Na ji dadin raga-raga da muka yi wa United —Klopp
Dama shi wasa ya gaji haka.
Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp, ya bayyana farin ciki game da nasarar da kungiyarsa ta samu na lallasa abokiyar hamayyarsu, Manchester United da ci 7 da nema da suka yi a gasar Firimiyar Ingila.
Ya bayyana nasarar a matsayin abin da wasa ya gada, ganin irin namijin kokarin da suka nuna.
- Kotu ta bayar da belin Alhassan Doguwa a kan N500m
- Dauda Dare ne dan takarar gwamnan PDP a Zamfara —Kotun Koli
’Yan wasan Liverpool irin su Cody Gakpo, Darwin Nunez da kuma Mohamed Salah kowannen su ya zura kwallaye biyu wajen casa United 7 da nema a filin wasa na Anfield.
Nasarar jefa kwallaye biyu da Salah ya yi a wasan, ta bashi damar kafa tarihin zama dan wasan Liverpool da ya fi yawan jefa kwallo a gasar Firimiyar Ingila da kwallaye 129 da ya jefa a wasanni dari biyu da 5.
Haka nan, rashin nasarar ce ta biyu da United ta yi a cikin wasanni 23 da ta buga a dukkanin gasanni, wacce kuma ta kawo karshen fatan ta na lashe gasar a karon farko cikin shekaru 10 ganin akwai tazarar maki 14 tsakaninta da Arsenal da ke jagorantar teburin gasar.