Na ga tsabar rashin imani a hannun ’yan bindiga —Farfesa Aliyu
A kan idona suke kashe mutane suna ba karnuka
Farfesa Aliyu Mohammed, wanda ya kubuta daga hannun ’yan bindiga ya bayyana wa Aminiya halin da ya shiga da rashin imanin da ya gani a wurinsu.
Ga yadda tattaunawarmu ta kasance da Shugaban na Sashen Kimiyyar Noma a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi wanda amasu garkuwa suka sace a Zariya ya kuma kwashe sama da mako uku a hannunsu:
- Maharan Dikwa ba yaren ’yan Najeriya suke ba’
- Mutum biyu sun mutu bayan karbar rigakafin Coronavirus
- Kungiyar OPC ta kone kauyen Fulani ta kashe mace mai ciki a Oyo
Yaya aka yi masu garkuwa da mutane suka sace ka?
Na dawo gida da misalin karfe 9:30 na dare, ban jima ba sai dana ya dawo da motarsa ya ajiye ya fita.
Da ma na bar wayata a cikin mota ina caji sai na tafi don in dauko; Kuma na saba kafin in shiga cikin gida, sai na dan zagaya don in tabbatar babu matsala.
Ina cikin zagayen ne na fito kofar gida da waya a hannuna, kawai sai na ga mutane sun nufo gidana da bindigogi ga shi kuma babu inda zan gudu.
Da suka iske ni sai suka hauni da sara da duka sannan suka zaunar da ni da karfin tsiya sai suka ce abin da ya rage shi ne su shiga cikin gidan.
A nan sai iyalina suka ji kururuwata, sai Allah Ya ba su hikima suka boye a dakin dafa abinci.
Koda suka shiga cikin gidan ba su samu kowa ba sai dana Abdul’aziz wanda suka kashe, daga nan sai suka lalata duk wani abu mai amfani a gidan.
Suka yi kokarin bude kofar bayan gida, ba ta bude ba sai suka yi tunanin iyalina sun fita ta wannan kofa daga nan suka dawo suka tafi da ni.
Duk da harbe-harben da sojoji da ’yan sanda da ’yan sintiri suke yi daga nesa amma ba su zo kusa da inda muke ba, har suka tafi da ni.
Kuma bayan haka akwai dana da ya dawo a babur suka harbe shi amma bai rasu ba.
A kafa suka zo ko a abin hawa?
Dukkansu da kafa suka zo kuma sun zo gidana kimanin su 15 kowannesu dauke da bindiga, amma da za su tafi da ni ashe sun wuce haka, sun rarrabu ne a wurare saboda fuskantar duk wanda zai kawo dauki. Kafin mu bar uguwarmu yawansu ya kai 30.
Kun yi tafiya kamar kilomita nawa?
Tun karfe 10:00 na dare muke tafiya sai misalin karfe 1:30 na dare suka tambaye ni, ka san wancan haske ina ne? Sai na ce musu a’a. Sai suka ce hasken fitilun Jaji ne.
Daga nan sai suka dauko babura biyu muka hau, wanda aka dauke ni mu hudu ne kowannensu da bindiga. Haka muka tafi har gari ya waye kafin muka kai bukkarsu.
Yaya rayuwa ta kasance a can?
Rayuwa ce wadda ba mai dadi ba.
Da isarmu suka sanya min sarka aka kuma daure hannuwana ga daurin sama ga na kasa kuma, in suka zo da ayarinsu da safe ko da yamma duk zuwa duka suke yi min. Sai su ce za a ba mutum shayin safe da na yamma.
Sun kuma fada min cewa an fada musu cewa ni mai kudi ne, ina da gidaje da motoci, ina kuma da shanu, kuma ina da hanyoyin samun kudi da yawa saboda haka zan biya Naira miliyan 20.
Sai na ce musu ba ni da kudi, gidan da nake ciki shi kadai na mallaka.
Suka ce ba su yarda ba, kafin su je su dauki mutum sai sun tabbatar da abin da yake da shi kuma sun fada min ina da suruki kanen Albani wanda wai yake aiki a Ma’aikatar Man Fetur, wai shi ma yana da kudi.
Tun daga nan suka ajiye ni cikin ukuba ta safe daban, ta rana daban, ta yamma daban.
Duk yamma za a kwance mu a sarka a umurce mu da mu je mu yi itacen girkin abinci kuma da shi ne suke jin dumi.
Daga baya suka dawo Naira miliyan 10. ’Yan uwa da abokan arziki suka hada miliyan 10 aka kawo musu, amma sai suka ce ai rabin kudin aka kawo.
Kanena da ya kai kudin sai suka ce ya koma shi daya ba za su sake ni ba.
Sakamakon haka sai da na kara kwana 15 a hannunsu, kuma ana ta kokarin yadda za a hada sauran Naira miliyan 10 da suka bukata.
Duk lokacin da shugabansu ya zo ana kwance mu don mu je mu yi gaisuwa, a wani lokaci ne da muka je yin gaisuwa sai shugaban ya nuna ni ya ce da yardar Allah yau za ka gida.
