Na gaji bashin 8.9bn a matsayin shugaban APC — Ganduje
Amma Ganduje ya ce jam’iyyar na ɗaukan matakan da suka dace don rage yawan bashin.

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa shugabancinsa ya gaji bashin Naira biliyan 8.9.
Ganduje ya bayyana haka ne a Abuja yayin taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar APC.
- Boko Haram sun sace mutum 2 da kayan abinci a Borno
- Buhari da El-Rufai ba su halarci babban taron APC ba
A cewarsa, wannan bashi ya samo asali ne daga kuɗaɗen da aka kashe a shari’o’i kafin zaɓe, ƙalubalantar sakamakon zaɓe, da ƙarar da aka shigar da ’yan majalisu, gwamnoni, da na shugaban ƙasa.
“Shugabancin kwamitin zartaswa na ƙasa na yanzu ya gaji bashin Naira 8,987,874,663 da kuma tari shari’o’i daban-daban,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa mai bai wa jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a, Farfesa Abdul Kareem Kana (SAN), na aiki don rage wannan bashi.
“Muna sake roƙon Kwamitin Zartarwa na Ƙasa da ya taimaka domin shawo kan matsalar,” in ji Ganduje.
Taron ya samu halartar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, Mataimakinsa Kashim Shettima, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, gwamnonin jihohi da wasu manyan shugabannin jam’iyyar.