…Na kadu da na ji da sa hannun Bisallah a kisansa – Ajoke Muhammed

Gobe Asabar ne za a cika shekara 40 da kashe tshohon shugaban kasa Janar Murtala Muhammad, Aminiya ta zanta da Samanja Michael Otuwe dattijo mai shelkara 69 kuma odilan marigayi tsohon Shugaban Najeriya Janar Murtala Ramat Muhammed shekaru 40 da suka wuce, ya fadi dalilin haduwarsu da Murtala dakuma  yadda aka kashe shi: Aminiya: Mene […]

…Na kadu da na ji da sa hannun Bisallah a kisansa – Ajoke Muhammed
…Na kadu da na ji da sa hannun Bisallah a kisansa – Ajoke Muhammed

Gobe Asabar ne za a cika shekara 40 da kashe tshohon shugaban kasa Janar Murtala Muhammad, Aminiya ta zanta da Samanja Michael Otuwe dattijo mai shelkara 69 kuma odilan marigayi tsohon Shugaban Najeriya Janar Murtala Ramat Muhammed shekaru 40 da suka wuce, ya fadi dalilin haduwarsu da Murtala dakuma  yadda aka kashe shi:

Aminiya: Mene ne tarihinka?
Odila: Sunana Samanja Micheal Otuwe. Ni dan kabialr Igala ne daga Jihar Kogi. karamar hukumarmu itace Olamaboro wacce aka ciro daga Ankpa.
Aminiya:Me ya sa ka yi sha’awar shiga aikin soja?
 Odila: Don ina sha’awar aikin. Bayan na kamalla karatun firamare da na Sakandare na Ankpa Model sai na tafi Ikko inda na shiga aikin soja. Na shiga aikin soja ina da shekara goma sha takwas, a ranar 11 ga watan 9 na shekarar 1967 a Ikeja ta jihar Legas, kuma a nan aka horar da mu, domin lokacin akwai alamun fara yakin basasa. Bayan mun kammala samun horo sai aka tura ni bangaren “siginal” watau masu aikewa da sakonnin soja. Lokacin janar Murtala yana Sufeto na Siginan Sojan Najeriya.
Aminiya: Ya aka yi Janar Murtala ya dauke ka a matsayin odilansa. Ko wani ne ya neman maka alfarma?
Odila: Lokacin Murtala yana Kanar, yana duba “Master fareti” irin na soja da ake yi kullum da safe, sai ya lura ya dauke ni a matsayin odalinsa. Lokacin ina da igiya daya.
Aminiya: Mene ne dalilin da ya sa ya dauke ka daga cikinku da yawa?
Odila: Ya ce saboda ya lura ina da tsabta. Babban dalilin ke nan kuma ka san da kuruciya da son aiki irin na sojan da.
Aminiya: Shekara nawa ka yi a matsayin dogarin Janar Murtala.
Odila: Na shekara 11 ina aiki da shi. Yana da yara uku lokacin, da Aisha da Zakari da kuma Fatima.
Aminiya: Mene ne halin Janar Muratal da ka sani wanda ba kowa ya sani ba?
Odila: dan baiwa ne , Soja ne da soja ke son yin koyi da shi. Misali, duk wanda ya yi laifi to sai ya ba shi ladan laifin da ya yi. Ba ya manta an yi laifi, sai kuma ya ba da ladan yin haka. Kuma haka aikin soja ya gada, idan kayi mai kyau kanka, idan ka ya mara kyau kanka. “Laifi da dadi, hukunci da zafi.”
Aminiya: Me ka ce wa matarka dangane da aiki-ba-kama-hannu-yaro bayan da Murtala ya hau mulki?
Odila: (Dariya) Aiki da Janar Murtala a matsayin soja kadai ya isa mutum ya bada labara, balle an hada da shugabancin kasa baki daya. Yarana suna mantawa da ni, don ina barin gida sai asuba in dawo ko da tsakar dare lokacin duk suna barci. Matata ai a bariki take ta san aikin soja. Don lokacin muna barikin Apapa. Sai dai a ranakun lahadi ko asabar ina zuwa gida wurinsa ko da ba za mu je ko’ina ba.
