Na koma PDP ne saboda Jonathan dan yankinmu ne – Mataimakin Gwamnan Ribas

Mataimakin Gwamnan Jihar Ribas Mista Tele Ikuru wanda ya koma Jam’iyyar PDP daga APC, ya ce dole ne al’ummar jihar su fito kwansu da kwarkwatarsu, su zabi Jam’iyyar PDP domin dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Dokta Goodluck Jonathan shi ne nasu ba na Jam’iyyar APC ba. Mista Tele Ikuru ya bayyana haka ne lokacin […]

Na koma PDP ne saboda Jonathan dan yankinmu ne – Mataimakin Gwamnan Ribas
Na koma PDP ne saboda Jonathan dan yankinmu ne – Mataimakin Gwamnan Ribas

Mataimakin Gwamnan Jihar Ribas Mista Tele Ikuru wanda ya koma Jam’iyyar PDP daga APC, ya ce dole ne al’ummar jihar su fito kwansu da kwarkwatarsu, su zabi Jam’iyyar PDP domin dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Dokta Goodluck Jonathan shi ne nasu ba na Jam’iyyar APC ba.

Mista Tele Ikuru ya bayyana haka ne lokacin da yake bayani kan dalilin ficewarsa daga Jam’iyyar APC, inda ya ce zaben Shugaban kasa Jonathan ya zame musu dole domin shi ne dan uwansu kuma dan yankinsu ba Buhari ba, wanda ba su san shi ba kuma ba dan yankinsu ba ne.
A jawabin da Ikuru ya gabatar ya shaida wa al’ummar Jihar Ribas cewa: “Mu mutanen wannan zamani a tarihance mun shekara 48 muna goya wa shugabannin da suka fito daga sassan kasar nan baya da kuri’unmu da dukiyarmu, don haka rashin hankali ne kuma iyaye da kakanni da ’ya’ya da jikokinmu da ba mu haifa ba, ba za su yafe mana ba, a ce mun dawo muna zagon kasa ga Shugaban kasar da muka fara samu daga wannan yanki. Don haka na tsame hannuna daga wannan cin amana.”
Sai ya bukaci dukkan magoya bayansa da daukacin jama’ar Jihar Ribas su hada hannu da sauran ’yan Najeriya wajen zaben Shugaba Jonathan wanda shirinsa na sake fasalin kasa ya kawo musu sauki da jin dadi haka ma ga sauran ’yan Najeriya.
Akwai bayanan da ke cewa matsi daga wani kawunsa Cif Uche Secondus, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na shiyyar Kudu maso Kudu da kuma rashin jin dadin yadda APC ta gudanar da zaben fidda-gwani na dan takarar Gwamna na daga cikin dalilai biyu da suka sa Ikuru ficewa daga APC.
A martanin da Gwamna Rotimi Amaechi ya mayar ta bakin Kwamishinan Watsa Labarai ta Jihar, Misis Ibim Semenitari, ya nuna mamaki kan matakin da Mataimakin nasa ya dauka tare da musanta cewa ana dakile shi a harkokin siyasa hatta a karamar hukumarsa ta Andoni.
“Ina son sanar da jama’a cewa Injiniya Ikuru shi ke juya harkokin karamar hukumarsa ta Indoni, kuma shi ne mutum na biyu wajen tafiyar da gwamnatin Jihar Ribas. Kuma Gwamna Amaechi na ba Ikuru duk martaba da girma kamar yadda mukaminsa na Mataimakin Gwamna ya tanada, kuma yana nuna masa kauna da daukarsa a matsayin aboki kuma dan uwa,” inji Kwamishinar.
Ta ce: “Duk da Gwamnan ya rika kyakkyawar fatar cewa jita-jitar da ake yadawa na zargin Ikuru da yin harshen damo ka kasancewarsa dan Jam’iyyar APC da nuna kauna ga PDP ba gaskiya ba ne, kuma ya amince cewa kowane mutum yana da ’yancin ya zabi makomarsa a siyasance. Sai dai ya ji takaicin yadda Ikuru ya zabi hanyar rashin mutunci wajen shara karya da bata suna maimakon bin hanyar girma ta komawa inda yake.”