Na goyi bayan Sarki Muhammadu Sanusi II kan cire tallafin fetur
Tun da aka samu canjin shugabanci a Najeriya, na kudurta a raina cewar, lokaci ya yi da ya kamata duk wani da ke da wata shawara ko wani hangen nesa da zai kawo ci gaban wannan kyakkyawan shugabanci, to lallai kada ya yi kasa a gwiwa wajen fito da shi a fili, domin ta haka […]
Tun da aka samu canjin shugabanci a Najeriya, na kudurta a raina cewar, lokaci ya yi da ya kamata duk wani da ke da wata shawara ko wani hangen nesa da zai kawo ci gaban wannan kyakkyawan shugabanci, to lallai kada ya yi kasa a gwiwa wajen fito da shi a fili, domin ta haka ne kawai za mu tabbatar da cewa, fadi tashin da muka yi domin ganin wannan canjin ya samu bai tafi a banza ba. A kan wannan dalili ne na zare alkalamina a wannan don goyon bayana ga Sarki Muhammadu Sanusi na biyu a cikin kalamansa da ya yi a wani taro da aka gudanar a Lagos, inda ya yi kira ga gwamnatin mai girma Shaugaba Buhari da cewar, ta cire tallafin manfetur.
Tallafin manfetur, wasu makudan kudi ne da gwamnati ke warewa a duk shekara domin tallafa wa harkar manfetur, ta yadda za a rika sayar da shi kasa ga yadda farashinsa ya kamata ya kasance. Ke nan a lokacin da aka ce farashin manfetur ya kai Naira 120 a kasuwar duniya, ita kuma Najeriya sai take sayar da shi akan Naira 65, ke nan gwamnatin tarayya za ta rika sanya tallafi na Naira 55 ga kowace lita daya.
To sai ka duba ka gani, wadannan kudin dai kudin ’yan Najeriya ne ga baki dayansu, amma su wane ne ke amfanuwa da cin gajiyar wannan tsari na tallafin mai? ’Yan Najeriya ne dukansu? Ko alama, wasu daidaikun mutane ne daga cikin al’ummar da ke rayuwa a birane, daidai lokacin da mutanen kauye ke rayuwa ba tare da ruwan shan kirki ba ko wutar lantarki.
Janye zancen mutanen kauye wadanda su ne mafi yawan al’umma, hatta a cikin birni ’yan kadan ne za su amfanu. Yanzu idan talaka mai sana’ar kabu-kabu (acaba) ya zo gidan mai, iyakarsa ya sanya lita biyar, daidai lokacin da wani Alhaji da ke cikin wata makekiyar mota zai zo ya ce a sanya masa lita 50 a motarsa, lita 60 a jarkoki domin ya sanya a janaritonsa na gida, lita dari biyu domin a sanya a janariton kamfani… Anya babu kwaruwa a cikin wannan sabgar?
Yanzu mu dauko misali daga shekara ta 2013, wadda aka bayyana cewa, tallafin manfetur ya lashe tsabar kudi har Naira biliyan 971, wanda hakan ke nufin, idan aka raba wadannan kudin zuwa watanni 12 da muke da su a shekara, tallafin mai ya lashe zunzurutun kudi har naira biliyan 80.9 a kowanne wata. Kuma abin haushin shi ne, wadanda suka amfana da wannan tallafin, ba za su wuce kashi talatin cikin al’ummar Najeriya ba (Idan sun kai), domin masu kudi ne wadanda ke juya kasar a bisa tafin hannuwansu, wadanda kuma har ila yau, su ne suke da gidajen manfeturin da ke lashe kudin talakawan Najeriya da sunan tallafi.
Kamar yadda Malam Abubakar Binji (BSO mamba a Jihar Sakkwato) ya taba bayyanawa, da za mu dauki kananan hukumomi guda 774 da muke da su a Najeriya, za mu ga cewa idan aka raba musu wadannan kudi maimakon saka su a tallafin man fetur, ke nan a kowanne wata, kowacce karamar hukuma za ta samu Naira miliyan 104 kari a kan abin da take samu. Don Allah idan kowacce karamar hukuma aka damka mata wadannan kudi a hannunta kuma aka tabbatar da cewar ta yi aikin da ya rataya a kanta, shin talakawa ba za su ji dama ba?
Ya za ka ji idan aka ce yau karamar hukumarka ta sawo magani na miliyan dari wadanda za a bai wa marasa lafiya kyauta? Ko kuma an saye abinci na Naira miliyan 100 da za a raba a karamar hukumarka? Ko kuma ace an yi amfani da Naira miliyan 100 wajen samar wa mutanen karamar hukumarka aikin yi? Abin da nake son cewa shi ne, duk inda aka yi aikin naira miliyan dari na ci gaban al’umma, to lalle wannan aikin ba zai boyu ba. Amma ga shi an dade ana ta batar da kudin al’umma da sunan tallafin manfetur. Masu kudi suna kara kudi, talakawa na kara shiga halin kaka nika yi.
Ko shakka babu, idan aka daina saka wadannan makudan kudin a tallafin manfetur, kananan hukumomin da ake kiyasta suna karbar Naira miliyan 100 zuwa Naira miliyan 150 a matsayin kudinsu na wata-wata, za su samu karin kamar kashi 40 bisa ga abin da suke karba. Ashe ke nan ba karamin aikin ci gaba ne za su gudanar da kudin ba, musamman zamowarsu a karkashin shugabancin adilin shugaba mai dattako, wanda bai taba kwabon kowa balle ya bari ka taba, wato shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Hanya mafi sauki da talaka zai iya cin gajiyar dimukuradiya, ita ce ta amfani da karamar hukuma. Yanzu idan karamar hukumar da ta samu karin Naira miliyan 104 na da gundumomi guda 10 a cikinta, kowace gunduma za ta iya samun Naira miliyan 10 da dubu 500 da za ta yi wa al’ummarta aikin ci gaba. Ita gundumar idan ta ga dama, ta biya wa al’ummarta tallafin manfetur, idan kuma ta ga dama ta saya musu magani, ko ta yi musu hanyoyi, mai daki dai, shi ne ya san inda dakinsa ke yi masa ruwa. Amma dai shi ne mafifici akan, a rika daukar dukiyar daukacin jama’a a na mika wa wasu mutane ’yan kadan suna lashewa.
Damadai babban abin da mu mutanen Najeriya ke tsoro shi ne, mummunan shugabanci, kuma Allah cikin ikonsa Ya raba mu da shi. Shugabanmu na yanzu, shugaba ne da ke iya yin tsaye tsayin daka domin ya tabbatar an bai wa al’umma hakkokinsu. Don haka lallai a cire tallafin manfetur, a sanya tallafin wahalolin da dukan al’umma ke fama da su. Allah Ya taimaki Shugaba Muhammadu Buhari tare da Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II, tare da mu baki daya.
Za a iya tuntubar Babi, a kan: 08033186727 Nasir Abbas [email protected].