Aminiya: Ya kake zuwa gida bayan an tashi aiki?
Odila: Ina da direbana, watau ina da mota mai lambar CbU na manyan ma’aikatan gwamnati. Shi yake kai ni gida kuma ya dauko ni.
Aminiya: Da gaske ne yana shigar burtu ya tafi yawo a Legas?
 Odila: kwarai kuwa, don yana yin safiyo don sanin farashin kaya. Ya taba sanya kaya ‘yan kwallo ya sa bakin madubi ya hau doki mu kuma muna binsa a baya da dabara, ya daure dokin a gidan mai, sannan ya shiga kasuwar Sangros don jin ko farashin kaya ya tashi. Kafin ya fito da dokar kayyade farashin kayayyaki “Price Control,” ya shiga Ajegunle da kuma Agege, ADC yana rubuta farashin, amma ya yi bad-da-bami babu wanda ya gane shi. Har wata mata ta ce idan ba saye zai yi ba ya wuce, wani na bayansa zai sayi kaya.  
Aminiya: Me ya faru ranar 13 ga watan Farairu ranar da aka kashe Janar Murtala?
Odila: (Kuka na kusan minta uku) Janar Murtala ya hau mulki ranar 29 ga watan Yulin 1975, sannan aka yi masa kisan gilla ranar Juma’a 13 ga watan Fabrairun 1976. Janar Murtala mutum ne mai karamci, don ya ki yarda da a yi watsi da kayan Janar Gowon daga gidan Shugaban kasa da ke Barikin Dodan, shi ya sa ya ce a kwashe kayan a tsanaki, sannan a yi wa gidan kwaskwarima kafin ya tare. Haka ta sa yake tasowa daga gidansa da ke Ikoyi. Wanna ya sa ‘yan ta’addan suka samu damar kai masa hari, domin kuma ya ce kowane dan kasa yana da damar yin amfani da titi, sannan bai son masu Babura su yi masa rakiya ko sojoji.
Lokacin da muka fito zuwa ofis da safe, mun kawo Sakatariyar gwamnatin tarayya da ke Ikoyi, lokacin an yi wa wurin kwaskwarima don an zagaye shi da kwanon rufi. Mun fito daga gidansa na Ikoyi zuwa ofis da ke barikin Dodan da mota Marsandi mai Tutar Najeriya a hagu da kuma tutar dakaru a dama, a daidai mahadar Alagbgon sai mai ba da hannu ya daga hannu don bai ga tutar ba, domin akwai motaci biyar ko shida a gabanmu.  Ka san ba mu da jiniya, don Murtala bai son matsa wa jama’a. Kutsam sai wadansu mutane suka bullo daga hannun hagu suna sanye da babbar-riga, da suka dage rigar sai suka ciro bindiga AK-47 suka bude mana wuta. Sai wani soja ya fito daga titin Gulf ya harbi direbanmu a kai, inda nan take ya mutu(ya yi kuka da hawaye). Ganin haka sai na kwnta a kan jakar Murtala mai dauke da kayansa na gida wacce zai sanya ya tafi sallar juma’a ba sai ya koma gida ba. Shi ma Janar Murtala da ADC suka yi kwanto irin na soja lokacin da ake harbe-harben, suka yi lamo kamar sun mutu.Sabo da kwanciyar da na yi a jikin direban  jini ya zuba mini, sai suka dauka duk sun kashe mu. Sai suka ruga zuwa gidan rediyo don su sanar sun kwace mulki. Bayan da muka ji shiru sai ADC ya bude kofar motar, ashe ba su yi nisa ba, sai wani soja mai mukamin Manjo ya waigo, sai  ya ce ku dawo ba su mutu ba. Haka ya sa suka dawo suka zazzage dukkan  harsasansu akan mu. Ni an harbe ni a kafada da cinya.
Daga nan sai muka samu tallafin sojojin da ba sa cikin ‘yan