Na koma FC Barcelona ne don in lashe manyan kofuna -Luis Suarez

Shahaharren dan kwallon Liberppol na Ingila a da kuma yanzu yake kwallonsa a kulob din FC Barcelona na Sifen Luis Suarez ya ce babban dalilinsa na barin klob din Liberpool shi ne don ya koma babban kulob din da zai iya lashe manyan kofuna. Suarez dai ya shafe kimanin shekara uku da rabi a Liberpool […]

Na koma FC Barcelona ne don in lashe manyan kofuna -Luis Suarez
Na koma FC Barcelona ne don in lashe manyan kofuna -Luis Suarez

Shahaharren dan kwallon Liberppol na Ingila a da kuma yanzu yake kwallonsa a kulob din FC Barcelona na Sifen Luis Suarez ya ce babban dalilinsa na barin klob din Liberpool shi ne don ya koma babban kulob din da zai iya lashe manyan kofuna.

Suarez dai ya shafe kimanin shekara uku da rabi a Liberpool amma kofin daya kawai ya lashe a can, watau Kofin Carling a shekarar 2012. Sannan ya taba zama dan kwallon da ya fi nuna kwazo a gasar rukunin firimiya na Ingila da kuma wanda ya fi zura kwallaye a raga.
dan kimanin shekara 28, kulob din Barcelona ya saye shi ne a kan Yuro miliyan 80 a bara, al’amarin da ya sa ya zama dan kwallon da ya fi tsada a kulob din.
Kawo yanzu dai akwai yiwuwar kulob din FC Barcelona ya lashe manyan kofuna uku a kakar wasa ta bana. Da farko kulob din ya kai wasan karshe a kofin kalubale na Sifen da aka fi sani da Copa del Rey sannan shi yake samun tebur a gasar rukunin La-Liga na Sifen a halin yanzu haka kuma yanzu kulob din ya kai matakin kwata-fainal a gasar zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League).