Na gaji sana’ar wasa da maciji daga kakana – Zainab Sarkin Gardi
A bisa al’ada, akan sami mazaje masu jarunta da kan yi wasa da dabobbi masu hatsari kamar su kura, biri ko macizai domin samun taro da kwabo. Sai dai a wannan karon, wata mace ce mai kamar maza wacce ta kware wajen wasa da macizai, a inda take rataya shi a wuyanta, ta sanya kansa […]
A bisa al’ada, akan sami mazaje masu jarunta da kan yi wasa da dabobbi masu hatsari kamar su kura, biri ko macizai domin samun taro da kwabo. Sai dai a wannan karon, wata mace ce mai kamar maza wacce ta kware wajen wasa da macizai, a inda take rataya shi a wuyanta, ta sanya kansa a cikin bakinsa tana kuma ba shi umarni ta hanyar yi masa Magana, duk da sunan sana’a.
Matar mai suna Zainab Sarkin Gardi Malumfashi, ta shaida wa Aminiya cewa ta gaji sana’ar wasa da maciji ne a wajan kakanta na bangaren uwa, wanda shi ma shahararre ne a sana’ar wasa da maciji. Ta kuma kara da cewa ita ’yar asalin garin Malumfashi a Jihar Katsina ce. Ta ce takan karade garuruwan Kurmi, inda take gudanar da sana’arta domin neman taro da kwabo. A cewar ta, idan ka ga mutum na wasa da maciji aka ce ya yi cizo, to bai san aikinsa ba ne. “Idan ka iya aiki da maciji, kafin ka fito neman kudi da shi sai ka nemi alfarma, ka gaya masa cewa arziki ka zo nema ba tsiya ba; duk wanda ka gani arziki a ka zo ci wajensa. Duk lokacin da ka ga maciji ya yi cizo, to an yi masa mugun ruko ne ko an nemi cutar da shi, domin ko a dawa in maciji ya ga mutum gudu yake, shi ma mutum din yana gudu.” Inji Zainab mai wasa da macizai.
Ta ce koda an sami kuskure micijin ya ciji wani daga cikin masu kallon was anta, to tana da maganin da za ta ba shi, cikin minti goma ya sami sauki; sai dai in abin ya zo da karar kwana. Ta shaida cewa a karo guda ne kacal ta taba fuskantar matsala a wasa da maciji, a lokacin da wani maciji ya nemi hallaka ta amma Allah Ya tsare ta, sakamakon addu’ar da ta yi a wannan lokacin. Ta kara da cewa ta sami amfani kwarai a sana’ar wasa da maciji, domin kadarar da ta tara da wannan sana’a, Allah Ya yi mata yawa da albarka. “Ko a yanzu na sami mijin aure, na yi aure, na bar sana’ar, na ci riba kwarai.” Inji ta.