‘Na koya wa mata 152 sana’ar yin kayan amfanin gida’

Shaima’u Bala Halliru wata mace da ta dara wa tsara, wadda ta yi fice wajen koya wa mata sana’o’in hannun.Ta ce ta koya wa mata akalla 152 sana’ar yin kayan amfanin gida na mata tun lokacin da ta fara sana’ar zuwa yanzu.“An haife ni ne a garin Sakkwato duk karatuna anan na yi shi. Bayan […]

‘Na koya wa mata 152 sana’ar yin kayan amfanin gida’
‘Na koya wa mata 152 sana’ar yin kayan amfanin gida’

Shaima’u Bala Halliru wata mace da ta dara wa tsara, wadda ta yi fice wajen koya wa mata sana’o’in hannun.
Ta ce ta koya wa mata akalla 152 sana’ar yin kayan amfanin gida na mata tun lokacin da ta fara sana’ar zuwa yanzu.
“An haife ni ne a garin Sakkwato duk karatuna anan na yi shi. Bayan kammala karatun NCE ne bana aikin komai ina zaune a gida ba sana’a duk da ina son yi aikin kwastam, sai ga wata kungiya da ake kira Gidauniyar Sa Ahmadu Bello Sardauna da ke zaune a Kaduna suka zo da wani tsari na daukar mata a koya masu sana’ar hannu. Sai na shiga cikin mata 100 da suka dauka a nan garin, in da na koyi sana’ar yin kayan amfanin mata na gida wato sabulun wanki da man wankin mota da na daki da bayan gida da rob da turaren jiki da na daki  da hodar mata da maganin sauro da sauransu,” inji ta.
Ta ci gaba da cewa bayan sun kammala “tun ina da sha’awa sai na ci gaba da yin sana’ar kadan-kadan ina kai kasuwa har abin ya bunkasa ana kirana a lokacin biki na yi wa amarya kayan don raba wa. Daga nan wasu makarantu da cibiyoyi suka sanyani ina koyawa dalibai da mambobinsu in da zuwa yanzu na koyawa mata guda 152,” inji ta.
Ta kara da cewa “idan ka cire matsalar tallafi, to daidai gwargwado ina samu don ina fita da su har Jamhuriyar Nijar a kowane mako, nakan samu kudi kusan dubu 20.”