‘Na ga yadda ake horar da yara su zama ’yan bindiga’

‘Suna kashe mutum su ba namun daji; na ga Farfesan Jami’ar ABU a wurinsu

‘Na ga yadda ake horar da yara su zama ’yan bindiga’
Aminiya ta gana da daya daga cikin wadanda fitaccen dan bindigar nan Kachalla ko Na Kachallah da aka kashe a makon nan ya taba sacewa sai da aka biya fansar Naira miliyan hudu kafin sako shi.

Ya  ce ya ga malamin Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) a dajin da aka ajiye su, sannan ya ga yadda ake koyar da kananan yara yadda za su zama ’yan ta’adda.

Yadda suka kama su

Ya bayyana yadda aka bude wa motarsa wuta a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari a kusa da kauyen da ake kira Rumanan Gwari kusa da garin Buruku.

Ya ce da suka bude wa motarsa wuta sai ya tsaya suka zagaye motar dauke da bindigogi “Ina fitowa daga cikin motar suka fara duka na har sai da na fadi kasa daga nan suka tasa keyarmu tare da sauran mutanen da muka kama matafiya zuwa cikin daji.

“Sai da muka yi tafiyar kusan mil uku kafin muka isa inda suka ajiye baburansu.

“Mun yi tafiyar kusan sa’o’i uku a kan babur sannan muka isa maboyarsu inda suka daure mu da sarka.

“Mun sha duka sosai a hannunsu a lokacin yi mana tambayoyi, wai sai mun fada musu abin da muka mallaka.

“Na yi kokari wajen yi musu bayanin abin da na mallaka sun kuma ce wai ba suna dukan mu ba ne don mun yi musu laifi, sai don kawai kudi suke so.”

 

Yawan ’yan bindiga da suka sace mu

“Suna da yawa domin sun kai mutum ashirin, kuma  akwai tsofaffi a cikinsu da kuma matasa.

“Na gabatar da kaina gare su da kuma abin da na mallaka sai suka ce akwai bukatar in sanar da ’yan uwana a sayar da kaddorina domin a kawo musu Naira miliyan 50.

“Sun tabbatar min da cewa da zarar an kawo kudin za su sake ni in tafi gida.

“Sai na sanar da ’yan uwana cewa su sayar da kaddarorina domin a sake ni.

“Daga bisani sun rage kudin fansar zuwa Naira miliyan 20, har aka dawo kasa da haka.

“Amma saboda ba a samu kudin da wuri ba, kusan kullum sai sun duke mu.”

 

Kwanakin da na yi a tsare

“Na kwashe kwana 12 a hannunsu kafin a sake ni.

“Abin da kawai ya dame ni, shi ne wadansu daga cikin ’yan ta’addar sun bayyana niyyarsu ta yin sulhu domin sun gaji da abin da suke yi.

“Sun kuma nuna min cewa an kashe musu abokai da ’yan uwa sannan aka lalata musu dukiyoyi wanda hakan ya sa suka shiga harkar garkuwa da mutane.

“Sun ce idan gwamnati na son a zauna lafiya su ma suna son haka, kuma a shirye suke a tattauna da jami’an tsaro.

“Idan kuma gwamnati ta ki, su ma za su ci gaba da aikata abin da suke yi.”

Da aka tambaye shi ko ya ga an kashe wani a dajin sai ya ce, “Kwarai kuwa suna kashewa domin tsorata mu.

“Mutum na farko da suka kashe wani tsoho ne saboda ba ya da wayar da za a kira ’yan uwansa.

“Saboda haka sai suka ce ba ya da amfani a wajensu kuma ba za su ci gaba da ciyar da shi ba, don haka shugabansu ya ce kawai a kashe shi.

“Shugabansu ya ba da umarnin a rufe masa fuska da wani kyalle sannan suka kai shi saman wani dutse kafin suka harbe shi.

“Suka bukaci mutum uku daga cikinmu su dauki gawar su shigar da ita cikin daji su jefar domin namun daji su ci.

“Haka kuma akwai wanda shi ma aka nemi wayarsa amma ba a gani ba duk kuwa da ya ce su suka karba a ranar da suka kama shi.

“Da bai samu damar kiran ’yan uwansa ba, sai ya ba da lambar wani dan uwansa amma saboda dan uwan ya ce Naira dubu 100 za su iya biya, sai suka ce rainin wayo ne ake neman yi musu, don haka sai suka rufe masa fuska aka harbe shi sannan mutum uku daga cikinmu suka dauke shi suka kai cikin daji suka ajiye gawarsa.

“Bayan kwanaki da muka shiga daji nemo itace sai muka tarar da gawarsa duk namun daji sun cinye wasu sassan jikinsa.

