‘Na kafa gidauniya ne don tallafa wa marasa galihu’
Idan kin yi ritaya wadanne abubuwa za ki ci gaba da yi a rayuwa?To babu wanda ya san me zai faru gobe sai Allah Madaukakin Sarki. Amma babban abin da nake bukata shi ne in na yi ritaya daga aikin gwamnati zan shiga harkokin kasuwanci ne domin akwai albarka a kasuwanci da noma da kiwo. […]
Idan kin yi ritaya wadanne abubuwa za ki ci gaba da yi a rayuwa?
To babu wanda ya san me zai faru gobe sai Allah Madaukakin Sarki. Amma babban abin da nake bukata shi ne in na yi ritaya daga aikin gwamnati zan shiga harkokin kasuwanci ne domin akwai albarka a kasuwanci da noma da kiwo. Watannin baya na gwada noman kifi kuma na samu alheri sosai.
Wadanne abubuwa ne ke haifar da yawan zawarawa a shiyyar Arewa?
Rashin hakuri da karya da yaudara da talauci na daga cikin abubuwan da suke jawo matsaloli a tsakanin ma’aurata. Sannan shekara shida da aka yi ana fama da matsalar tsaro a yankin Arewa ya taimaka wajen karuwar zawarawa a tsakanin al’umma. Don haka nake ba da shawara ga masu hali su tallafa wa wadannan mata da suke cikin mawuyacin hali. Yanzu haka akwai gidauniyar da na kafa domin tallafa wa marayu da marasa galihu kuma ina amfani da kudin aljihuna ne wajen biya musu kudin makaranta.
Sannan ina ba su abinci, ina dinka musu kayan makaranta daidai karfina. Akwai marayu goma da nake kula da dawainiyarsu a halin yanzu.
Mene ne sakonki ga matan aure?
Sakona ga matan aure shi ne kowa ta yi hakuri da mijinta, domin ana cikin mawuyacin hali. Sannan mata su kula da abubuwa irin su tsabtar jiki da na muhalli. Kada a bar gida da tarin shara sannan yara a rika yi musu wanka duk lokacin da za su je makaranta.
Ina kira ga mazan da suke auren mata barkatai, babu abinci mai dadi wasu lokuta ma sukan fifita wani sashe a kan sashe. Don Allah duk wanda ya san ba zai yi adalci a tsakanin matansa ba, to ya zauna da mace daya shi ne alheri a wajensa domin Allah Ya hana zalunci. Wallahi duk mijin da ke cutar matarsa to tabbas Allah Zai toshe kofofin samunsa.
Me kike so Shugaban kasa Buhari ya yi wa matan Arewa?
Babban sakona ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne matan Arewa maso Gabas suna bukatar tallafin gwamnatinsa da jari da kayan sana’a domin idan mace tana da Naira dubu 10 kafin wani lokaci kudin za su koma Naira dubu 15. Muna fatan Allah Ya ba shi damar cika alkawuran da ya dauka a lokacin kamfen. Abin da ya burge ni da Shugaba Buhari shi ne yadda ya nada mata shida a matsayin ministoci. Allah Ya ba su damar yin adalci a lokacin da suke gudanar da ayyukansu.
A karshe menene sakonki?
Sakona shi ne ina yaba wa jaridar Aminiya da ta ba ni wannan dama har aka yi hira da ni. Kuma ina fata za ku ci gaba da ba mata dama domin yin tsokaci game da matsalolin da suke fuskanta a rayuwa. Na dauki tsawon lokaci ina karanta wannan jarida kuma na amfana da dimbin ilimin da ke cikinta. Allah Ya kara mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasarmu Najeriya. Duk wadanda ke shirya makirci ga kasar nan Allah Ya tona asirinsu a ko’ina suke.