Na kan samu N45,000 a duk wata – Mai yankan farce

Ya ce duk da yake yana shan wahala matuka wajen yawo a cikin birnin yana neman kwastomomi, amma abin da yake samu yana isarshi.

Na kan samu N45,000 a duk wata – Mai yankan farce

Wani mai sana’ar yankan farce, (Tsohuwar ajiya).

Wani matashi mai kimanin shekaru 19 dake sana’ar yankan farce a birnin Benin na jihar Edo, Ibrahim Kabiru, ya ce ya kan sami akalla N1,500 a kullum, jimlar N45,000 a kowanne wata.

Ibrahim, a cikin wata tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ce sana’ar na taimaka masa matuka wajen biyan bukatunsa na yau da kullum.

Ya ce ya yi kaura ne takanas tun daga jihar Sakkwato zuwa jihar ta Edo domin yin sana’ar.

A cewarsa, duk da yake yana shan wahala matuka wajen yawo a cikin birnin yana neman kwastomomi, amma abin da yake samu yana isarshi.

Ibrahim ya shaida wa NAN cewa a baya yana sana’ar noman masara ne amma karancin jari ya sa tilas ya nemi wata sana’ar.

Ya ce ya kan karbi N100 a kan kowanne yankan farce da kankara, yayin da idan yanka ne zalla ba kankara ya kan karbi N50.

Mai yankan farcen ya ce jarin da ake bukata domin fara sana’ar bai wuce N1,000 ba domin sayen almakasa, soso, ruwa da kuma sabulu.

Da aka tambaye shi ko yana da niyyar komawa harkar noman idan ya samu jari sai ya ce eh, inda ya ce noma a yanzu dole yana bukatar jari.

Ya ce kasancewar bai yi karatun boko ba, sana’ar yankan farcen kawai zai Yankan farce, Edo, Beniniya yi sai kuma ta noman.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos