Na kashe maigidana don in samu kudin zuwa Dubai-Yaron mota
Wani yaron mota, mai suna Sani Sa’idu da ya kashe maigidansa a lokacin da suke tafiya tare a hanyar Fatakwal, inda ya bayyana cewa, ya kashe maigidan nasa ne saboda ya samu Naira dubu 150 na tafiya Dubai.’Yan sanda sun kama Sani Sa’idu dan shekaru 34 a duniya a karshen makon da ya gabata, kan […]
Wani yaron mota, mai suna Sani Sa’idu da ya kashe maigidansa a lokacin da suke tafiya tare a hanyar Fatakwal, inda ya bayyana cewa, ya kashe maigidan nasa ne saboda ya samu Naira dubu 150 na tafiya Dubai.
’Yan sanda sun kama Sani Sa’idu dan shekaru 34 a duniya a karshen makon da ya gabata, kan zargin caka wa maigidansa Mista Shittu Aremu da ke tuka babbar motar daukar man jirgin sama dauke da lita dubu 40 wuka a hanyar Fatakawal da ke Jihar Ribas.
Marigayi Arewa dan shekara 56 direban kamfanin sufuri ne na S.K kuma motarsa tana dauke da mai na fiye da miliyan biyar kuma ya bar jihar Legas zuwa Fatakwal tun ranar 13 ga watan Nuwamban shekarar da muke ciki.
Sa’idu ya ce ‘Wani abokina ne ya yi mini alkawarin cewa idan na samo Naira dubu 150 zai yi mini hanyar tafiya Dubai na rika siyo kayan wayar salula, sai kawai na ga hanyar da ta fi mini sauki ita ce in kashe maigidana in sayar da man motar. Muna cikin tafiya da shi mun doshi Jihar Delta sai aka kira shi daga ofishinmu, cewa hanya ba ta da kyau, saboda haka ya kwana a hanya, washegari ya karasa, to da ma na sayi wuka ba tare da ya sani ba, sai na ce masa daya daga cikin tayoyin ta huje, sai ya bude kofa ya leko, sai kawai na caka masa wuka a cinya, sai muka fara kokawa, sai na sake caka masa a ciki, sai jini ya rika zuba’.
Ya ci gaba da cewa ‘sai kawai na turo shi daga motar na yi gaba da ita zuwa Jihar Taraba a Arewacin Najeriya. Tunanina shi ne na tafi da ita Taraba na sayar da man a can a bakar kasuwa. Akan hanya na sayar da dirom biyu. Daidai gidan mutum biyu sai motar ta tsaya, har sai da na kashe mata fiye da dubu hamsin sannan ta gyaru. Ina zuwa kusa da Taraba sai sojoji da ’yan sanda suka tare ni. Suka tambaye ni takardun hanya, wato way-bill ina ba su sai suka ce na ba su lambar motar, ina ba su sai suka gano cewa man Fatakwal ya kamata a kai shi. Sai suka kama ni aka kawo ni nan Legas’.
Sani wanda dan asalin Jihar Gombe ne ya nemi a yi masa afuwa domin nauyin da yake kansa na iyali.
Rundunar ’yan sandan Jihar Legas, ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce tuni an tura jami’an tsaro don gano gawar Mista Aremu.
Sannan kuma ta ce da zarar ta kammala bincike za ta gurfanar da Sani a gaban kuliya.