…Na kadu da na ji da sa hannun Bisallah a kisansa – Ajoke Muhammed(1)
A ranar Juma’a 13 ga watan Fabarairu na shekarar 1976 ne aka yi wa tsohon shugaban kasa Janar Murtala Ramat Muhammad kisan gilla, abin da ya girgiza daukacin al’ummar kasar nan a wancan lokacin, kasancewarsa shugaba na kowa, mai himma da kwazo da son bin gaskiya. Janar Murtala Muhammad shi ne shugaban Najeriya na hudu […]

A ranar Juma’a 13 ga watan Fabarairu na shekarar 1976 ne aka yi wa tsohon shugaban kasa Janar Murtala Ramat Muhammad kisan gilla, abin da ya girgiza daukacin al’ummar kasar nan a wancan lokacin, kasancewarsa shugaba na kowa, mai himma da kwazo da son bin gaskiya. Janar Murtala Muhammad shi ne shugaban Najeriya na hudu kuma ya yi mulki ne yana dan shekara 37. Mutum ne mai saukin kai a lokacin da yake mulki, domin ba ya ketare talakawansa, idan ya fito aiki a motarsa yana yin hakuri ya shiga cikin jama’a kamar kowa. A gobe Asabar ne Janar Murtala Muhammed ya cika shekara 40 da rasuwa.
Uwargidar marigayi Janar Murtala Muhammad, Hajiya Ajoke Muhammad, ta shaida wa Aminiya cewa, kamar yadda Janar Murtala yake jajurtacce a wajen aiki haka yake ko a gidansa, ta ce kyawawan halayansa da aka san shi da su a bakin aiki, kamar gaskiya da rikon amana da yaki da rashin da’a, da sauransu, irin wadannan hallayen su ne yake da su ko a cikin gidansa, domin tsayayyen mutum ne, jajurtacce mai yawan kwazo.
Hajiya Ajoke wacce bayarabiya ce da take da ‘yar dangantaka da Fulani, ta ce ta hadu ne da mijin nata ne a sa’ilin da take karatu a makarantar koyon aikin likitan hakori da ke Legas a shekarar 1961, a lokacin ‘yan uwansa ne suka kulla dangartakarta da shi, tunda ga sannan suka fara soyayya, bayan da suka sake haduwa a Kaduna sai ya nemi su yi aure, aka kuma daura musu aure a Kaduna a shekarar 1963 bayan ta gama karatunta. A wannan shekarar ce ya zama kyaftin a rundunar sojin Najeriya.
Hajiya Ajoke ta ci gaba da cewa, a lokacin da Janar Murtala ya zama shugaban kasa ta kasance cikin zullumi da taraddadi, don a wasu lokutan ma takan kasa barci. A sa’ilin da aka yi masa kisan gilla kuwa ba abin da ta iya yi sai addu’a, domin tana sane da rashin tabbas na rayuwar soji . Bayan mutuwarsane ta bar aikinta na likitan hakori domin ta samu damar bai wa ‘ya’yansu cikakkiyar kulawa, wadanda a wannan lokacin ‘yan kanana ne kwarai. “ Na yi ta sharara kuka da labarin mutuwarsa ya riske ni, na ji takaici da bakin ciki .’’
‘’Na kadu kwarai da na ji labarin cewa Bisalla na da hannu a kisan gillar da aka yi wa maigidana saboda kusancin da ke tsakaninsu.Domin abokinsa ne tun suna yara, tare suka shiga makaranta, ajinsu guda kuma tare suka shiga soja.’’
A halin yanzu uwargidan Janar Murtala Muhammad ta rungumi harkar shuka tsirrai da furanni ne da ke barazanar bacewa daga doron kasa, ta yi fice a wannan harkar a ciki da wajen kasar nan, domin hakan ne yasa lambunta da ke layin Cooperatibe a Ikoyi jihar Legas ya shahara, da kuma lambun tunawa da Janar Murtala Muhammad wanda yake a babbar hanyar Lekki zuwa Epe a Legas, duk lambunan na samun halartar mutane daga ciki da wajen k,asar nan wadanda ke zuwa domin yin nazari ko shakatawa.
Allah Ya albarkaci aurensu da ‘ya’ya shida, wadanda suka hada da Aishat Ayebode wacce ta karanci aikin lawya a jami’ar Kings College a Landan, ta kuma yi karatun digiri na biyu a fannin kasuwanci, kuma a yanzu babbar sakatariya ce a Gidauniyar Murtala Muhammad. Sai Fatima Murtala Muhammed, wacce akanta ce kuma masaniya ce a fannin tsirrai, sai Zakari Murtala Muhammd wanda ya rasa ransa a wani hargitsin harbi da bindiga, lamarin da har ya zuwa yanzu babu cikakkiyar masaniya a kansa. Sai da namijin da shi ne daya tilo da ya rage ga Janar Murtala Muhammad, wato Riskuwa Abba, wanda ya taba zama mai bai wa tsohon shugaban kasa Olusagun Obasanjo shawara a fannin sayar da kadarorin gwamnati ( pribitisation), sai Zalihatu Murtala Muhammad, wacce ke aiki a Legas a wani kamfanin zayyanar gidaje.
A lokacin da Janar Murtala Muhammad ya rasu ya bar mahaifiyarsa Hajiya Ramatu da kawunsa Alhaji Inuwa wada ( Magajin Garin Kano) da matarsa da ‘yayansa da ‘yan uwasa da dama.