Na kashe abokina na yi tsafin kuɗi da maƙogwaronsa — Boka
A cikin kwana uku na kammala aikin markaɗe maƙogwaronsa abokin nawa.
Rundunar ’yan sanda a Jihar Osun ta kama wani boka da zargin kashe abokinsa da ya yi tsafin kudi da sassan jikinsa.
Kakakin rundunar, SP Yemisi Opalola ce ta fadi haka a ranar Juma’a a wajen taron manema labarai a birnin Osogbo.
- Kwankwaso ya shawarci masu shirin zanga-zanga
- Kotu ta tura matashi gidan kaso saboda rubuta sunan Allah a jikin kare
Ta ce bokan mai suna Kehinde Ganiyu ya furta da bakinsa cewa shi ne ya kashe wani abokinsa dan Kasar Ghana mai suna Emmanuel Collins mai shekara 35 da yake zaune a Osogbo.
Ta ce lamarin ya auku ne da misalin karfe 9 na daren ranar 9 ga watan Yuli da muke ciki.
An kai rahoton mutuwar Collins a ofishin ’yan sanda na Oke-Odo a Osogbo, inda bincike ya kai ga kama Boka Kehinde Ganiyu, in ji kakakin ’yan sandan.
Bokan ya yi bayanin cewa “ni kaɗai na kai ziyara gidan Emmanuel Collins a lokacin ina riƙe da wuƙata mai kaifi.
“Na same shi a kwance yana barci a dalilin rashin lafiya da yake fama da ita.
“A nan take na yi masa yankan rago na cire makogwaronsa da wasu sassan jikinsa.
“A cikin kwana uku na kammala aikin markada makogwaron abokin nawa na garzaya cikin dajin Igbo-Imese a yankin Aiwosi da ke Unguwar Oba-Oke a birnin Osogbo.
“Na yi aikin gauraya sassan jikin da wata hoda da sabulu da na tafasa su cikin tukunyar yunɓu domin yin tsafin kuɗi da ake kira da sunan Osole.
Aminiya ta gano cewa asirin Bokan ya tonu ne tun kafin ya kammala aikin haɗa maganin tsafin samun kuɗi cikin dare ɗaya.
Kakakin ’yan sandan ta ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da wannan Boka gaban kotu domin ya fuskanci hukunci.