Ashe sun yi waya da kanena cewa kudi sun hadu zai sa a zo a dauko ni, da aka zo aka dauko ni sai aka je aka ajiye ni a wata bukka, masu karbar kudin suka yi gaba suka karbi kudin suka kirga, sai suka ce a zo da ni.
Sai suka min sallama cewa Farfesa yau za mu rabu da kai, ga shi muna son zama da kai. Sai ka yi ta yi mana addu’a, Allah Ya kai ku lafiya ga hanyar da za ku bi har zuwa Galadimawa.
Da ma surukina ya zo kusa a mota, shi ne ya dauko ni zuwa asibiti aka fara duba lafiyata saboda sarar da suka yi min a kai.
A lokacin da aka kai ka mutum nawa ka samu a can?
A ranar da aka tafi da ni ban samu kowa ba, washegari ne aka kawo mutum daya bayan kwana shida aka kawo mutum uku sai muka zama mu biyar.
Ko ka bar wadansu a can?
Babu wanda aka saki a gabana, amma akwai mutum biyu da aka kashe.
Akwai wani da ake kira Alhaji Kadade wanda aka kawo shi ina da kwana daya, kuma sun harbe shi tun kafin nan.
Takaddama aka yi da ’yan uwansa an ce su kai Naira miliyan hudu suka roki ragi aka ce su kai miliyan uku da rabi sai suka kai Naira miliyan uku. Sai suka ce sun raina musu hankali.
Bayan an kai kudin, sun karba, washegari da Magariba suka kai shi wani kwazazzabo suka harbe shi, sannan suka ce idan na yi wasa haka za a yi min.
Bayan kwana shida sai aka zo da wadansu mutane su uku. Akwai makwabcina mai suna Saleh da wani dalibi da Umaru dan sintiri.
Sai na ji suna cewa akwai wani shugaban ’yan banga, da an zo da shi kashe shi za su yi, zuwa Magariba sai suka taru suka rufar masa da duka sai da suka ga ba ya da rai, a nan gawarsa ta kwana a gaban bukkarmu.
Da gari ya waye sai suka ce mana mu je mu ja gawar suka nuna inda za mu kai, suka ce kamar yadda suka yi wa wannan haka za su yi wa duk wanda ya yi wasa.
Suka ce sun kamo mu don kudi ne, in ba kudi, to kashe mu za su yi.
Na roki su bar ni, ko ni kadai in yi masa kabari in binne shi, sai suka ce a’a, a bar shi kawai karnuka su samu abinci, kuma haka aka yi.
Kuma haka suka kamo wani daga Giwa suka zo da shi sai suka ce a fara kai shi ya ga gawarwakin wadanda aka kashe domin saboda da ya san cewa shi ma in ya yi wasa da kudi haka za a yi masa.
Yaya rayuwarsu take tunda suna samun kudi, amma a suke zaune a cikin daji?
Rayuwar daji ai ba yadda za a ce tana da dadi, don ko ka samu kudi babu yadda za ka ji dadinsu.
Don kudi suna samu, amma babu wata kasuwa ko makaranta ko wani wuri da za a ce an kashe kudin an ji dadi saboda sun ce ko gari ba su zuwa, sai dai in sun zo yin sata, saboda haka shi ya sa suka tafiyar da rayuwarsu a cikin daji.
Sallar ma da nake yi suka soke sai na ce shi ke nan ga shi ba wanka ba wanki ba aski ba yanke kumba babu yin Sallah a wadannan kwana 25 da na yi a hannunsu.
Wace shawara za ka bayar don kawo karshen wannan matsala?
To, abin da suke fada min a hirar da na rika yi da su a lokuta da dama, shi ne cewa su gwamnatin ba ta yi musu adalci ta yadda yake ko kasuwanni ba su isa su je ba, haka ba su isa su je karkara ba duk inda aka ga Fulani, ana ganin masu laifi ne, sai a kama su da duka ko a kashe su ko a ci mutuncinsu.
Shi ne suke ganin an mayar da su saniyar ware a Najeriya wannan ya sa suka tattara kansu zuwa daji don ci gaba rayuwa.
Amma kamar yadda suke magana suna da ra’ayin a yi sulhu a tsakani don a samu masalaha.
Idan gwamnati tana tunanin amfani da karfin makami to mutanen suna da makamai.
Misali idan suka fito yin ta’adi soja ko dan sanda ba za su iya tsare ka ba, domin a lokacin da aka kama ni, sojoji da sauran jami’an tsaro sun yi ta harbi amma bai hana su tafiya da ni ba.
Saboda haka shawarar da zan bayar, ta farko mu koma ga Ubangiji a dage da addu’a dare da rana domin ita ce za ta magance wannan matsala.
Ta biyu gwamnati ta fahimci cewa suna da shirin da ba a tunani, ko ta gwada zama da su a matsayinsu na ’yan kasa, ko ta sa su a tsare- tsarenta ko kuma ta yi shirin da ya fi nasu domin babu gagararre sai bararre.
Amma a fahimtana shirinsu ya fi na gwamnati a yanzu.