Na goyi bayan wasikar Obasanjo zuwa ga Buhari – Bafarawa

“Rikicin makiyaya da manoma da ake fama da shi a kasar nan ‘yan siyasa na taka rawa cikinsa kuma ya koma siyasa, amma da wannan gwamnati ta saurari shawarar da ake ba ta tun farko, da haka bai faru ba, makiyayi da aka sani da sanda me ya hada shi da bindiga? Gwamnati ta sani […]

Na goyi bayan wasikar Obasanjo zuwa ga Buhari – Bafarawa

“Rikicin makiyaya da manoma da ake fama da shi a kasar nan ‘yan siyasa na taka rawa cikinsa kuma ya koma siyasa, amma da wannan gwamnati ta saurari shawarar da ake ba ta tun farko, da haka bai faru ba, makiyayi da aka sani da sanda me ya hada shi da bindiga? Gwamnati ta sani akwai bambancin jam’iyyu, amma kasa ta kowa ce.”

Wadannan kalamai sun fito ne daga tsohon Gwamnan Sakkwato, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, a wurin taron masu ruwa da tsaki na PDP a Jihar Sakkwato da aka gudanar a ranar Litinin da ya gabata. Haka zalika kuma Bafarawa ya goyi bayan takardar da Obasanjo ya rubuta wa Shugaba Buhari, yana mai cewa shi ya dauki Obasanjo shugabansa, kuma yana da damar da zai yi magana ga abin da ya ga bai dace ba, kuma Shugaba Buhari ya san duk abin da aka fada a takardar gaskiya ce, mutane su yi nazari kan abin da ya fada kafin su ce wani abu. Amma idan maganar martani ne, to Buhari ne kawai ya dace ya ba da amsa.

Ya dawo Jihar Sokoto, ya bayyana cewa Gwamnatin Tambuwal musiba da matsaloli ta gada ga gwamnatin Wamakko da ya zo kan mulki bai fadi abin da ya gada ba, yana ganin girman wanda ya gada baya son ya tona masa asiri “mu muna ganin laifin Tambuwal kamata ya yi ya fada mana abin da ya tarar baki ko fari ne tun da gwamnati ta jama’a ce, amma ya yi shiru mu Sakkwatawa fa muna jiran sai ya fada mana abin da aka bar ma shi ba abu ne na boyo ba, dole a fada mana ba laifi ba ne tun da gado ne ciyo ko lafiya ya tarar.’in ji Bafarawa.

Tun da farko Sakataren PDP na jihar Sakkwato ya sanar da cewa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun nemi Bafarawa ya tsaya takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa, kuma jam’iyarsu a hade take wuri daya. APC ne ke kokarin shiga tsakaninsu kuma ba za su samu nasara ba.