Na kashe N100bn a kan harkar tsaro a 2025 — Zulum
Gwamnan ya ce matsalar tsaro na kawo naƙaso wajen samar da ayyukan ci gaba a jihar.
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce gwamnatinsa ta kashe kusan Naira biliyan 100 a wannan shekara domin inganta tsaro a faɗin jihar.
Ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci Sarkin Uba, inda ya yi masa jaje kan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama.
- Jami’an tsaro sun kama masu garkuwa da mutane 7 a Gombe
- Najeriya ta shigo da tataccen man fetur na tiriliyan 12.8 cikin watanni 15
Zulum ya yaba wa jami’an tsaro da al’umma kan ceto manoman mata 12 da aka yi garkuwa da su.
Gwamnan, ya ce matsalar tsaro na hana samar da manyan ayyukan ci gaba a yankin.
Ya kuma sake alƙawarin gina makarantu, asibiti, hanyoyi, cibiyar kwamfuta, cibiyar JAMB da kuma Kwaleji a Uba.
“Ziyarar na zo ne don duba yanayin tsaro. Zan gana da jami’an tsaro domin tabbatar da Askira/Uba sun samu kariya.
“Ba za a samu zaman lafiya ba idan babu tsaro. Muna da shirin samar da hanyoyi, ilimi da kiwon lafiya,” in ji Zulum.
Sarkin ya gode wa gwamnan; “Ka yi mana abubuwa da dama. Da doka za ta ba da dama, da mun roƙe ka, ka ci gaba da mulki. Allah Ya yi maka albarka.”