Na goyi bayan a sake fasalin kasar nan – Dokta  Balarabe Kakale

Kwamishinan Kasafin kudi da Ci Gaban Al’umma na Jihar Sakkwato Dokta Balarabe Shehu Kakale ya zanta da Aminiya kan takararda ya yi da kuma dokar asusun kiwon lafiya da kirkiro shi da kuma alfanunsa ga jama’a da sauransu: Mene ne dalilin da ka nemi takarar dan Majalisar Taraya a Mazabar Bodinga da Dange Shuni da […]

Na goyi bayan a sake fasalin kasar nan – Dokta  Balarabe Kakale

Kwamishinan Kasafin kudi da Ci Gaban Al’umma na Jihar Sakkwato Dokta Balarabe Shehu Kakale ya zanta da Aminiya kan takararda ya yi da kuma dokar asusun kiwon lafiya da kirkiro shi da kuma alfanunsa ga jama’a da sauransu:

Mene ne dalilin da ka nemi takarar dan Majalisar Taraya a Mazabar Bodinga da Dange Shuni da Tureta?

Na gode Allah. Dalilin da ya sanya na shiga siyasa har na shiga takara shi ne zimmar ba da tawa gudunmawa da amsa kiran da al’umma suka yi min. In jama’a suka ce ka ba da taka gudunmawa bai kamata ka ki ba, musamman yankinmu da ke da kishirwar wakilci a fannin bunkasa kasauwanci da abubuwan more rayuwa da noma da ilimi da kiwon lafiya a shekara 12 da ake wakiltarmu. A ganina in da a ce na samu dama zan yi tsaye wajen kwato hakkin yankinmu da kasarmu baki daya. Laifinmu ne da muke barin bara-gurbi suna tafiya Majalisar Wakilai don dan majalisa ba yankinsa ko jiharsa kadai yake wakilta ba kasa ce gaba daya, yake wakilta. Maganar da za ta taimaki mata da matasa da manoma da ’yan kasuwa ita zan fi bai wa karfi, ba za mu bar abin da yake hakkinmu ya tafi ba.  Kuma akwai bukatar gyaran fuska na karfin iko da aka bai wa Shugaban Kasa ya yi yawa, a koma tsarin Firayi Minsta zai yi maganin bara-gurbin wakillan da ake turawa da suka zama cima-zaune da dumama kujera. Don a cikinsu za a rika daukar ministoci da sauran manyan mukaman gwamnati ka go ba mai yarda a tura wanda bai cancanta ba, balle ya tafi ba ruwansa da zaman majalisa. Na yarda a canja fasalin kasar nan, rashin canja fasalin Najeriya yana cikin matsalolinmu a kasar nan. Domin wadanda ke yin aiki a Abuja ba su san matsalar jihohinmu ba, aiki ya yi wa Shugaban Kasa yawa a gyara fasalin, kowane yanki ya yi mai fitar da shi, ba dalilin da zai sanya sai an dauki saniya mai rai an tafi da ita Legas daga Sakkwato. A samar mata da daraja a rika gyara naman a nan sai ka ga an samar wa matasa aiki. Ya kamata a sakar wa gwamnoni mara a tsarin samar da wutar lantarki su yi hulda da wasu kasashe su samu wutar lantarki mallakinsu da harkar albarkatun ruwa da sauransu, nauyi ya yi wa gwamnatin tsakiya yawa.

Duk lokacin da dan siyasa ya fito neman kujera za ka ji yana fadin zai kawo ci gaba bayan ya samu nasara ba abin da zai kawo. Kai da me za ka bambanta da sauran in da ka samu nasara?

