Na kafa gidauniya ne don tallafa wa marasa galihu– Fatima danjuma

Aminiya: Farko za mu so ki ba mu takaitaccen tarihin rayuwarki?Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukacin Sarki. Sunana Fatima Idris danjuma, Gimbiyar Mai Gundumar Yalwan Tudu da ke karamar Hukumar Bauchi.  An haife ni a garin Kaduna.  Na yi makarantar firamare da sakandare a garin Maiduguri, daga nan sai na zarce zuwa Makarantar Koyar […]

Na kafa gidauniya ne don tallafa wa marasa galihu– Fatima danjuma
Na kafa gidauniya ne don tallafa wa marasa galihu– Fatima danjuma

Aminiya: Farko za mu so ki ba mu takaitaccen tarihin rayuwarki?
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukacin Sarki. Sunana Fatima Idris danjuma, Gimbiyar Mai Gundumar Yalwan Tudu da ke karamar Hukumar Bauchi.  An haife ni a garin Kaduna.  Na yi makarantar firamare da sakandare a garin Maiduguri, daga nan sai na zarce zuwa Makarantar Koyar da Dabarun Yaki (National War College) da ke Birnin Tarayya, Abuja.
Daga nan sai na sake shiga Cibiyar Koyon Aikin Jarida da ke Abuja.  Bayan na kammala sai na fara aiki da wata jarida mai suna Eberyday Newspaper wadda ake bugawa a Abuja. Bayan na yi aiki na tsawon lokaci sai na koma Jihar Legas na ci gaba da aiki da jaridar Mail Newspaper.
Daga nan sai na samu aiki a gwamnatin Jihar Bauchi a shekara ta 2007 har yanzu.   Kuma ina ci gaba da neman ilimi daidai gwargwado domin babu wata al’umma da za ta samu ci gaba sai da ilimi. Yanzu haka ina aiki da Ma’aikatar Watsa Labarai ta jihar kuma ni ce Sakatariyar kungiyar Mata ’Yan jarida ta Ma’aikatar Watsa Labarai ta Jihar Bauchi.
Wadanne kalubale kika fuskanta a lokacin da kike karatu?
Babbar matsalar da na fuskanta a lokacin karatu ita ce ni ’yar talaka ce da kyar nake samun kudin biyan makaranta.  Akwai mata da dama da suke shiga makaranta amma saboda rashin kudi su gagara kammala karatu kuma idan mutum ya duba sosai zai fahimci cewa talauci ya taimaka sosai wajen hana mutane shiga makarantu.
A wace shekara kika yi aure?
Na yi aure ina da shekara 17. A shekarar 1988 ne mijina wanda yake tsohon soja ne ya halarci kasashe da dama domin ba da gudunmawarsa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.  A lokacin da aka yi min aure ina aji uku ne a makarantar sakandare.
’Ya’yanki nawa a halin yanzu?
Ina da ’ya’ya biyar, mata uku maza biyu kuma dukkansu suna makaranta. Fatana  Allah Ya ba mu abin da za mu ci gaba da biyan kudin makarantarsu. Kowa ya san cewa ilimi shi ne sanadarin da ke jawo ci gaba a kowace kasa a duniya.  daya daga cikin ’ya’yana soja ne wanda yanzu haka yana Jihar Borno inda ake fafatawa da ’yan Boko Haram.
Mene ne sakonki ga ’yan mata masu tasowa?
Abin da zan fada musu shi ne ya kamata su sauya tunaninsu domin yanzu duniya ta sauya da yawa daga cikin maza sun fi son auren mace wacce ta iya rubutu da karatu wato mai ilimi. Saboda haka ina ba da shawara ga mata masu tasowa bayan an yi aure babu laifi mace ta ci gaba da karatu, domin gemu ba ya hana ilimi. Bayan haka don Allah mata a yi hakuri domin yanzu ana fama da karancin kudi a tsakanin al’umma kada a matsa wa mazaje.
Wadanne matsaloli kike ganin wasu daga cikin matan Jihar Bauchi suke fuskanta?
Akwai dimbin matsaloli da matan jihar suke fuskanta domin kowa ya san cewa Jihar Bauchi tana daga cikin jihohin Arewa maso Gabas da suke fama da tarin ’yan gudun hijira wadansu daga cikin matan ba su da aikin yi don haka ina fata shugabanni za su bullo da wasu sababbin dabaru na tallafa wa matan jihar.  Talauci da rashin aikin yi ya yi tsamari a wannan shiyya ta Arewa domin an dauki tsawon lokaci muna fama da tashe-tashen hankula wadanda suka yi sanadiyar asarar dimbin rayukan al’umma, ka ga kuwa dole a samu dimbin zawarawa a wannan shiyya.
Bayan haka ina rokon sabuwar Ministar Harkokin Mata, Hajiya Jummai Alhassan ta fada wa Shugaban kasa cewa sama da kashi 85 cikin 100 na wadanda suka kada masa kuri’a a zaben da ya gabata mata ne, don haka muna fata Gwamnatin Tarayya a karkashin Shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta kyautata wa mata a wannan sabuwar gwamnati ta talakawa. Ni ba ’yar siyasa ba ce, amma ina ganin babu laifi daga lokaci zuwa lokaci mu rika ba da shawarwari masu amfani da za su kawo sauyi a tsakanin masu mulki.
Yanzu haka akwai wani bincike da aka gudanar a Bauchi, mata da dama ba su samu damar shiga makaranta ba, sakamakon yadda suke fama da talauci da rashin aikin yi, amma duk da haka muna ba da shawara ga mata kada mace ta zauna ba ta yin aikin komai domin yanzu sama da kashi 85 cikin 100 na maza ba sa kaunar zama da mace wadda ba ta da sana’a.
A yau duk inda mace ta kai da jiji da kai da rangwada matukar ba ta iya karatu da rubutu ba, to tabbas za ta samu koma baya a rayuwa.