Na ga wallen Mikiyar ta-mola

A rana ta kwanciyar magirbi ga watan Yawon-wulli na shekara ta dubu karamin lauje da sili da zagaye, na fito daga mafuskantar alkibla don kadaita Mahalicci da ibada, sai wani abokin kwadagona ya kalle ni ya ce ‘man kaza,’ ashe bai sani ba, Baffan Editocin Kamfanin Buga Amintattun jaridun kasar Haurobiya na saurarensa. Ni dai […]

Na ga wallen Mikiyar ta-mola
Na ga wallen Mikiyar ta-mola

A rana ta kwanciyar magirbi ga watan Yawon-wulli na shekara ta dubu karamin lauje da sili da zagaye, na fito daga mafuskantar alkibla don kadaita Mahalicci da ibada, sai wani abokin kwadagona ya kalle ni ya ce ‘man kaza,’ ashe bai sani ba, Baffan Editocin Kamfanin Buga Amintattun jaridun kasar Haurobiya na saurarensa. Ni dai na ja bakina na tsuke. Shi kuwa wanda ya tafka wannan kwakyariya dai yaron GizBaba ne,  kuma su ke yi mana karaji da ihu a lokacin da mikiyoyin Haurobiya ke fafatawa a gasar cin modar tamolar duniya a kasar Barazana-da-zilliya.
Abokin kwadagona bai gushe ba, sai da ya kara kirana da ‘man doguwar dabba.’ To, wannan zan iya yarda, domin na ziyarci Tenhiya, gari mai doguwar dabba, garin Ahmad Aghali Ibba. Don haka ma na samu martaba, har wasu ke ganin Jinjiniyar dodanniyar gidana ita ce ‘man rago, amma duk wani dan dugwi-dugwi, ai “man kaza ne,’ musamman masu yekuwar kwarzanta dukan tamola da harbatta mati.
Kada dai  a ce na cika shataletale da walankewa irin na dodanni, abin da kawai nike son nusar da ’yan dugwi-dugwi abokan GizBaba, wadanda ke ta yaba kwazon mikiyoyin Haurobiya, shi ne, su sani harkar tamola da harbatta mati ba za su kai Haurobiya ga gaci ba, musamman ma jin cewa an raba wa tsakin mikiyoyin Haurobiya Hauro malala gashin tunkiya karamin lauje da sili da dubu tsayuwa bisa kafa daya, a matsayin ladar tabarar da suka yi a kasar Barazana-da-zilliya.
Batu na ingarman karfe, Gwamnatin kasar Haurobiya ta tsara yadda ’yan dugwi-dugwi za su daina sha’awar koyon watsattsake da buda wagagen littattafai, don fafutikar kwarewa a fannonin inganta rayuwar al’umma. Kuma ko suna sha’awa, ai gwamnatin Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge ta tsara kulle-kullen cin dunduniyar jami’an Asusun ilimi da ke kula da jam’in jama’ar jami’o’in Haurobiya; ta shiga takun saka da malaman fasaha da kere-kere, su kuwa direbobin alli da ke tuka ’yan dugwi-dugwi don kai su ga gaci, an kassara su, inda aka bar su ‘babu lada, ba la’ada.’
Haurobiyawa, kada fa ku dauka cewa ko Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge ta tafka ta’asa a kwanon tasa, a’a, ta dai shiga sa-in-sa da ku ne, saboda kun ki yin likimo ku more irin wannan gwaggwabar garabasar damo-da-kura da diyya da aka fara difara muku tun daga shekara ta alif sili da manuniya kasa da ta kasa da ta kasa har zuwa dubu karamin lauje da sili da tsayuwa bisa kafa daya.
Haurobiyawa ku shiga taitayinku! Mai danboto na shirin kai kasar nan kasa warwas!
Jiga-jigan Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge da mukarraban Shugaba Jatau Mai Sa-in-sa da Haurobiyawa a wajen jonatantin mulki su kadai ke cabawa. Ga shi nan dai Madam In-gwangwaje-in-wala ta bari a wawushi damin Hauro gashin balama, aka jinka wa mikiyoyin Haurobiya, alhalin bokayen turai na yajin aiki; ga dimbin kayukan kayau da ke fama da tsilli-tsillin matsalolin rayuwa. Kodayake ma, ai wannan matsalar talakawan Haurobiya kawai ta shafa. Su ma talakawan in ban da wauta, ‘yaya za a yi taguwar mutum ta kece, sannan ya bukaci jiga-jigan kasa su sanya zaren lilo da basilla don dinkewa?’
Batu na waskiya, yaran da ke rausayawa a bayan kangon Gizo-gizon dakin gwaggwago za su bude filin dukan tamola, har sai sun kware a harkar harbatta mati, ta yadda wata rana a tafi da su kasar Barazana-da-zilliya, don su samu zillewa da damin Hauron Haurobiya. Kuma wannan na nuni da cewa a kasar Haurobiya an fifita tamola a kan watsattsake da buda wagagen littattafai; an kuma fifita harbata mati a kan kula da uwar jikin al’umma. Uwa-uba, an daukaka juhala akan adala.
Wadanda suka samu gararumar gyaran jar miya a mulkin mai dan boto da sanda jirge haka za a yi ta harbatta mati da kwakwalenku, ta yadda da zarar sun cillo muku gurneti da nakiyar masu haramta bobo da kwambon bokoko, sai su ce mun shawo kan matsalar, alhali an riga an yi wa al’umma ‘sakiyar da babu ruwa.’ Sanin kowa ne tun da aka haifar wa Haurobiyawan Jihar Bararon-nono (Alanguburo) da Ciwon-cibin boko, sai zuki-ta-malle iri-iri ake sharawa; ta safe daban, ta marece daban. Can ma a Jihar Yawon-Bebe, musamman mazaunan birnin Dama-tumatur ba su sha da dadi ba.
Batu na ingarman karfen karafa, ina mai sanar da Baffan Editoci Kukana ya fi na Tenhiya, amma don kada in ci gaba zubar da hawaye, ya kamata a ba ni kangon GizBaba in gina katafariyar makaranta, mai manhaja mara hajijiya, wadda za ta nusar da Haurobiyawa yadda za su kawar da juhala, su tabbatar adala.
Ni dai, na ga wallenki mikiyar tamola. Na ga baiken daukacin mikiyoyin Haurobiya!