To ba zan yi wa kaina alkalanci ba, mutane sun san abin da nake fadi ko zan iya, abin da zan fadi nan a hulda ta da jama’a da sanin tarihina da ilimin da nake da shi, na tabbata ina da rawar da zan taka ta neman hakkinmu daidai da kundin majalisa. Don wakilci ba abu ne da za ka zo ka shimfida hanyoyi ba, aikin Majalisar Zartarwa ce, aikin Majalisar Dokoki shimfida tsari a gudanarwar gwamnati da bibiyar ayyukan gwamnati da suka shafi al’ummarka. Tarnakin da Nijeriya ke fama da shi ya ta’allaka ne ga dokoki da tsarin da ake ciki wasunsu sun tsufa ba su tafiya da zamani. Tabbas in da na tafi majalisa sai na kalubalanci duk wata doka da ta zama karfen-kafa ga ci gaban al’ummarmu. Misali harkar tsaro da ta tabarbare babu dalilin da zai hana a samar da dokar kafa ’yan sandan jihohi. Na yi imani tsaro ba zai inganta yadda ake so ba, matukar  kashi 100 na kula da ’yan sanda na hannun  Gwamnatin Tarayya. Najeriya na bukatar fiye da ’yan sanda  miliyan daya amma yanzu ba su wuce dubu 400 ba, akwai  gibi na kusan miliyan guda. Tsarin mulki da ya ce Gwamnatin Tarayya ke da alhakin tsaro yana da gyara don ga shi yanzu karara an kasa. Tsari na lafiya da ilimi a Najeriya gaba daya suna bukatar garambawul. Irin wadannan abubuwa ne za mu yi. Abu ne na fatar baki za ka kawo a yi muhawara a ba shi kula har ya zama doka. Don ka san abin ba na wasa ba ne, a nan Sakkwato mun ba Mai girma Gwamna shawara kan maganin mura wanda yake dauke da kodin. A duk kasar nan mu muka fara jerin gwano na neman Gwamnatin Tarayya ta hana shigowa da shi. Muka yi kasidu da tarurruka, muka hada kai da sashen soja aka rufe wurin sayar da kwaya a Kasuwar Sojoji ta Mami. Bayan rubuce-rubucen sanar da jama’a wannan maganin guba ne ga al’ummarmu da taro a Kano da Lagas a karshe gwamanti ta ji kiran Sakkwatawa, duk da har yanzu akwai sauran aiki.

Abubuwan da kake ganin sun kamata a yi wa gyaran fuska akwai sha’anin lafiya. A matsayinka na kwararren likita yaya kake kallon Inshorar Lafiya na Kasa da badakalar da ake zargin ana tafkawa a ciki?

Farfesa Yusuf ya zo da niyyar yin gyara amma an ki barinsa ya aiwatar da abin da ya dace, aka sanya masa tarnaki aka lalata abin har aka dakatar da shi. A haka sai Gwamnatin Tambuwal ta fito da asusun wakafi  na lafiya, abin da ake so a Sakkwato a samar da baitul mali na kula da marasa lafiya. Don rashin lafiya ba ya ba ka lokaci kwatsam yake zuwa musamman manyan rashin lafiya da ke sanya a sayar da gida ko gona ko jari ya kare. Ire-iren ciwon kamar su koda da daji  da  ciwon laka da hawan jini mai tasanani, a kididigarmu a Jihar Sakkwato baki daya masu ciwon ba su kai dubu 10 ba. Wannan tsari zai sa gwamnati da al’umma su dauke musu wahalar magani. A wani kiyasi namu a jiha  marasa lafiya ba za su wuce dubu 150 ba. A cikin mutum miliyan biyar da muke da su, akalla in aka samu mutum miliyan daya na amfani da kudinsu a hada da na gwamnati marasa lafiya zai samu gata. Mutum zai zo da katinsa ne kawai asibiti a ba shi magani tun daga kan cutar maleriya har zuwa dashen koda ba tare da ya biya ko kwabo ba. Amma kafin haka sai mutum ya rika yin zubi a wannan asusu na gata da gwamnati ta samar. Wannan shirin mun kwaikwayi Gwamnatin Tarayya ce muka yi wa namu gyaran fuska ya dace da abin da Musulunci ya amince da shi, don kawar da aringizo da gibi, muka kauce wa maganar inshora wadda take haramun ce a Musulunci don ta ci karo da shari’a.

Mai lafiya ya taimaki marar lafiya shi ne amfanin asusun bayan albarkar taro da kara inganta tattalin arziki a jihar. Wannan shirin za a kaddamar da shi kuma za a ci amfaninsa.