Na ga jirgi
Wani Banufe ne ya je Kano, to sai hanyarsa ta kai shi kusa da filin jirgin sama. Shi bai saba ganin jirgi kasa-kasa haka ba a Bidda, ga jirage nan sai wucewa suke kasa-kasa. Yana so ya daga kai ya gani amma yana tsoron za a yi masa kallon dan kauye. Sai ya tambayi bandaki […]
Wani Banufe ne ya je Kano, to sai hanyarsa ta kai shi kusa da filin jirgin sama. Shi bai saba ganin jirgi kasa-kasa haka ba a Bidda, ga jirage nan sai wucewa suke kasa-kasa. Yana so ya daga kai ya gani amma yana tsoron za a yi masa kallon dan kauye. Sai ya tambayi bandaki zai kewaya, ya dauki buta ya shiga ya kulle. Ya ajiye butar a gefe, ya daga kansa sama yana kare wa duk jirgin da zai wuce kallo. Can ya fito ya yi hamdala, sannan ya ce a ransa: “Yau kam na ga jirgi.”
Daga Abdullahi Musa Hadeja, 07066180429