‘Na koma sata ne saboda korata daga soja’

Wani tsohon soja mai shekara 27 mai suna Babangida Ibrahim wanda ya shiga hannun ’yan sanda bisa zarginsa da kasancewa barawon babura da motoci ya ce ya koma sata ne saboda an kore shi daga aikin soja.Tsohon sojan ya bayyana haka ne a lokacin da ’yan sandan Jihar Kaduna suka gabatar da shi tare da […]

‘Na koma sata ne saboda korata daga soja’
‘Na koma sata ne saboda korata daga soja’

Wani tsohon soja mai shekara 27 mai suna Babangida Ibrahim wanda ya shiga hannun ’yan sanda bisa zarginsa da kasancewa barawon babura da motoci ya ce ya koma sata ne saboda an kore shi daga aikin soja.
Tsohon sojan ya bayyana haka ne a lokacin da ’yan sandan Jihar Kaduna suka gabatar da shi tare da abokan satarsa ga manema labarai a hedikwatarsu a Larabar makon jiya.
Ya ce, an sallame shi daga aikin sojan ne saboda zarginsa da amfani da takardun sakandare na bogi.
Kuma ya zargi mahaifiyarsa da taimaka masa yana sata, “Ita ce ta taimaka min da wani magani da nake amfani da shi wajen kwace wa mutane babura bayan na saka su barci. Ina amfani da maganin wajen ba duk wanda nake son yi wa sata idan ya yi barci sai in sace mota ko babur dinsa,” inji shi.
Tsohon sojan ya ce a cikin kankanen lokaci da fara satar ya sace babura sama da 60 daga ’yan acaba kafin ya koma satar motoci.
Ya ce ya yi amfani da maganin da mahafiyarsa ta ba shi a kan mutane masu yawa ciki har da masu kudi da ’yan acaba, “da zarar na shaka masu ko na diga masu a cikin abin sha shi ke nan sai su hau barci,” inji shi.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Umar Shehu ya ce an kama wanda ake zargi ne tare da wani abokinsa mai suna Umar Haruna mai shekara 25 a Unguwar Kanawa a garin Kaduna.
Kwamishinan ya ce bayan an gudanar da bincike an gano motoci bakwai a wurinsu kuma an kama su ne a ranar 18 ga Maris, 2014.
’Yan sandan sun kuma gabatar da wani matashi mai suna Sabo Bature mai shekara 32 bisa laifin satar bindigar mahaifinsa ya sayar wa wani mai suna Simeon Adamu da ke Nasarawa kan Naira dubu 35, inda ’yan sandan ke neman mahaifin saboda bindigar ba ta da lasisi.