Na gina gida da sana’ar gasa gurasa – Saminu Maigurasa

Duk da kasancewar sana’ar gashin gurasa sana’a ce da aka fi saninta tsakankanin mata, amma akwai wani matashi, mai suna Saminu Adamu wanda ya kware a sana’ar kuma shafe kimanin shekaru 15 yana gudanar da ita.Matashi dan kimanin shekara 27, yana zaune ne a unguwar Shatsari a yankin karamar Hukumar Dala cikin birnin Kano, ya […]

Na gina gida da sana’ar gasa gurasa – Saminu Maigurasa
Na gina gida da sana’ar gasa gurasa – Saminu Maigurasa

Duk da kasancewar sana’ar gashin gurasa sana’a ce da aka fi saninta tsakankanin mata, amma akwai wani matashi, mai suna Saminu Adamu wanda ya kware a sana’ar kuma shafe kimanin shekaru 15 yana gudanar da ita.
Matashi dan kimanin shekara 27, yana zaune ne a unguwar Shatsari a yankin karamar Hukumar Dala cikin birnin Kano, ya bayyana wa Aminiya cewa bai taba jin kunya ko yi wa kansa a kaskanci ba saboda yana yin wannan sana’ar.
Saminu ya sami shaidar kammala karatun firamare, inda ya yi karatun a makarantar firamaren Jakara. Daga nan kuma bai ci gaba da karatu ba sai ya kama sana’ar gashin gurasa gadan-gadan.
Ya ce: “Ban san wata sana’a ba baya ga gashin gurasa, na koyi sana’ar gashin gurasa ne daga wajen mahaifiyarsa kasancewar ita ce sana’ar da na tashi na same ta tana yi. Tun ina karami takan sa ni ayyukan da suka shafi
sana’arta, a haka yau da gobe na koya. A da can da jarin mahaifiyata nake amfani. Amma da na girma sai na
fara yin tawa ta kaina, inda na sanya jarina nake yin gurasar. Sai dai har a lokacin da na fara tawa gurasar nakan taya mahaifiyata gudanar da ta ta kafin daga bisani ta zo ta daina yin sana’ar gaba daya sakamakon rashin lafiyar da ya kwantar da ita,” inji shi.
Ya kara da cewa ba ya jin wani abu na daban domin yana gudanar da wannan sana’ar: “Na rigaya na saba da wannan sana’ar tun ina
karami ni ba na kallonta a matsayin sana’ar mata, ina yin ta ne da zuciya daya, kamar yadda kowane mutum yake gudanar da sana’arsa. A kullum nakan gasa gurasa kimanin buhun fulawa daya da rabi. Idan na tashi tun da asuba zan kwaba fulawa. Idan lokacin gasawa ya yi kuma sai na sa wutan a tanderu na fara gashi. Anan ne kuma mutane za su rika shigowa suna saye. A haka zan kai har rana ina gasawa ina kuma sayarwa. Wasu sukan kawo kudinsu tun dare domin a ajiye musu wace aka fara gasawa,” inji shi.
Game da fa’idar da ya samu albarkacin wannan sana’ar, ya bayyana cewa ya samu nasara sosai dalilin wanann sana’a,
inda ya ce a yanzu haka ya fara gina gidan kansa bayan aure da yake shirin yi. Daga karshe ya yi kira ga gwamnati da ta tallafa musu kamar yadda take tallafawa wasu masu sauran sana’o’i.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya