawo muka rufe. Dalilin da ya sa na yi mamaki shi ne ban taba ganin irin wannan abin al’ajabi ba. Domin dukkanin kabarin da muke hakawa idan mun tadda tsohon kabari dole mu ga alamar an binne wani a ciki, ko dai mu ga likkafani ko kuma kasusuwa ko kuma burbushin katakon da aka binne shi da shi. Amma shi wannan ga shi sabon kabari ne amma babu komai a ciki.
Shin ka taba samun gawa da ta farfado yayin da kake yi mata wanka?
Ai shi mutum in dai har ya mutu to ba zai taba tashi ba, saboda haka na taba samun wani mutum da aka kawo shi, zan yi masa wanka sai na ga yana yin numfashi. Sai na ce a kai shi asibiti likita ya duba shi. Ana zuwa asibitin ashe tuni ya karasa a kan hanya, sai likita ya tabbatar da cewa ya riga ya mutu, sai muka dawo da shi muka yi masa wanka muka binne shi. Kuma tunda nake aiki a wannan makabarta ban taba ganin wani abun ban tsoro ba. Ko zancen da mutane suke yi cewa ana ganin aljanu da fatalwa duk karya ne.
Ina batun da ake yi cewa akan ga micizai da kunamu a kabari?
Da ne muke ganin mijizai a cikin makabartar amma yanzu ba mu ganinsu. Mukan ga kunama ko yau ma na ga kunama. Amma a cikin kabari ba ma ganin manyan mijizai sai dai kanana wadanda ba su cutarwa. Su kuwa wadannan idan muka gansu babu ruwanmu da su sai mu ci gaba da aikinmu.
Kun taba haka kabari kuka ga mutumin bai rube ba?
Ba mu taba gani ba. Ai duk mutumin da aka binne ba zai taba zama haka ba sai ya rube. Duk wanda ya yarda aka binne shi ko da bai karasa mutuwa ba to dole ya mutu. Saboda haka zancen da mutane suke yi cewa an binne wani an gan shi ya tashi, yana jan carbi a kan kabarinsa ko kuma a ce an gan shi yana yin Sallah karya ne. Ba mu taba ganin haka ba amma za ka ji mutane suna yada karya da jita-jita a kan haka. Duk wanda Allaha ba Ya so kasa ta ci shi sai ya dauke shi daga kabarin.
Akan biya ka albashi sakamkon aikin da kake yi a nan?
Ana ba mu dan albashi amma alherin da muke samu daga jama’a ya fi karfin albashin. Saboda ana ba mu sadaka da abinci da sauran abubuwa kuma da shi muke ciyar da iyalanmu, mu biya haya da kudin makarantar yara. Ba ma karbar komai daga wurin jama’a na binne gawa ko yi mata wanka.