Na koma APC ne saboda jagorancin Buhari da Tambuwal – Gumburawa

Tsohon dan Majalisar Tarayya na kasa da ya wakilci kananan hukumomin Kware da Wamakko, Hon. Sa’idu Muhammad Gumburawa ya fice daga jam’iyar PDP zuwa APC saboda jagorancin Shugaba Buhari da Gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal. Sa’idu Muhammad Gumburawa ya yi wannan furuci ne a satin da ya gabata a zantawarsa da Aminiya kan canja shekar […]

Na koma APC ne saboda jagorancin Buhari da Tambuwal – Gumburawa

Tsohon dan Majalisar Tarayya na kasa da ya wakilci kananan hukumomin Kware da Wamakko, Hon. Sa’idu Muhammad Gumburawa ya fice daga jam’iyar PDP zuwa APC saboda jagorancin Shugaba Buhari da Gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal. Sa’idu Muhammad Gumburawa ya yi wannan furuci ne a satin da ya gabata a zantawarsa da Aminiya kan canja shekar da ya yi wadda ta kara kashe PDP a Sakkwato.

“Shugaba Buhari adili ne gwargwado mai so da kishin kasarsa, duk abin da zai kawo cigaba a Najeriya a shirye yake ya yi gwargwadon yadda Allah Ya ba shi iko. Wannan halin nasa ne ya sanya shi kadai ne talaka ke zabe babu kudi, har ya iya samun kuri’u miliyan 12 bai bayar da ko naira ba, domin ko a zaben da ya gabata Buhari na zaba.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal mu na tare da shi tsawon lokaci ya na girmama ni ko yaushe, mutuncin da ke tsakanina da shi da sanin halayensa ne ya sanya na zabe shi a lokacin, yanzu ko na yanke shawarar komawa APC” a cewar Gumburawa.

Da aka tambaye shi kan barin jam’iyar APC da ya yi a farkon kafata saboda Sanata Wamakko ga shi har yanzu yana cikin APC sai ya ce “A lokacin da na fita shi ne jagorata a jiha, yanzu kuwa ba shi ba ne jagora Tambuwal ne ke da wuka da nama a gudanar da mulki da jam’iyya a Sakkwato, mutane sun nemi na zo a yi tafiyar da ni ko da Alu ko babu shi zan zo, na bar APC saboda mutum daya na dawo don mutum daya,” in ji shi.

Da ya juya kan rikicin da jam’iyar ke fama da ita, ga shi yanzu ya shigo cikinta sai ya ce matsaloli ko’ina ana samunsu ko kan iyali, bai hana a shirya ba, duk jam’iyyun kasar nan suna cikin rikici ba APC kadai ba, in akwai jagora mai kyau komai za a iya magance shi da yardar Allah, in dai Buhari na raye APC za ta dushe duk wata jam’iyya a kasar nan. Kan alkawarin Buhari na wa’adi daya ya ce wannan jita-jita ce kawai, ko an yi haka kuwa su masoyan Buhari za su nemo shi ya sake tsayawa takara, don ba za su sake bari PDP ta yi tasiri ba har abada ta tashi aiki.

Gumburawa ya gwale masu hasashen ya shigo APC ne kan taimakawa Tambuwal a rikicinsa da Wamakko ‘na shigo APC ne don samun cigaba a jiha, matsala kuwa tsakaninsu ne su shirya kansu amma abin da muka sani ba shi yiwuwa a yi damisa biyu a fage, ace ga gwamna wani ya kira kansa jagora ba gwamna ba, na shigo ne don taimakawa talakawa a yi masu abubuwan cigaba.’