“’Yan ta’addan suka fada mana cewa mu ma idan ba mu yi hankali ba haka za a jefar da gawarwakinmu.”

Yadda aka sake ni

“Sai da na biya Naira miliyan hudu kafin suka sake ni.

“Sun fada min cewa idan kudin sun cika za su kyale ni.

“Bayan sa’o’i sai suka ce in cire rigata daya, suka rufe min fuska sannan suka dora ni a kan babur har muka fita wani waje mai nisa sannan suka cire min kyallen a fuska suka tambaye ni ko na gane wanda ya kawo kudin fansar na ce musu eh, sai suka ce to in bi shi tare da yi mana fatar Allah Ya kiyaye hanya.”

Ko za ka gane wajen da aka ajiye ka?

“Eh, a kusa ne da Sabon Birni kusa da dajin da ke Rigachikun a kan hanyar zuwa Dogon Dawa.”

Ko ka sayar da kadarorinka kafin a samu kudin fansarka?

“Gaskiya ne ba ni da kudin da suka bukata amma ina da gidaje biyu a kauye don haka sai aka sayar da daya a kasa da Naira miliyan daya amma sauran kudaden ’yan uwana ne suka hada.

“An kuma sako ni ne a ranar Asabar, 19 ga Disamban da ya gabata.”

Ina ka ga motarka?

“Lokacin da aka kama ni, na tambaye su ko zan iya tafiya da makullan motata, sai suka ce duk yadda na so. Don haka sai na tafi da su. Shugabansu wanda ake kira (Nasiru) Na-Kacallah (wanda rahoto ya nuna an kashe shi wajen rabon dukiyar mutane da suka kwace) ya karbi makullan daga wajena, sannan ya tambaye ni a ina motar take na fada masa.

“A lokacin da za a sake ni na tambaye su makullan motar amma sai suka ce wai suna wajen Na-Kachallah shi kuma a lokacin ba ya nan ya yi tafiya.

“Amma daga baya na ga motar a ofishin ’yan sanda da ke Buruku.”

Mutane nawa ka bari a dajin bayan an sake ka?

“Na bar mutum uku sai dai ban sani ba ko biyu daga cikinsu za su tsira, domin sun ce su mutanen kauyen Badarawa ne a Karamar Hukumar Shinkafi a Jihar  Zamfara.

“Saboda babu damar kiran waya a kauyensu sai sun kira dan uwansu da ke Kano ko Legas wanda zai kira wani da ke kusa da garinsu kafin ya kai waya wajen wani dan uwansu da za su yi masa magana.

“’Yan ta’addan sun amince a biya Naira dubu 300 kafin daga baya su rage kudin zuwa dubu 200, amma sai ’yan uwansu suka ce su fa Naira dubu 100 kawai za su iya biya.

“Ni dai na bar wajen ne ana jiran Na-Kacallah ya zo kawai ya ba da umarnin a kashe su.

Abincin da ake ba mu

“A kwana 12 da na yi a tsare, taliya suke ba mu sau biyu a rana sai dan ruwan sha kadan da suke ba mu, kuma babu na alwala hakan ya sa Sallah sai dai ka yi ta a cikin zuciya.”

Akwai mata a cikinsu?

Mun tarar da mata biyu a wajen kuma a cikin wadanda aka kama mu tare akwai mace daya sai dai ba su dukan mata domin su ke girka abinci.

“Babu mata ’yan bindiga cikinsu sai dai yara ’yan kasa da shekara 10 zuwa 15 da ke tsare mu.

Wanda ya gane cikin wadanda aka yi garkuwa da su?

Akwai wani Farfesa daga Jami’ar Ahmadu Bello  (ABU) da aka kama wanda suka ce sai an ba su Naira miliyan 10.

“An ba su miliyan biyu amma sun ce wai kudin abinci da alburusai da suka batar wajen harbe-harben da suka yi da jami’an tsaro ne don haka sai an karo musu miliyan 8 kafin su sake shi.

“Ya fada min ba ya da wannan kudi da suka bukata kuma shi ma sun doke shi domin an kama shi kafin mu sannan ya yi kusan wata daya a hannunsu ga shi yana da kusan shekara 60 a duniya.

Shawara ga gwamnati

Abin da na lura shi ne ba na tsammanin gwamnati za ta iya magance wannan matsala saboda haka ina ganin akwai bukatar sasantawa da su, domin mutanen kauyuka su zauna lafiya da kwanciyar hankali.

“’Yan ta’addan Birnin Gwari sun ce babu inda za su kuma duk wanda ke bin hanyar yana cikin hadari.

“Kuma ga shi mu ba mu da wata hanyar da za mu rika bi in ba wannan ba.